048

5 1 0
                                    

_*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*_

*NA*

_JAMEEY_

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*PAGE 48*

"Ke kishirya tomorrow by 8am flight din mu zai tashi."a hankali ta ɗago rinannun idanin ta,ta azan saman fuskar shi da take a murtuke ko murmushi babu sai faman hade rai yakeyi kamar wanda akaima dole numfasawa tayi tana cewa."ina son zanje Saloon." Taɓe baki Faruq yayi yana cewa."inaga kinsan hanya ai ko.?"da mamaki take bin shi da kallo yanda yake faman hade rai,dan shagwabe mashi fuska tayi tana cewa."No kai zaka kaini."sauke idon sa yayi dake kan wayar hannun sa ya kuma kallan ta yace."nayi kama da driver din ki.?"yayi maganar cike da tsarewa yana cigaba da operating phone din shi,bata ce komai ba sai aikin kallan sa da takeyi wani makoko na neman fasa mata mako shi haka takeji,numfashinta ta janyo sannan ta fesar tace."my husband is my driver and also is my everything idan baka kaini ba wazai kai ni.?"maganar ta,ta soki zuciyar shi,mikewa yayi yace."kice bake ba zuwa saloon kenan."yana ida fadar haka ya fita yana kara wayan sa a kunne.Wasu zafafan kwalla taji sun taho mata tafara kokarin maida su cikin rashin sa'a suka samu damar silalo mata Koda ya fita balcony ya samu waje ya zauna yana cigaba da waya."No Uncle I,zan baro ta wajen Fulani."daga bangaren I yace."bai kamata kabarta ba kadawo tareda matar ka."lokaci ɗaya ran Faruq ya baci yace."one week fa?bazan iya dadewa har haka ba."okay saboda ba tsohuwar kaba ce ai."murmushi ya dan sako na gefen baki yana shafa keyar shi yace."ohh Uncle harda gori."dariya yayi yace."abinda ke cikin raina na faɗamaka."sorry Uncle yanzun dai zan tsaya are you happy."yawwa son ko kaifa Allah yabarmin kai da rai da lafiya."ameen my uncle,ya aunt."she's fine,ina tunanin zuwa jibi zamuyi landing to Katsina."wani irin dadi ya lullube Faruq yace."am so happy Uncle ina missing dinka badly."me too son nayi kewar ka."Faruq yace."zaku jima ko.?"Yeah,so how is my daughter."dan shiru yayi kamar baiji shi saida ya kuma tambayar shi sannan yace."tana lafiya."why are you silence.?"dan kame kame yafara yace."Am am bakomai banjika bane."Okay muyi magana anjima."Ok."kashe kiran yayi ya wuce side din shi.Itako Ramlat da kyal ta mike zuwa kitchen ta iske yar aikin ta na gyara kifi,dukawa tayi ta gaishe da Ramlat cikin girmamawa."Yawwa Bilkis."sofa tahau ta zauna tace."Make me coffee."to Hajia."aje aikin data fara tayi sannan tafara preparing din coffee bata jima ba ta kawo mata,dukawa tayi ta mikama ta."ranki shidade gashi."amsa tayi ta aje saman dining table din dake cikin kitchen  a hankali ta fara sipping din coffeen."Mi za'a girki ranki shidade.?"shiru Ramlat tayi tanaci gana da sipping tea dinta tace."Paper fish with cus-cus."to ranki shidade."cigaba da aikin tayi tace."but kibari zan hada girki ki aje min komai."toh ranki shidade." cigaba da haɗa mata komai tayi kamar yanda ta bukata."angama komai Hajia."mikewa Ramlat tayi tafara preparing cus-cus din as lunch,tareda taimakon Bilkis ta gama komai banda kamshi ba abinda keta shi a cikin kitchen din."Anty wannan girkin na musamman ne kamshinsa ma na daban ne."Murmushi Ramlat tayi tace."Really.?"gyada kai tayi tace."sosaima kuwa Hajia."Warmers ta dauko ta zuba girkin sannan ta samu katon basket ta zuba ciki,wasu Warmers din ta kuma dauka ta zuba sannan takai su dining ta jere ta dawo tace."Hajia nagama gyara komai."okay kije ki shirya zan aike ki."to ranki shidade."fita tayi ta nufi room din ta,sannan mai wanke wanke tafara aikin ta itama Ramlat din fita tayi ta nufi bedroom dinta,sannan ta nufi bathroom zata watsa ruwa.

☆☆☆☆

Tunda suka fito daga Lecture take tsaye gaban Senate bulding da alamu akwai wanda take jira ciro wayar ta tayi kira Iphone X mas da alamu akwai wanda take kira"bad network."shine abinda ta faɗa tanajan ɗan guntun tsoki wanda har saida sautinsa ya bayyana,tafiya tafara kasa harta baro bakin sanate din baki daya ta tsaya bakin titin da zai sadaka da main gate na makarantar."Napep."ta saida mai keke napep da yazo gittawa ta gefenta tsayawa yayi ya leko ya kalleta."Hajia ina zuwa.?" Shiga cikin napep din tayi tace."GRA."tashin mashin din yayi sukaci gaba da tafiya saidai still bata daina neman number da take nemaba saidai har yanzun line da take nema not reachable.
tafiya mai nisa sukayi ya ajeta har kofar wani makimancin gida ya tsaya da ita,miko masa kudi tayi sannan ta saka kanta cikin gidan da mai gadin gidan tafara haduwa."sannu da zuwa Hajia."Yawwa malan idi ya aikin.?"Alhamdulillah."da haka ta saka kai cikin apartment din dayaka kasance shine tsakiyar gidan."Ka tabbata wannan itace Sara kanwar Sanda."jinjina kanshi yayi ya maida dubansa ga wanda ya tambaye shi yace."Kwarai kuwa ranka shidade,shakikiyarsa ce bana ko kokonto."daukar bakin glashing sa yayi saman fuskar sa yace."kasan bana son kuskure matukar aka samu matsala kaima kasan sauran."Allah yataimaki mai gida bana tantama."good."tada kan motarsa yayi suka hau baban titin GRA sukabar unguwar a sukwane har kura na tashi.
"Mamma sannu da gida."yawwa har an dawo makarantar.?"ajiye jikarta tayi ta zauna a gajiye tace."Eh Mamma walahi yau duk nagaji dayawa."sannu ai kina ma kokari,ina Ashirun.?" Dan kwabe fuska tayi tana cewa."hmm wallahi raina a bace yake nafi awa biyu ina jiransa amma yaki zuwa daukana ni kuma na hau adaidaita sahu."da mamaki mahaifiyar ta ke kallanta tace."kedai Saratu bakijin magana yanzun baki gudun yayan ki ya ganka cikin adaidaita baya hanaki ba."bata fuska tayi kamar zatayi kuka tace."Allah nagaji dayawa ga yunwa inaji ga zafin rana,nidai a canza mani driver bana iyawa." Ta ida maganar tana share hawayenta,kama baki Mamma tayi tana kallon Sara dakuwa tayi mata tana cewa."kincin gidan ku,ba wani drivern da za'a sauya wannan din shine dai mutumin kirkine kuma sai kiyi masa uzuri." Share hawayen takaicin shanyata da yayi Sara tayi tana cewa."Haba mamma kullin uzuri nidai nagaji wallahi jibine duk na rame saboda bala'in da nike sha inta faman jiransa."wannan karan tarasa abinda zatace ma yar tata saidai ido data bita dashi wayarta ta dauki neman agaji hakan yasa ta dauki wayar tana fadada annurin fuskarta."barka kade ɗan albarka ya aikin.?"daga dayan bangaren yace."Alhamdulillah,Sara fa ta iso gida kuwa.?" Maida dubanta tayi wajen Saran daketa faman sumbure sumbure tace."Eh gata nan ma."bata wayan."mika mata tayi batareda tace komai ba,amsa tayi ta kara a kunnen ta."miyasa baki jira Ashiru ba.?" Turo baki tayi kamar Sanda tana gabanta ta fara cewa."Yaya wallahi na jima ina jiran shi..."yiman shiru you are very stupid!ko zaikai dare miyasa zaki hau motan haya danke kadai na tanaji shi,saboda bakida mutunci kika shure umurnina."narai narai tayi da ido kamar mai shirin kuka."dan Allah kayi hakuri banyi da gayyaba nafi awa biyu ina jiransa fa Yaya."yiman shiru bakisan abinda kikeyi ba inda kinsan illar bin motan haya da kikayi na tabbata koda zaki kai dare bazaki kuskuren hawan taba,ki saurareni da kyau matukar kikace zaki shure umurnina zaki hadu da fushina,this is last warning da zaki kuma gigin bin motan haya."toh kayi hakuri."mikama Mamma waya."a sanyaye ta mika mata."Umaru kayi hakuri ni kaina saida nayi mata fada."bakomai Mamma,ina fatan ba abinda kuke bukata.?"eh babu gaskia."idan akwai Sara ta sanar mani."badamuwa,Allah yayi albarka."Amin."da haka sukayi sallama,ajiyar zuciya ya fesar yana aje wayar saman table a hankali ya mike tsaye yana dukan hannayen sa ya sake fesar da zazzafan numfashi yace."Aikin banza kwata kwata bakijin abinda nike fada maki Sara,kin zama mai kunnen kashi."Morning Sir."a hankali Acp Sanda ya juyo ya kalli ɗan sandan dake kame daga bayan sa yace."Morning."Sir you have an appointment by 2pm."for what.?" sadda kanshi yayi kasa yace"for general meeting in Abuja."with suprised yake kallan yaron sa kamar wani bako agare shi yace."dama yau ne.?"yes Sir."jinjina kanshi yayi yace."sai yanzun zaka sanar mani."Sorry Sir,laifi nane dan ban kuma tunatar dakai ba."yanzun karfe nawa."12 pm Allah ya huci zuciyar ka."bazan je ba."a kidime yake kallan Sanda kana ganin shi zakasan ya razana iya razana."Sir...ɗaga mashi hannu yayi fuskar shi ba alamun wasa a cikin ta yace."get out in my office."sorry Sir."yace yana kara sara mashi sannan ya fita,da wani irin matsiyacin kallo Umar Sanda yaraka bayansa yana jan dogon tsoki."mutane dayawa basu san ka'idojin aikin su ba mtsw."komawa yayi ya zauna,yana maida kansa jikin kujera ya rufe idanunsa ya rufe,wayar sa dauki ringing bin wayar tashi yayi da manyan eye bowls dinshi saidai da sauri yai picking tare da mikewa tsaye ya ƙame yace."Good day Sir."daga dayan bangaren akace.

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now