089

2 0 0
                                    

_*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*_

*NA*

_JAMEEY_

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*PAGE 89*

"Hajja lafiya kira kamar yanzun"?daga bangaren Hajja tace."Ummaru ka taho Khadijatu bata lafiya da gani dai haihuwar nance tun dazun take fama da nakuda."inalillahi wa'inna ilahirraji'un!gani nan a hanya Hajja"datse kiran kawai yayi da saurin sa ya nufi kofa kota kan Hajia kubrah baibi ba ganin yanda ya fita hayyacinsa batasan sadda tasha gabansa ba tace."kanka daya kuwa Umar,ka dawo hankalin ka mana."dafe Kansa yayi yanajin wani irin yanayi yace."OMG haba mommy kibani hanya mana inaji fa akan kunnenki kikaji Hajja tace Khadija nakan guiwowinta ta ina zansamu nutsuwa haba mana momy kiji tausyaina mana."yanzun d'an shegen zaka raka haihuwa har kana neman kifewa Kasa?" I'm so sorry mommy kimin izinin tafiya tare da addu'ar ki, ALLAH ya sauki Khadija lafiya" da saurin sa ya fita har gudu yake hadawa saidai ta raka shi da kallan takaici ba ita kadai ha hatta kanen sa da ido suka bisa Banda Rumaisa data maye masa baya itama a guje yana shiga mota itama ta shiga da gudu ya figeta zuwa gidan Hajja,itako mommy takaici ya addabeta kamar tayi kuka haka takeji, parking kirki Umar bai tsaya yi ba ya shige part din Hajja da gudunsa yanda ya iske Jummala tabbas ya daga hankalinsa kuka kawai take garza tana zata mutu take zuciyar Umar ta tsinke baisan sanda ya isa wajen Hajja ba yana mai kokarin daukar Jummala."bi sannu ba'ayi ma mai juna irin haka Umar kabi sannu dai haihuwar ma aita karaso kabari kawai tayi ta a gida"Aaa Hajja banaji zan iya barin Khadija a wannan halin akaita asibitin dai zaifi."surarta yayi ko nauyinta baiji yayi waje da ita ya sakata a mota shida Rumaisa sukaja motar ko Hajja bai tsaya dauka ba kai tsaye babbar asibitin K/dara ya nufa da ita cikin tsantsar tashin hankali itako Jummala tagama galabaita banda aikin sannu da Rumaisa ke jera mata shiko kadan kadan ya waigo ya kalli fuskar Jummala da idanuwanta ke a rufe kamar mai bacci Aemma banda nishin azaba ba abinda take fitarwa tana jiran zan mutu wayyo Allah Yaya Umar kataimakeni wayyo Baffana shieknan mutuwa zanyi Umma na"da sauri yayi parking yana sake daukota kamar ya dauko jinjira daman tun kafin ya iso har Rumaisa ta sanar da nurse Abida sawa tayi ya sata a bicycle din hospital akayi da ita babbar maternity mai dauke da different parts saidai Jummala taki sakin hannun Umar din gam haka ta damke tafin hannunsa tana yaya Umar ka taimaka mani zan mutu,kana ganin kasan tagama fita a hayyacin ta,shiko duk ya gama zaucewa kukan kadai ya rage masa yayi ji yake kamar yabita inda dama yai mata haihuwarma yace "ba zaki mutu ba Khadijatu zaki haihu lafiya da ikon ALLAH,Ina kaunar ki keta musamman ce kina da mahimmancin gaske arayuwata banajin zanyi tasiri a wannan duniyar matukar kika tafi kika barni Jumm noala"ya ida maganar yana Jan dogon numfashi ya daga hannayen sa sama yaci gaba da cewa "ya zuljalalu wal'ikram ga marainiya nan baiwarka ya hayyu ya qayyum ka sauketa lafiya"a hankali ya mike tsaye ya dubi nurse Abida yace"kuje Allah ya dafa mata"da Ameen suka amsa saidai wasu daga cikin su harda kwalla saida sukayi ma Jummala a wajen Umar ya duke bisa guiwarsa take yaji hawaye masu dumi suka zubo masa dafasa yaji anyi a razane ya dago kanshi Rumaisa ke bashi hakuri itama kukan takeyi rungume Rumaisa kawai yayi da karfinsa ya rasa miyakeji a yau din nan,sai a lokacin Hajja ta iso tana"yanzun dan dibar albarka Umaru saika gudo kabaro ni Kai ga mai diya ko"?kama baki tayi tana kara matsowa gabansu tace"kar dai ace kuka kakeyi Umaru Amma dai ALLAH ya shiryeka dai,ai addu'a kawai take bukata dai"a hankali ya saki Rumaisa yabar wajen yanata kewaye kewaye..... Yanzun haka matata tana dakin haihuwa taya kake zaton hankalina zai kwanta a halin yanzun."?Muhi ya ida maganar ya dafe goshinsa da yake masa zugi yana kallan Buba shima din shi yake kallo saidai kallan al'ajabi yakema Muhin kafin yace."ka daina cewa matar ka mana Muhsin kuma banda abunka kaidin me zaka iya yimata kadai gama naka aikin tunda ka mata ciki, yanzun gashi kabarta da wahalar haifesa."dakikin kallo yabi Buba dashi yace."tunda dai kayarda cikin nawa ai ba matsala bace,ni yanzun ba wannan ba nasa ayi mani addu'a a sauke mani qurani a makarantun allo tunda aka tabbatar min da cewa anytime tana iya haihuwa"d'an dage kafada Buba yayi yace"well ina fatan hakan"waya kawai Muhi ya dauko yace"Hamisu ya ya?"daga bangaren Hamisu yace"har yanzun dai bata kaida haihuwar ba"ya salam! ji nike kamar na amsar mata haihuwar nan wayyo matata Ina sonki Jummala"Ajiyar zuciya ya sauke yace"Ina dai sauraronka shifa wancan lusarin fa."?dariya kawai Hamisu yayi yace"ranka shidade haukane kawai baiyiba yau kai kace matarsa ce"ya isa"Muhi ya daka masa uwar tsawa yace."Jummala matata ce Ni kadai ka kuskura bakinka ya kara furta wannan kalmar bako shakka saina datse harshen ka."yanda yaji muryar Muhi tabbas yasan ya gama fusata jiki a matukar mace yace"tuba nike mai gida, yanzun dai munakan yi mata addu'a"any updates,let me know"kashe wayar kawai yayi ya dubi Buba yace"d'ana nayin shekara zanje na anshi abuna sannan ba auro uwarsa muyi rayuwa mai dadi"Dan dariyar shakiyanci Buba yayi yace "Kada ka manta a gidanwa take a halin yanzun his excellency Yusuf Umar ba zai lamunci shirmanka ba,Kuma kada kamanta yanzun sune da gwamnati kuma sudin abakan hamayyar mu ne"ba damuwata bane,koma waye matata nasani da d'ana fakat"ya Ida maganar yana daukar mataki akan fuskar shi sharewa kawai Buba yayi bai Kara cewa komaiba da haka Muhi yabar falorn yanayin bedroom yanajin Kansa kamar ba shi ba.A wajen Jummala kuwa ba kananun Drs bane akanta da an yanke shawarar yi mata C's saboda har Umar saida yasa hannu an fiddota zuwa wajen C's ana shiga da ita cikin room din tana haihuwa,tana haihuwa take ta sume batasan inda kanta yakeba jinjirin kadai aka raba da uwar aka bawa N.Abida tafara kokarin gyara jaririn anayin kan uwar domin bata taimakon gaggawa a wajen Umar Y daga shi sai Hajja da Rumaisa saidai wannan karan his excellency Yusuf Umar ya iso wajen shike faman bawa Hajja hakuri da taketa faman kuka ganin irin wahalar da Jummalar ke sha, Sis Abida ce ta fito daga room din da sauri Umar ya tareta yace"Yaya Sister."? nunfasawa tayi tace", she's deliver know but bata cikin hankalin ta ayi mata addu'a dai."gaba kawai tayi tangal tangal Umar Y yayi saida suka ganshi Kasa ya zube sakamakon muryar wata nurse dayaji tana ta mutu fa, inalillahi wa'inna ilahirraji'un likita.... kanshi sukayi suna salati a kidime excellency yasa aka kira Dr yazo wajen Umar sawa yayi aka kaisa cikin aminity aka basa bed domin samun rest saboda tsoro da tarin fargaba su suka cika zuciyar Umar din, shiko Muhi koda yaji wannan information din baisan sanda ya fige mota ba yayo hospital din gadan gadan kamar zaibar kasar ga bugu da kirjin shi ke masa tsabar tsoro da fargaba,duk da yaji Khadijan ta haihu amma fargabar rasata sun danne farin cikin haihuwar da akai masa duk da burinsa ya gama cika ta haifa masa d'a namiji kamar yanda yake fata a rayuwar sa.

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now