080

7 0 0
                                    

_*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*_

*NA*

_JAMEEY_

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*PAGE 80*

Dan shiru tayi tana kallon Samira tana nazartarta sannan ta numfasa cike da gadara ta fara cewa."Zan daukeki aiki sai dai ina da sharuda kamar yanda na gaya maki." Numfasawa tayi tana mai cigaba da cewa." Iyakacin ni zakiyi ma aiki a gidan nan ban yarda kina magana da kowa wace mace a gidan nan,ba ruwanki da kowa abinda ya kawo ki shi zakiyi kuma moping shara wankewanke har da girki duk ke zakiyi idan har kin amince to idan sun maki tsauri kofa a buɗe take." Furzar da naunauyen numfashi Samira tayi tana dan gyara tsugunin da tayi duba da ta dade a tsugunne har kafafunta sun fara yi mata dayi kuma Hajiya Mero taki cewa ta zauna kallon Hajia Mero tayi tana cewa."In sha Allah zan kiyaye Hajia."Taɓe baki Hajia Mero tayi tana cewa."Okay duk wata zan dinga baki 10k." Jinjina kai Samira tayi tana cewa."Toh Hajia nagode sosai Allah ya saka da alkhari."Ko Amin bata ansa ba sai ka ci gaba da cewa da tayi."Karfe bakwai na safe yayi maki a gidan nan saboda haɗama yan makaranta breakfast idan kuma kikayi lete da matsala dan yaran basu haɗa karatunsu da komai ba fatan kina dauka dai.?" Ɗaga kai kawai Samira tayi ba tare da ta sake cewa komai ba tashi tayi bayan ta bata damar tashi tana nuna mata kitchen ta shiga dan fara haɗa masu lunch,babban apartment ne mai dauke da two bedrooms sai kitchen da toilet sai kuma upstairs shi kuma two bedrooms ko wane parlo cike yake da manyan kujeru tsayawa tayi kallon tsaruwar parlon tana wucewa kitchen din dan fara aiki komai nuna mata Hajia Mero tayi da kanta tana kuma nuna manta duk yanda ake yin abubuwa sannan ta fita ta bar mata kitchen din numfasawa Samira tayi tana fara aikin dake gabanta.

★★★

Da kuka Ramlat ta turo parlon Momy,tashi tsaye Momy tayi tana kallon ta tana tarota gami da cewa."Ramlat lafiyarki kuwa?maike damunki?mai ya saka ki kuka.?"rungume Momy tayi tana kukanta a hankalin ɗagota Momy tayi daga jikinta suna zama saman tower tana cewa."Nace ki gaya man maiya faru.?"Share hawayenta tayi da bayan hannunta tana turo baki tana cewa."Momy ba Ya Faruq bane."Cike da mamaki Momy take kallon Ramlat tana cewa."Faruq kuma?mai kuma ya faru mai yayi maki shi da baya garin ma."Sauke ajiyar zuciya Ramlat tayi tana gyara zamanta gami da gaya mata duk abinda ya faru a tsakaninsu,kallon Momy tayi tana cewa."Nidai Momy ya bar man apartment ba zan iya zama dashi ba."Numfasawa Momy tayi tana cewa."Kenan Faruq ya dawo garin?to ke maiyasa baki son ya zauna a apartment din naki.?"Girgiza kai Ramlat tayi tana cewa."Momy tun asali ai ba a wannan apartment din yake ba tunda akayi aurenmu bai ta kwana a apartment dina ba haka nima ban taɓa kwana a nashi apartment din ba kowa nashi yake kwana yake rayuwarshi sai yanzun kawai zai wani hado kaya yace zai dawo a nawa bayan tun can da ba haka muke ba." Murmushi Momy tayi tana kama hannun Ramlat tana cewa."Ramlat."Ɗagowa Ramlat tayi tana kallon Momy ba tare da ta ansa ba numfasawa Momy tayi tana cewa."Ramlat ai nasa dadi zaki ji da mijinki ya fara nuna yana son zama a kusa dake ko Ramlat?nasa ai fatan da muke kenan hankalinshi ya dawo kanki kuyi rayuwarku cikin soyayya da yardar juna, sai naga dawowar tashi a apartment din naki wata dama ce Allah ya baki a hannunki yanda zaki maido da hankalinshi a wajenshi ki mantar dashi da yama taɓa son wata busy girl yar jarida."Sunburo baki tayi tana cewa."Amman Momy nidai gaskiya a yanzun banjin Yaya Faruq a zuciyata kamar yanda shima bai jina a zuciyarshi daman Allah ne ya ɗaura man kuma na rokeshi ya yaye man dan haka Allah ya bashi wanda yake so nima ina son ya sawaƙe man na auri wanda yake sona."Wani kallo Momy tayi mata tana cewa."Amman dai Ramlat baki da hankali ko? To bari kije aurenki da Faruq idan har Kinga abinda ya tsinkashi to mutuwa ce dan haka daga yau daga nan karda na ƙara jin magana makamanciya irin wannan tun wuri ki cire maganar saki a bakinki dan haka maza tashi ki koma gidanki tunda rashin wayau ya kawoki."

Kuka Ramlat ta fashe dashi tana cewa."Wayyo Allah Momy wallahi ba zan iya cigaba da auren Ya Faruq ba tunda yana da wanda yake so ya saƙawa man ya auri wanda yake so nima a barni na samu mai sona na aura tunda bai ɗaura man idda ba."Tashi first lady tayi tsaye tana cewa."Ramlat inason ki saka a ranki ba zaku taɓa kashe aurenku ba koda kuwa ku duka ne baku so haka zaku zauna da juna har mutuwa tazo tayi sanadin rabuwar taku dan haka ina mai ƙara gaya maki karki kuma yi man magana makamanciya irin wannan idan kuwa ba haka ba zan mugun saɓa maki kin dai jini dakyau."Sosai Ramlat take gunzar kuka kamar wanda aka gayama sakon mutuwa haka Faruq ya shigo ya taddasu tsaye cirko cirko ita da Momy kallon Momy yayi yana matsawa wajen Ramlat yana kama hannunta yana cewa."Wifey what happened?Momy kukan mai take haka.?" Tsaki Momy tayi tana cewa."Gata nan sai ka tambayeta ai tunda tana da baki." Fisge hannunta Ramlat tayi daga rikon da Faruq yayi mata tana barin wajen dakatar da ita Momy tayi tana cewa." Karki sake ki fita daga parlon nan Ramlat." Cak Ramlat ta tsaya tana kuka ba tare da ta waigo ba,zama Momy tayi tana nuna ma Faruq waje ya zauna tana cewa."Dawo ki zauna tun ban saɓa maki ba Ramlat." Waigowa Ramlat tayi tana cewa."Wayyoo Allah Momy amman Mom...shiiiii Momy ta dakatar da ita tana ɗaura yatsunta sama bakinta tana mai cewa."Zauna." Zama Ramlat tayi tana kauda kanta gefe dan ko kallon Faruoq ita sam bata son tayi,shi kuwa Faruq jigum yayi yana kallon Ramlat yana mamakin abinda ya haɗa ta da Momy dan bai kowa ma ranshi wani abu ba,katse shirun Momy tayi ta hanyar nuna Ramlat da yatsu tana cewa."Ramlat dole sai kin ɓata man rai hankalinki zai kwanta ko.?"Girgiza kai Ramlat tayi tana sauke ajiyar zuciya tana cewa."Ba haka bane Momy ko ɗaya bani san ɓacin ranki kawai ni na gaji ne kin san nayi dai hakuri iya hakuri da Ya Faruq ni ɗaya na soshi nayi hauka na har na gama shi kuma da wanda yake so a cikin zuciyarshi tunda har yana da wanda yake so a barshi ya auri zaɓin ranshi, nima sai ya sake ni naje na auri wanda yake sona nima nayi rayuwa a karkashin soyayya shine nayi laifi Momy?shin Momy maiye laifina a wannan maganar? Mutunmin da baya sona har gaya man fa yasha yayi to nima yanzun yanda yake jin baya sona haka nima bani sonshi ban kuma iya yin zaman aure dashi kawai ki bashi izinin saki na tunda ma Allah ya kawo shi." Tunda Ramlat ta fara maganar Faruq yake jin wani iri a zuciyarshi har wani zafi yaji zuciyarshi ta fara saboda furta kalma ƙi da Ramlat ta furta mashi,lumshe ido yayi yana buɗewa gami da cewa."Momy Ramlat gaskiya ta faɗa kuma sai naga babu laifi dan anyi mata abinda ta buƙata tunda ita ta nema da kanta." Murmusawa Momy tayi tana cewa."Naji sai dai Ramlat ina son na neman wata alfarma a wajenki."Kallon Momy Ramlat tayi tana cewa." Alfarma kuma Momy wace irin alfarma ce wanann.?" Numfasawa Momy tayi tana cewa."Kwarai kuwa Ramlat tunda kin bukaci saki kuma za'a sake ki kamar yanda kika buƙata sai dai inason kiyi hakuri sai bayan election kinga zaɓe ya gabato bai wuci wata uku ba idan har akayi wannan sakin zai iya taɓa mana siyasarmu ace duka yaushe akayi bikinku har kun rabu idan aka gama election da kaina zan ansar maki takardarki a wajen Faruq."Firzar da naunauyen numfashi Ramlat tayi tana cewa."Hakane Momy, amman da sai ya sake ki gobe zan bar kasar na koma Abudabi gida kawai ba zan sake zuwa Nigeria ba Momy zan kuma boye duk wata hanyar za'a gane babu aure a tsakaninmu da Ya Faruq koda zanyi wani auren ba mai sani sai ku ba zan yarda na auri dan nigeria ba ma baki ɗaya."Girgiza kai Momy tayi tana cewa."Idan har na kai ayi man alfarma to a bari sai bayan election sai ayi sakin Ramlat." Dan shiru Ramlat tayi sai kuma tace."Shikenan Momy Allah ya kaimu ai wata ukku ne ya rage election ba wani nisa sosai,amman kice ya kwashe kayanshi ya maida apartment din shi."A'a Ramlat ki barshi ya zauna a naki apartment din na wata ukun."Shikenan Momy Allah ya kaimu after election din."Da Amin Momy ta amsa banda Faruq da yake kallonsu yana jinjina ma karfin halin Ramlat wai shi Faruq zai saketa aikuwa yaga yanda za'ayi dan ko Takawa bai isa ya sashi sakin Ramlat ba yanda ta nace ta aureshi haka kuma zata zauna dashi dan shi yanzun yake jinta a zuciyarshi kuma yanzun yake jin zai yi rayuwa da ita,rayuwar ma ta aure amman yaji after election din tayi yaga yanda za'ayi a gabanshi ake deal da auren shi gaskiya kam,da haka Ramlat ta koma gidanta ba tare da ta ƙara zama a gidan Momy tunda taga Faruq yana nan yayi masu zaune.

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now