_*🏝️NAHIYATA AREWA🐄*_
*NA*
_JAMEEY_
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
*PAGE 20*
"Why Faruq mike damunka.?" Tell what happening to you.?"Yarima Ishaq ya tambaye shi cikin damuwa,maida kanshi ƙasa Faruq yayi sai huci yake kamar wanda aka anso daga bakin zaki can ya numfasa ganin irin kallon kai nike saurare da Uncle I yake mashi yasa shi gyara zamanshi da kyau yanda Uncle din zai fahimci da kyau ya fara cewa."Ka tausaya mani Uncle kowa bai damu dani ba even dady please ka tausaya mani." Numfasawa Uncle I yayi yana jinjina mashi kai yana cewa."Tell me what's going on.?"Sake matsawa yayi gefen kanin mahaifiyartashi ya zayyana mashi komai tun daga farko har karshe ya firzar da naunauyen numfashi yayi yana cigaba da cewa."Itace zabina kataimake ni Uncle I."Tunda Faruq ya fara ma Uncle I bayanin baison Ramlah shi Jamila yake so,Uncle yake kallonshi yanajin inama ace mafarki ne ba gaske ba,ganin kallon da Faruk yake mashi,ya firzar da huci mai zafi ya fesar yana tunanin ta ina zaifara baice komai ba ya dako dankareriyar Samsung ultra din shi yana dannawa,kiran yayarshi yayi a waya 3x har ta kusa yankewa ta dauka."Uncle I u re well come dazun Fulani ke shaida mani dawowar ka." Murmushi ya saki kamar yana a gabanta yana cewa."Yes inason magana dake idan kina free."Okay yanzun dai zanje meeting you know siyasa ta matso ban zaune." Numfasawa yayi yana cewa."Hakane idan kinsamu tumet ko kuma zanzo da kaina."Okay ba damuwa."Da haka sukayo sallama da juna."Mumy ce ko?Uncle.?" Cewar Faruq yayi ma Uncle I tambayar cike da damuwa,ɗaga mashi kai yayi yana cewa."Eh itace." Cike da takaici Faruq ya girgiza kai yana cewa."Banda lokaci zanyi meeting da Govenor wifes,Sanators,Reps and on,always bata da lokacin dan ta."daƙuwa Uncle I yayi ma Faruq yana cewa."Stop it Faruq she's you mother kaimasu uzuri mana ka kwantar da hankaln ka,sannan kanemi akhairi idan matar kace zaka aure ta,itama Ramlat may be akwai rabo tsakanin ku,dan haka kadaina saka kanka a damuwa kasan idan kana Depression zaka iya aikata komi akan bacin rai pls Faruq kadaina saurin fushi,dan haka yanzun tashi muje kabawa Khalid hakurin abinda kai mashi." Dan turo baki Faruq yayi yana cewa."Uncle kaga... Katseshi Uncle I yayi yana ɗaga mashi hannu yana cewa."Bansan musu bamu haka dakai bansan mu fara tashi muje."
A tare suka nufi side din nasu amman ba Khalid kiran shi Faruq yafara."Khalid."shiru har kewaye ya duba bashi kiranshi Uncle I yayi bai ɗauka ba,ana biyu ya fito daga wanka ganin Uncle I yashi dauka da sallama abakin shi."Uncle I inason in....ya isa kana ina.?" Uncle ya katseshi yana tambayar shi,shiru yayi yarasa abinda zaice."Kana ina Khalid,munzo side din ku baka nan." Numfasawa Khalid yayi yana cewa."Am sorry to say,bansan ya zaka dauki zancen ba." Jinjina kai Uncle I yayi yana cewa."Oya tell me?" Lumshe ido Khalid yayi yana cewa."Yanzun haka ina Abuja."Shiru Faruq yayi jin abinda Khalid ya faɗama Uncle I.Zaka iya fushi dani har haka Khalid?A zuci yake maganar shi,yana mamakin Khalid a zahiri.
☆☆☆☆
Matasa ne keta faman lika postoci a kofar gidajen mutane da shaguna wajen sana'ar Jama'a suna likawa suna ihu da bushe-bushe wisil dake nuna tsantsar dabanci na yan bangar siyasa suna ihu cikin wata uwar zuga suna cewa."Sai Honourable Balarabe Salisu."Shine abinda suke ta maimaitawa suna cikin lika postors din wasu matasan suka fito da gariyo barandami da addina a hannun su,suma ihun suke basuyi wata wata ba suka fara kware postors din da matasan suka lika,cikin kankanin lokaci rikici ya balle a tsakanin matasan,kowa yana kokarin yakar junan su."Bamayi ba uban daya isa yasa mana poster din da bamaso a cikin unguwa."Faɗa suke sosai kowa ido ya rufe suna cikin rigimar ɗaya daga cikin yan unguwar yasa adda ya sararma abokan hamaiyyar su hannu take jini ya balle sai shatata yakeyi kasa."Ihuhuhu ba zamu yarda ba,yau saidai ayi mutuwar kaso."Kure yace yana zaro takobi ya daga zai dabawa matashin da ya yanki abokin shi,tashin jiniyar yan sanda tasa kowa ya watse da gudu ana kare,yan sanda suka kama wasu daga cikin matasan wasu kuma sun gudu,duk sunjima junan su ciwuka a jiki police station aka kai matasan bayan kanta (cell).DPO ya dauki statement akafara dukan su ana tuhumarsu akan ta'addanci."Kune masu tadama al'umma hankali ko?akan bangar siyasa kuke neman halaka junan ku."duka bana wasa ake masu ba ranar a cell suka wuni wajen yan sanda.
YOU ARE READING
NAHIYA TA AREWA
General FictionThe Story of Nahiyata Arewa is the one that comprise the most important things such as Correction,Injustice,Betrayl and Revenge including Entertainment and Education, is a Falatable and testable story.