_*🏝️NAHIYATA AREWA🐄*_
*NA*
_JAMEEY_
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
*PAGE 5*
Katafaren Park ne mai dauke da wurare daban-daban na shakatawa,ba abunda babu a cikin kamilallan garden din..city Park wanda yake dauke da koraye masu matukar birgewa da ban shi'awa,yan matane da samari su shidda,mata ukku maza ukku a gefen su ga shishanan aje sai zuƙa suke suna fesa hayakin ta cikin kwanciyar hankali.. ɗaya daga cikinsu ya dago yana kallon Farouk yace."Farouk yakamata mubar kasar nan hakanan." Lumshe sanyenyun idanunsa Farouk yayi masu ƙara mashi madarar kyau da kwarjini yana cewa."Aaa Oldman ya hana." Zaro ido guy din yayi yana cewa."Why haba my man." Taɓa baki Farouk yayi yana cewa."I don't know." Ya ida maganar yana shan shishar shi ko ajikin shi..Wata Beb dake gefen Farouk sai karairaya take tana yauki daka ganta kasan ta hannun ce, kallon Iman yayi yana cewa."Iman kinsan gobe akwai club fa."Cewar Hashim wanda suke kira da Ba'ba.
Gyada kai wanda aka kira da Iman tayi tana cewa."Idan Farouk zaije nima zanje."Iman ta ida maganar cikeda yauƙi,dan harara Farouk ya watsa mata yaci gaba da harkar gaban shi,cikeda shagwaba tace."Haba Baby ya zakai mani haka kasan kaine farin cikina kuma bazan iya k..... Ɗaga mata hannu Farouk yayi yana cewa."Shut up are you mad?wai bana gaya maki ban bukatarki ba,infact all kind of mata banson shi pls Iman live me alone pls." Ji yayi wajen ya fice mashi a rai baki ɗaya akan maganar da Iman tayi mashi daukar wayoyinshi kawai yayi ko kallonsu baiyi ba ya fito ya nufi parking lot din wajen,a fusace yafigi mota yabar Park din ranshi na tafasa ba inda ya wuce sai guest house dan hutawa.
☆☆☆☆
*NIGER STATE*
Ba ƙaramin wahala Ola yake sha a wajen yan-sanda ba tunda aka kawo shi ake gana mashi azaba iya azaba dan sun kafe akan shine ya kashe CP na jahar Niger,wani irin ƙwaton icce wani police ya buga mashi a ƙafa ba ko digon tausayi a fuskar shi ya dago kai Ola yana cewa."Bazaka faɗi wanda yabaka wannan kwangilar ba ko.?" Cikin halin mutuwa ko rayuwa dan a hankali a hankali Ola yake fitar da numfashi tsabar wahala yana cewa."Oga bansa niba,kuyi mani rai." Haka Ola keta faman gitta rai akan tuhumar da ake mashi na kisan CP Adamu..wani daga cikin yan-sanda mai dan sauƙin fahimta ya kalleshi yana cewa."Miya haɗaka da wayar CP?" Rintse ido da karfi Ola yayi yana jin hantar cikinshi tana wani irin bala'in motsawa tsabar bala'in da yake ciki, ɗaga hannu yayi yana cewa."Allah na rantse maka Oga ban dauki wayar shi ba." Numfasawa dan-sandan yayi yana cewa."Iphone 14 Pro white color,ko bakai ka dauketa ba?."Shiru Ola yayi banda hawaye ba abinda ke zirara a saman fuskar shi,ganin irin kallon da suke mashi ya kallesu yana girgiza kai yace.
"Eh amman wlh siya nayi ba daukota nayi ba, dan kasuwar da nike kenan a cikin wannan jahar sai dai wayoyi,wlh ban kashe shi ba ranka shidade." Furzar da iskan baƙinshi dan sandan yayi yana cewa."Okay wajen wa kasiyeta?" Kuka Ola ya fashe dashi yana cewa."Wlh Allah bansan suba harkar wayoyi nikeyi nasiyane kawai."Murmushi ACP Sanda yayi yana jinjina kai yace."Bakai ka kashe Adam ba,yanayin ka kawai ya nuna hakan,saidai nawa ka sayi wayar?"sauke numfashi Ola yayi jin Sanda yace bashi ya kashe CP ADAM ba, cikin son barin wajen ya numfasa yana cewa."Dubu ɗari na saye ta." Waro ido ASP Sanda yayi yana cewa."What.?" Ɗaga mashi kai kawai Ola yayi yana share hawaye, girgiza kai Sanda yayi yana cewa."Kenan kai barawo ne." Girgiza kai Ola yayi yana cewa."A'a Yallabai ban sata kayarda dani."
Wani dan sanda dake gefen ACP Sanda ya kwalama Ola wata guduma a saman ƙafa ba ko tausayi,dan shi yafi jin haushin Ola a yanzun akan wa'anda suka kawo wayar dan su daman already tasu ta ƙare,suna shigowa hannu kashe su kawai za'ayi command ne daga sama, amman irin su Ola masu sayen kayan sata sune suke kashe ƙasa da ance ba'a sayen kayan sata to ko ba duka ba za'a rage kaso da wa na satar dan ka sato anƙi saye an barka da kaya ka rasa ya za kayi da kaya cikin biyu za'a samu ɗaya ko dai a maida inda ya sati kayan ko kuma mutum ya daina sayar baki ɗaya,maganar ACP Sanda ce ta dawo dashi tunani yana kallonsu,sake maimaita ma Ola,ACP Sanda yayi yana cewa."Ai kafi barawon tsaye illa domin su ke satowa kuna siya,in banda kana ƙasurgumin barawo taya za'a kawo maka wayar dubu dariya tara zuwa million ka siyeta naira dubu ɗari,Officer ku maida mani shi cell. Ihu Ola ya kurma yana cewa."Ranka shidade kadubi girman Allah kada kasani cell wlh ni ba barawo bane." Marin shi ACP yayi yana cewa."Ina waya take.?" Cikin kuka Ola yake cewa."Na saida ta." Ƙara ball wani dan sanda yayi dashi yana cewa."Ubanwa ka saida mawa.?" Wuntsilawa Ola yayi kamar wata ball wani ya buga mashi belt yana dawowa inda aka tsugunanshi yana cewa."Daniel Okeke." Tsaki Asp yayi yana cewa."Nawa ka saidata.?" Share hawayenshi Ola yayi yana cewa."Dubu ɗari biyu." Shiru kawai ACP yayi dan ya rasa ma mai zaice ma Ola kallon officers yayi yana cewa."Dakyau officer ku tafi dashi."Ola na kuka kamar ranshi zai fita akayi dashi cikin devision din na Niger dan cigaba da binciken Daniel.
YOU ARE READING
NAHIYA TA AREWA
General FictionThe Story of Nahiyata Arewa is the one that comprise the most important things such as Correction,Injustice,Betrayl and Revenge including Entertainment and Education, is a Falatable and testable story.