_*🏝️NAHIYATA AREWA🐄*_
*NA*
_JAMEEY_
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
*PAGE 60*
"Ranka shidade kayi manyan baki."a hankali ta tashi zaune ya jinjina bayansa jikin gado yace"su waye.?"Allah yataimake ka daganin su jami'an tsaro ne."shigo dasu."fita yayi bai jima ba suka shigo a tare bayan sun gaisa Asp Ukorh yace"ya karfin jikin naka"? "Alhamdulillah"yace"masha Allah, ina fatan doctor ya sanar dakai zuwan mu last week"gyada kanshi yayi yace"kwarai kuwa nasani"akwai 'yan tambayoyin da zamuyi maka ina fatan zaka bamu hadin kai"Insha Allah"dafarko dai zanso kafada mani minene sabanin rikicin dake tsananin ka da Yarima Jabbar"numfasawa yayi ya sake gyara zaman shi yace"kamar yanda kasani Jabbar dai 'dan uwana ne, bisa al'ada kowa ya sani duk Omo oban da yakasance Jeri na ukku a cikin wannan Masarauta yana sawa ranshi zai iya zama Sarki, toh sai wannan tsari ya bace ya zama babu wanda zai zama Sarki a cikin mu"miyasa kace haka"murmushi yayi yace"kaima ka tambaya 'dan sanda wai saboda bamuyi nasarar budewar wannan da'kin ba na Okeke shiyasa ake gadarar ba za'ayi mana sarauta ba wannan dalilin shine ga jefa gaba mai girma a tsakanina da Jabbar duk kasancewar sa kanina sai yake ganin shine tafi cancanta da mulkin Masarautar nan"miyasa bazakabar masa ba"Hmm ranka shidade kataba ganin inda kani ya gaji abu ga babba bazai yuyuba abin takaicin ma ba nan Jabbar ya tsayaba sai yazo yana gasa dani akan wadda nike mafarkin zan aura"wake nan"gimbiya Azira 'ya ga Ahmad Okeke"lallai kam duk da shi Sarki Ahmad ya shaida mana cewa wannan shine rigima ta karshe da zata kuma faruwa a cikin wannan alahali kai ya kake ganin abun"? iskar bakin shi ya fesar yace"kamar nima kenan babu abinda zai kuma faruwa da izinin Allah"Madallah, maganar Sarauta idan Allah ya hukunta wanda zai bude wannan da'kin ya bayyana zakuyi mashi mubayi'a"kwarai kuwa, mulki na Allah ne kuma wanda zai gaji wannan kujera tun fil azal Allah SWT ya hukunta babu bukatar jayayya akai"hakane Abdulgaffar muna fatan wannan statement din da muka dauka zai zama hujja akanka matukar wata husuma ta kuma faruwa a cikin wannan Daula"nama fatama, hakan bazai kuma faruwa ba"mungode da hadin kan daka bamu, Allah yakara lafiya"Amin officer thanks"
☆☆☆☆
Yau takama Juma'a babban masallacin kandihar na Jihar Katsina cike yake da tasassar 'yan Adam,iya ganin ka, masallacin yayi shiru ba abinda ke tashi sai hu'dubar limamin masallacin dake tashi cikin zakin murya mai amo da zakin sauraro, hu'duba yakeyi akan zaben da yake matsowa yana jan hankali akan matasa da su kiyayi shiga bangar siyasa ya kara da cewa"yana da kyau iyaye ku kula da ya'yan ku kusan dawa yaran ku ke hudda yau sai kaga uba ya saki ya'yan sa sasaka kai suna yawo batareda aikin yi ba, komai sai ace dole sai gwamnati zatayi alhalin wannan gwamnati bazata iya kula mana da rayuwar ya'yan mu ba, ba zata iya sama masu da aikin yi ba, ya'yan mu basu da wata rana ga gwamnati sai bangar siyasa daga inda sukaci sun manta damu da yaran namu baki da'ya dole mu tashi tsaye mu kula da tarbiyar yaran mu sannan mu sama masu ayyukan yi komai kankantar shi kada mu raina sa'a da zaman banza kwara zama da sana'a komai kankantar sa, daga karshe zan kara jan hankulan mutane akan ya'yan mu mata ya zama dole mahaifi da mahaifiya su kula da tarbiyar yaran su musamman wannan zamanin da keta haddin ya'ya mata ya yawa mu kula dasu sannan mubawa ya'yan mu mata ilimi saboda ilimin 'ya mace bakaramin abu bane zata kasance uwa zata bayar da tarbiyar da mutane sama da dubu zasu amfana da ita tamkar mun ilimantar da al'umma ne Allah yabamu ikon sauke nauyikan dake kanmu zan kara jan hankalan mutane mu dage mu zabi shuwagabanni na gari mutanen kirki wa'anda zasu damu da matsalolin mu masu tsoron Allah sannan mu dage da addu'a kuma mubarma Allah SWT zabin mu Allah yabamu shugabanni nagari masu kaunar talakawa wa'anda zasu kawo mana ci gaba, a cikin kasa baki da'ya....da haka liman ya gama hu'dubar sa sannan aka tada sallah.
FARUQ POV
"Uncle I"Ina jinka 'dan lelena"cikin sanyi murya Faruq yace"Ina neman wata alfarma agareka"baki daya ya maida kab hankalin sa wajen Faruq din yace"fadi koma minene nasan bazai fi karfina ba da ikon Allah zanyi maka shi"ajiyar zuciya ya shide a hankali yace"Ina so ka shige mani gaba in samu cikar burina inaji a jikina idan har ban samu abinda nike so ba rayuwata na cikin garari kuma Ina da yakinin bazan kuma samun kwanciyar hankali ba."cikin tarin tsoro da al'ajabi yake karema Faruq din kallan mamaki yace."minene wannan abun da yake neman ya da'gama da'na hankali har akwai abinda zai gagare da'na kuma a wajena? har akwai abinda nike da shi Wanda zan Gaza sadaukarmaka dashi?" Girgiza kanshi yayi a hankali yace."da ace wannan abun da nike so mallakin kane tabbas bazan taba samun kaina a fargaba ba saidai kash baka da iko da abun saidai kaine silar da zan samu abun! saidai bansan yanda zaka dauki abun ba!"a hankali Uncle I ya janyo sofa din da yake zaune akai ya matso da ita dab da Faruq din yace"koma ya zan dauke shi wannan ba matsala bane minene? Sanar mani damuwar ka Umar"yanda kawun nashi ya Kira shi da ainahin Umar dinsa hakan yakara bashi tabbacin bawa matsalar tashi mahimmancin da yayi yace"Ina sonta uncle nayi imani da Allah ita nafara so kuma akanta na zan kulle shi, saidai narasa ta ina zan fara"wannan karon lamarin Faruq din yasa shi a firgici bai taba kawoma kanshi abinda zai fada masa kenan a zatonsa Faruq din yagama tunanin wata 'ya mace a duniya kasancewar kudurin shi kenan ya rayu da mace 'daya kamar yanda yake plains, abinda yafi daure mashi kai dududu watan Faruq nawa da aure ko shekara bai kullaba zai bijiro da maganar son wata"wacece ita? "Jamila sunanta wallahi ina kaunar ta har cikin zuciya ta."cikin kankanin lokaci Uncle I ya tamke fuska yace"wane taimako kake bukatar inyi maka"firstly kasa Mum ta goya mani baya hakama daddy nasan banda matsala da takawa shi zaisa Fulani ta amince"jinjina kai yayi cikin tarin takaici yace"itafa matar ka damuwar ta ba taka bace? I think she's first person daya kamata nafara convencing tafara baka hadin kafin kowa angaya maka ita din bata da gata.?"ka yarda dani Uncle banaji zan iya boye maka komai araina, walahi ban taba ji ina son Ramlat ba asalima ni nasan ina cutar da ita ne, nakasa mallakar kaina akanta dan Allah kataimake ni in samu yarinyar nan, banajin zan iya loosing dinta koda komai nawa zai kare"what!? mi kakeyi haka Faruq, kada kace baka taba kula Ramlat ba da sunan iyalinka? Kada kace wulakanta yarinyar nan kakeyi Umar? miye haka? Look wallahi kayi gaggawar gyarawa kada hakkinta ya hanaka samun cikar burin naka da kake tunkaho"hawaye masu zafi suka zubo mashi da sauri yasa hannu ya maida su yace"I can't uncle, always am trying to do that but nakasa bansan miyasa bana jin Ramlat araina duk yanda take kokarin kulani nagaza, nidai ka goyaman baya"kana nufin baka da desired akan Ramlat at all"yes! that was am think, the solution zan sallami Ramlat ta aure wanda yake sonta wanda zai bata kulawa fiye dani"you are very stupid Faruq kasan mi kake fada kuwa?" Jinjina kanshi yayi yace"yes I know! Bazan iya cigaba da azabtar da yarinyar mutane a banza ba"wani irin nauyi zuciyan Uncle I tayi ya rasa abinda zaice ma Faruq saidai idanuwan sa daya zuba masa kamar mai neman wani abu a jikin Faruq"why are you looking at me uncle? Talk mana what's the solution ya zanyi.?"Hmm Faruq kenan lamarin ka yafi karfina gaskia, kada ka manta Ramlat jinin kace ita Jamilar da kake magana akai fa.?"bakin shi ya cika da iska ya fesar yace."ita kuma rayuwata ce, I can't live without her."turkashi kazo da rudani mai girma Faruq!"
"Aa uncle babu rudanin dayazo dashi asalima masalaha yakawo a tsakanin mu tunda bai sona ya sauwake mani sannan yaje ya nemo desired dinsa Allah ya hada kowa da rabonsa na alkahiri"cewar Ramlat data sha kuka har saida idanuwanta sukayi luhu luhu tsabar kukan data sha, all his conversation babu abinda bataji kuka takeyi sosai kamar ranta zai fita daga jikinta Allah yasani she love Faruq badly abun harya wuce tunani"OMG"Uncle I ya fada a matukar razane kanshi ya daure tamau baiyi zaton zataji maganar da sukayi da Faruq, he promise to his heart bazai taba bari kowa yaji wannan labarin ba da kanshi zai shawo kowace matsala batareda kowa yaji sai gashi all his plains is destroyed...Kukan data kece dashi ya dawo da uncle I daga duniyar razana da gudu tayi cikin gida tana sharbar kukan ta duk yanda yaso ya dakatar da ita hakan bai samu ba, a fusace ya dawo kan Faruq din ya rufe shi da fada kamar zai duke shi"amma dai baka da imani Faruq kabani kunya wallahi ina ganin ka educated ashe ba haka bane some times you are illiterate wallahi shame on you! yanzun minene ribanka kasan halin da zaka jefa yarinyar mutane, thus for love duk kabi ka lalace cikin kankanin lokaci inaga ita data kwashe shekaru tana sonka? kuma kana mijinta baka sauke hakkinta dake kanka ba, ya kake tunanin zataji a cikin zuciyarta? Kalleni da kyau sannan ka bide kunnuwan ka sosai ka saurareni wallahi ba ruwana cikin sakarcin ka Faruq kaje ka nemi duk uban da zaka nemo ya shige maka gaba wajen mallakar ta amma badai ni ba, ga Ishaq din mahaukata kamar ka, nonsense"hawaye masu zafi suka sake zubo masa muryarsa na breaking yace"sorry Uncle nasan nayi hurting dinku amma ina so kasani babu abinda kudi basa bayarwa I use my wealth and my father's power wallahi saina mallaki yarinyar nan! haba uncle so kake na rasa raina! nagaji"OK haka kace wato bakayi regret akan abinda ka aikatama Ramlat ba ko? her situation ba wani abu bane agareka ba ko Umar? kasa son zuciya Ababa ko? Good komai ya biyo baya kada ka neme ni, kuma sai kayi nadamar cin kashin da kakema yarinyar nan,kaje ka gani idan karfin mulki ko tarin dukiya nabawa mutun komai kuma a lokacin da yaso, can't kaima kasan kana yaudarar kana ne, if I swear to my almighty God na tabbata yarinyar nan ba mamaki batasan kana son ta ba"ajiyar zuciya ya sake shidewa zuciyar na bugawa da karri kanshi yafara daukar zafi yace"kwarai kuwa bata sani ba saidai ayau din nan saina tabbatar da akaina agareta kamar yanda Khalid ke kirana da raggo matsoraci wallahi yau saina nunawa duniya ni Faruq Umar Faruq ba matsoraci bane kuma ni ba raggo bane, kuma kudina da nasabata zata bani komai!"murmushin takaici uncle I kebin Faruq dashi yanayi mashi kallan tsantsar mahaukaci yace"best of luck"cikin tarin takaici ya nufi side dinshi yanajin tsananin bakin ciki aran shi, shiko Faruq glass cups din dake saman dinning ya dinga fatali dasu kasa suna tarwatse karar tayi sanadiyar fitowar Fulani Maryam daga room dinta da gudunta ta iso wajen Faruq din duk irin kokarin da tayi ganin ta dakatar da Faruq daga abun da yakeyi abu ya gagareta saida ya gama tarwatsa kaf dishes din wajen sannan ya fita compound din gidan kamar wani sabon mahaukaci sabon kamu duk hadimai da dogarawan dake cikin harabar gidan kasancewar yau Juma'a sun cika harabar cikin Masarautar kota kansu Faruq baibi ba ya shige motar shi a sukwane yabar masarautar har yana badawa gate man kura gudu yake shatatawa kamar zaibar kasa cikin fitar hankali.Share pls
YOU ARE READING
NAHIYA TA AREWA
General FictionThe Story of Nahiyata Arewa is the one that comprise the most important things such as Correction,Injustice,Betrayl and Revenge including Entertainment and Education, is a Falatable and testable story.