002

14 2 0
                                    

*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*

*NA*

*JAMEEY* 

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*PAGE 2*

Hadiye yawu Hajia kubrah tayi mai kauri tana kallon Camera tana cewa."mu siyasarmu bata san wani abu ba wai shi hamdama balle kuma babakera,dan kuwa kamar yanda na fadi a baya bamu da guri da kuma fata da ya wuce muga mun tallafi tallakawanmu kuma mun basu abun yi sunyi sana'a dan dogara da kansu daga matan har da mazan ma,haka zalika kudin tallakawa basu gamu mu abinda yake a gabanmu ya zamuyi mu fiddo al'ummar jahar Katsina daga cikin bakin talaucin da gwamnatin baya ta saka su a ciki." Jinjina kai Jamila tayi tana kallonta zatayi magana security din Her Excellency ta dakatar da ita ta hanyar cewa."Enough Miss Jamila time is over." Maida numfashi Jamila tayi ba dan taso ba ta maida maganarta tana cewa." Noted." Sannan ta maida kallonta a gaban camera tana cewa." Jama'a al'ummar jahar Katsina mai tarin albarka kun dai ji yanda ta kasance a tsakaninmu da maigirma Her Excellency Hajia Kubrah Yusuf Umar a yau din nan a dakin taro ba abinda zamu ce a yanzun sai mu gani a ƙasa ba fadin ba Allah ya taimaki Al'ummar jahar Katsina baki ɗayanta." Daga haka ta ɗauki Microsoft dinta da ta nadi voice ta saka a jikka sai an gidan tv da suka ɗauka live suma suka fara haɗa nasu kayan suna jindadin kasancewar Jamila a taron dan tambayar da tayi ma maigirma Her Excellency Hajia Kubrah tana cikin zuciyarsu tsoro yake hanasu furta ta.

☆☆☆☆

Gudu sukeyi baji ba gani banda haki ba abinda sukeyi a cikin jejin Allah,ba gida gaba ba gida baya..Sunyi gudu iya gudu har sun gaji ga tarin gajiya da yunwa dake addabar rayuwar su,kwance sukayi cikin masara gefen wani cifji dakyal suke sauke numfashi domin ji sukeyi ransu na masu barazanar ɗaukewa.Yan matane guda ukku a cikin su akwai saurayi guda ɗaya shine mai ɗan kwari a cikin su..kallonsu yayi yana jin wasu hawaye Masu zafi da raɗaɗi suna gangaro mashi a saman kumatunsu bai da yanda zai yi da yana da yanda zai yi da basu wanann gudun na wahala ba,a hankali yayi maganar gudun karda ma a jisu yana cewa."Yanzun minene mafita ya zamuyi da waɗannan mutanen da suke bibiyar mu.?" Ya ida maganar cikin fisgar numfashi dake mashi barazanar daukewa akowa ne lokaci..Matashiyar budurwar dake cikin suce ta fashe da kuka mai ƙona rai cikeda sarewa tace."Nabani yanzun shikenan rayuwar mu tazo karshe mutuwa zamuyi." Girgiza kai yayi cikin ƙara mata ƙwarin gwiwa yace."Kidaina kuka Khadija insha Allah bazamu mutu ba idan har kuwa kinga mun mutu to lokacinmu ne yayi kuma a nan ba da yardar Allah."

Girgiza kanta tayi cikin karyewa tace."Taya zakace haka bayan agaban idanun ka suka kashe Mu'azu sannan sukayima Gambala fyaɗe shine zakace mu kwantar da hankalinmu na shiga ukkuna ni Jimmala."Ta ɗaura hannu bisa kai tana kuka wiwi,dakatar da ita yayi ta hanyar cewa."Ya isa idan sukaji kukanki fa duk kashemu zasuyi wa kikafi shiga tashin hankalin kowa daurewa kawai yakeyi." Cikin kukan da take ba firgici da zallar tsoro tace."Anki karabu dani wayyo innata yauwa Baffana shikenan ni Jummala tawa tazo karshe mutuwa zanyi."Dab dab dab sukaji anyo wajen su da sauri suka soke cikin sako domin boyewa banda haki ba abinda sukeyi suna naman su Jummala a haukace daidai wajen sakon suka tsaya suna dube dube..Cikin fushi wani daga cikinsu ya fara magana yana cewa."Yautai idan muka kamasu kufasa masu kai idan bahakaba tona mana asiri zasuyi." Wanda aka kira da Yautai yace."Angama kai kayi nan,Isi kayi yamma nikuma zan duba ta gabas."Haka suka runtuma ana kare dauke da manyan bindigu da addina kana ganin su kasan ba Allah aransu.

Tunda suka boye cikin cifji ko numfashi mai karfi basuyi, haka su Yautai suka gama neman su basu ba alamun su,saida rana ta faɗi amman basu gan suba kusan tare suka dawo wajen cifjin nan suka tsaya suna maida numfashi Yautai yace."Da alama yaran nan sun mana batan dabo sai dai komawa wajen Oga basu bakaramin hadari bane tunda abin yazama haka zamu kona wannan Nahiyar koda yazo zaiga lallai ba neman wasa mukayi masu ba,kusan waye Muhi ba san ragi ba kuma baida sabo kunji yanda za'ayi..Daram haka kirjin su ke bugawa jin za'akona inda suka boye tabbas sunsan asirin sune zai tonu gashi kowa yanason ya tsira da rayuwar shi Khadija tafara shehshekar kuka da sauri  Nura ya  toshe mata baki da karfi duk tsoro ya kamasu sunaji sunfara sama wajen wuta banda faduwar gaba,tsoro da tarin firgici ba abinda su Jummala keji a wannan lokacin ga wuta sunaji tafara kama wajen ga tsoron zalincin da suke gudu wajen azzalumai musamman mata dake fama da damuwar fyaɗe a kowane lokaci.

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now