029

5 1 0
                                    

_*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*_

*NA*

_JAMEEY_

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*PAGE 29*

Kwanan Ubaidu biyu rabon shi da gidansu tunda yaima Ba'ba Ladidi tas bai kuma waiwayar su ba zaune yake cikin wani kango inda suke kaurancin su shida abokan sa,ba abinda matasan keyi sai cakewa da kayan maye iri iri Ubaidu ya dubi Tosi yace."ya kukayi da mai gida.?"Hayakin dake cikin bakin shi ya busar yace."Oga mutumin nan fa ya sharemu nema yake yai mana wasa da hankali." Jinjina kai Ubaidu yayi yana firzar da hayakin wiwi ta baki ta hanci yaƙin yake fita yana kallon Tosi yace."Ai kuwa daya rainama kansa wayau muddin yace zaiyi wasa da Ubaidu." Jinjina hannu Tosi yayi yana cewa."gaskia ne Oga."Cigaba da sheke ayar su,sukeyi dayake group din su Ubaidu su goma ne shidda daga cikin su musulmai ne sai hudu cristian ne suna cikin hidimar su,sukaji su Jigiri sun masu dirar mikiya da makamai suka fara kai masu sara da addina."Kam bala'i."Ubaidu yace yana zare takobi ya afka cikin dabar su Jigiri suka fara fafatawa."sai mun karku tunda kuka taba mani yarana."cewar Jigiri da suke bata kashi tsakanin su da Ubaidu,Cikin kankanin lokaci sun har mutse unguwar da hayaniya kaima junan su sara suke baji ba gani wajen yacika da mutane anrasa mai raba matasan rigimar da sukeyi abinka da Kauraye.kafin kace kwabo har motocin yan sanda sun iso wajen baki ɗayan su suka tarwatse aka kama na kamawa wannan karan harda Ɗahiru Kure aka kama dayawan su sunjima junan su ciwuka haka aka jefasu cikin mota da akema kirari da shiga da kukan ka fita da Allah ya isa,ba inda aka tsaya sai devision aka watsa su bayan kanta bada jimawa ba DPO na devision din yasa aka dauki statement Jigiri ya gaya abinda akaima yaran sa daukar fansa yazo,shima kure ya faɗi abinda ya hadasu,bakaramin mamaki DPO yayi ba da yaji dalilin tarzomar tasu cike da tausayin su DPO yake kallonsu yana cewa."Yanzun akan Bangar Siyasa zaku dinga jima junan ku ciwuka kuna bata rayuwar ku duk akan Siyasa.?" DPO ya ida maganar a fusace yanda yaga sun batama junan su jiki duk akan siyasa,cigaba da cewa DPO yayi."dan haka zaku dandani kudar ku daman kuke tadama Jama'a hankali."Cell aka sasu aka hau jibgar su kamar ba gobe,shiko Ubaidu jikinshi duk jini ya dawo gidansu,yana shigowa ya tadda mahaifin shi da kakar shi,ko sallama baiba ya fado cikin gidan ya nufo dakin shi Hannatu da fitowar ta kenan daga bandaki taga yayan ta cikin mawuyacin hali da gudu ta tare shi tana kuka tana cewa."Yayana miyafaru wa yai maka haka.?"ta tambaya tana cigaba da kuka,kama hannun Hannatu yayi yana lallashin ta maganar Ba'ba Ladidi ta katse mashi maganar da yai niya."uban wa zai mashi haka mugun halin sane yajaza masa kuma baiga komai ba tunda ya dauko hali irin na uwa ina dalili wannan yaro da haihuwar ka gwara barin ka,nikam dai Isuhu ka haifa mani bala'i shiyasa naki yarda da auren maiyyar yarinyar nan gashi ta haifa mani yuyuyu ya'yan Allah bani." Tunda Ubaidu ya shigo mahaifinsa yake kallonsa zuciyarsa cike da damuwa dan duk duniya idan akwai abinda yake damunshi bai wuce irin rayuwar da Ubaidu yake ba,baida yanda zai yi ne sai dai yana mashi addu'ar Allah ya shiryeshi ya maido shi akan hanya, kallon Ba'ba Ladidi yayi yana cewa."Haba Umma ya'yan nawa kike jifa da waɗannan kalaman.?"Isuhu ya ida maganar cike da damuwa jin abinda mahaifiyar sa ke jifan ya'yan sa dashi shiko Ubaidu daskare yayi yanajin saukar kalaman Ladidi har cikin kwanyar kansa."gantalallu wadannan tsinannun yara inama ban hada komai da kuba haka zaku lalace."wannan karan Ubaidu yakai karshe ga kulewa daman ga haushin farmakin dasu Jigiri suka kawo masu yanaji ga bala'in Ladidi musamman kalaman da take jifansa dasu shida kanwar sa.

A hankali yafara tako ya iso gaban Ladidi daketa faman sababi ɗanta nabata hakuri yarasa yanda zaiyi da bala'in mahaifiyar sa ihun da ta saki shiya dawo da Isuhu a cikin tunaninsa ganin Ubaidu da sharbebiyar adda ya dabawa Ladidi ita a hannu take jini ya balle zaro ido Isuhu yayi yana yin kaisu yana cewa."Kai Ubaidu uwar tawa zaka kashemin?"Isuhu yace yana kokarin tare ɗan sa."saina kasheta ban kaunar ta nima ita ta kashemin tawa uwar."Yai kan Ladidi da adda da gudu ta afka daki ta rufe dakin tana fasa ihu,shima Isuhu da sauri yasha gaban Ubaidu ya sharara mashi maruka har biyu yana fidda uban huci."dakarni nace."Ubaidu ya daga hannu da niyar rama marin da mahaifinsa yai masa sai kuma yafasa,sake dauke shi da mari Isuhu yayi yace."dan uban ka da raina zaka nemi kashemin uwa iyeh ka gurbata rayuwar ka a banza."Kallan shi kawai Ubaidu yakeyi yana jijjiga kai yace."kaci darajar kana mahaifina wallahi yau da saina sauke hannun ka Baba tunda nike ba wanda ya taba nuna Ubaidu da yatsa ban sauke saba bare akai ga marina."shekeke Isuhu yayi yana kallan Ubaidu aransa yana ayyana anya Ubaidu bai bugu ba dagani baida hankali." Numfasawa Isuhu yayi cike da damuwa yake kallon Ubaidu yana cewa."ka lalata rayuwar ka Ubaidu yanzun haka dagani a bige kake." Cike da takaicin hanashi karasa yake cewa."Kaga waccen tsohuwar itace ta lalata rayuwar Ubaidu bani ba kuma saita kwashi adashen ta."jikin Isuhu yai sanyi ainun ganin tsantsar tsanar da ya'yansa suka yima mahaifiyarsa tin yarintarsu har gashi sun girma ba abinda ya sauya a ciki.

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now