078

6 0 0
                                    

_*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*_

*NA*

_JAMEEY_

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*PAGE 78*

Koda Journal Jamila ta iska cikin gidan Jaridar tasu ba karamin mamaki ne ya kamata ba ganin ma'aikaitan Jaridan Baki da'yan tsaitsaye cirko cirko duk wanda ka kalla a cikin su zakasan yana cikin farin ciki marar misaltuwa musamman Journa Umar Y Umar da yafi kowa daukin ganin Jamila sai faman washe baki yakeyi kamar gonar auduga da sauri ya isa bakin motar ta ya bude mata door yana sakar mata wani irin tsadadda murmushi yace."Welcome back to our company Journal Jamila Abubakar you're highly welcome."ya ida maganar yana kara fadada annurin fuskar shi Kai kace anyi mashi wani irin babban  albishir ne."Thank you Sir."Nice to see you again as Hikima Journal member Bismilla." Ya ida maganar yana nuna mata wajen da CEO din Journal din ke tsaye suna sakar masu murmurshin jin dadi, a hankali suke taku ita da Umar Y kana ganin fuskokin su bako shakka zakasan bakaramar kewar juna sukayi ba."Good morning,sir."Jamila ta gaishe da ogan nasu cikin girmamawar data dace dashi."morning J.Jamila,am happy to see you again." Jinjina mashi kai tayi alamun nunajin dadin ta tace."Thank you Sir."abokan aikin nata ne sukaita zuwa inda suke tsaye suna yi mata welcome kowa ya na nuna mana tsantsar farin cikin sa na dawowar ta ALLAH ya sani bakaramar kewar ta sukayi ba months din data kwashe basu ganta takusa getting one year,wasu rabon su da ita tunda y'an kiddinafas suka sakota da sukaje mata murnar dawowa sai yau,ba karamin kyau tayi masu ba idan kayi mata kallo da'ya dole saika sake duban ta sabo da kyau na daban tayi masu Banda glowing da black skin dinta takeyi ba kadan bakin fatarta ke Kara bayyana tsantsar kyau na Jamilar ba."muje ciki ko."? Muryar CEO din ta katse mata murmushn da take ta faman yi wanda ba zata  iya kayyade a dadin yawan sa ba tunda ta fito a gida take faman jinta cikin nishadi more especially data hadu da mutane masu mahimmanci a tattare da ita domin zaman amana takeyi da abokan aikin ta,Kuma da zuciya da'ya gaba yayi duk suka maye mashi baya cikin katon gidan Jaridar wanda yake tashe a duka fadin Kasar Nigeria ba na biyun shi bakaramin Journal ba ne shiyasa suke da tarin followers a ko wace kafar sadarwa domin su open ne komai basayin rufa rufa saboda gidan Journal ne da yake da different parts har da VIP section ke akwai na y'an Kasuwa da sauran part's wanda basu kyalkashin kulawar gwamnati zaman kan su yakeyi,anan ne ake gabatar da Shirin dake tada hankulan mutane da dama musamman kusoshin gwamnati wato Shirin Tafaru takare shiirin dake cin kashin kanshi....Wani katon hall ne suka suka sauka Baki dayan su yaji decorations kowa ya samu waje ya zauna inda Jamila itama ta zauna cikin abokan aikin ta mata saidai mamaki kawai takeyi tana alajabi miye za'ayi anan din ita dai tasan duk lokacin da aka shigo cikin wannan Hall ba karamin abu mai mahimmanci ne za'a gudanar yawanci sukan yi amfani dashi onces in year shima idan za'a karrama ma'aikaitan su ko Kuma idan sunayin shagalin anniversary na Journal din sukan bude hall din domin abokan aikin su y'an Jaridu da sauran masoyan su sukan zo domin taya su murna."Journal Jamila."ta tsinkayi sanyayyar muryar sa cikin dodon kunnen ta a hankali ta mike tana haurowa saman high table inda manya manyan Journalist din suke zaune aka nuna mata sit ta zauna murmushi ta sakewa Umar inda yayi gyaran murya yafara magana a tsakanake yake cewa."I'll show my great thanks to almighty God,who show me these wonderful and special day, I'm very very happy, my words can't explain how I feel in my mind,only I say Alhamdulillah alhamdulillah, I'm sure duk wanda ke wannan waje fuskan sa kadai zai shaida maka irin tarin farin cikin da muke ciki Alhamdulillah,kamar yanda kowa yasan reason na taruwar mu anan waje domin mu karrama babbar ma'aikaciya, abokiyar aiki, masoyiya Kuma hazikar ya'r Jaridan nan wadda ta kashe dare da rana domin yin aikinta da gaske da amana batare da gajiyawa ba ba kowa bace face.... d'an maida numfashin shi yayi yana kara gyara tsayuwar shi ya sake sauke sanyayyar ajiyar zuciya yaci gaba da cewa."Journal Jamila Abubakar." Baki daya wajen aka dauki tafi,duk wanda ka gani kasan yana tsantsar Jin dadin program din da ake yi inda y'an Jaridu na sassa daban daban ke daukar abun live ana haskawa direct gidajen television kusan ko ina gwada shirin akeyi, tafin da aka Kuma saki ne ya dawo da Jamila cikin nutsuwar ta tabbas sunyi mata bazata tabbas zatace bazata ce wannan domin Bata taba zato da tsammani wai ita Jamila har takai wannan matsayin da za'a karrama ba Batare da wani babban dalili ba,duk da tasha ansar Awards da dama na karramawa hardai da na best Journal of the year saida ta amsa na Kasa baki da'ya saidai wannan karramawar da ake mata an shammace ta Kuma anyi surprised din ta fuskar ta kadai ta shaida hakan domin da tasan za'ayi mata irin wannan bazatar data shiryawa abun."Journal Jamila biography." Abun da ta Kuma ji ya daki dodon kunnuwan ta a karo na biyu ta sake maida duban ta akan fuskar Umar da yaketa rattafo tarihin ta musamman akan aikace aikacen da tayi da irin gwagwarmayar da tayi arayuwa wanda ya danganci aikinta yaci gaba da cewa."yana da kyau kowane d'an Jarida yayi koyi da J.Jamila musamman irin jajircewr ta,akan aikinta ba abun da bazatayi ba dan ganin ta inganta aikinta akan gaskia da rikon amana,tayi aiki a gidajen Jaridu daban daban har ALLAH yakawota wannan Journal mai tarin albarka a shekarar 2021 zuwa yanzun din nan a matsayin ma'aikaciya kowa yasan irin kalubalen da J.Jamila ta fuskan ta akan wannan aikin Amma duk da haka,bataji gwiwowinta sun sare ba ta sake dawowa akan aikinta akaro na biyu duk dan saboda al'umma saboda aikin Jarida aiki ne na al'umma duba da haka wannan gida na Journal ya shirya kwarya-kwaryar walima gami da karramawa ga wannan hazikar ma'aikaciya Kuma mentor  ga mutane, da haka zan maida ragamar wannan taro ga CEO na wannan Journal domin cigaba da aiwatar da wannan program thank you."tafi suka sake dauka cike da kamewa J.Umar ya koma sit dinsa ya zauna wanda ke facing na Jamila yana aikin kallonta ko keftawa baison yi danma yana basarwa kasancewar yasan direct program akeyi, shugaban Hikima Journal din ne ya taso ya fara da cewa......

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now