028

6 1 0
                                    

_*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*_

*NA*

_JAMEEY_

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*PAGE 28*

Jirgin Sanda ne yai landing a cikin Niger International Air Port, basu jima da sauka ba motocin sukazo daukar shi,cike suke da Jami'an tsaro kowa hannunsa dauke da gun kirar AK 47 cikeda sassarfa suka budema Sanda motar tsakiya ya shiga kirar Rang rober a sukwane sukayi waje daga Air port din zuga guda, a hankali suke tafiya kasancewar Sanda mutun ne da baison hayaniya sosai yafi son komai yayi shi a tsanake sanin dokar uban gidannasu harta bi masu jiki."Guest House."yace yana daukar ruwan goran dake aje gefen sa a nutse ya bude murfin yasha yana sauke ajiyar zuciya a hankali drivernsa ya karkata akalar motar sa zuwa guest house dinsa hakan yaba abokan tafiyar tasu dama maye masu baya har katafaren gidan nasa dake cikin unguwar GRA danna horn sukayi take gate man ya bude masu gate one by one suka shiga kowa yai parking.

Wangale mashi kofar motar akayi a nutse ya sako kafar sa kasa yana shakar sanyayyar iskar dake fesowa a hankali tana ratsa shi runtse idanun sa yayi kafin ya bude a nutse yake takowa cikin kamewa da nutsuwar data zame ma Umar Sanda jiki tunkan ya iso har sun bude mashi kofar shiga falorn,da sallama abakin a ya shiga sanyin Ac da kamshin turaren sa suka hade lokaci ɗaya wani sanyayyan kamshi ya ratsa zuciyar sa zama yayi saman kushin yana sauke ajiyar zuciya mai sanyi ya maida kallansa kan abokan aikin sa yace."Sp ya case din nan ya kwana.?" Numfasawa Sp yayi yana cewa."Ranka shidade wallahi ba abinda ya sauya jiya iyau yanzun basu communicating da kowa abin takaicin ma yanzun ko tracking dinsu akayi ba'a ganin location." Furzar da iskan bakinshi Sanda yayi yana cewa."Okay insha Allah wannan karan komai zaizo karshe ni kaina tafiyar nan da nayi hankalina na nan da case din nan nike kwana nike tashi a raina." Jinjina kai Sp yayi yana cewa."Gaskia ne Oga wannan karan komai zaizo da sauki."Allah yasa."Ameen."ya amsa sannan ya fita dan ba Umar damar hutawa suna tafiya ya shige bedroom dinsa ya rage kayan jikin sa,sannan ya shiga wanka fitowarsa wanka keda wuya wayar sa tahau ringing,murmushi ya kawata fusakar ganin mai kiran shi,kira na biyu ya dauka yana tsane ruwan jikin sa yasata a handsfree."Mutumi na barka da dawowa."murmushin ya kuma yi yace."mun kusa isowa dai."

"Korafi bai karbuba raina nabani kadawo" numfasawa Sanda yayi yana cewa."Abbas matsala kacan ka daidai ban jima da dawowa ba."Okay bari inbari ka huta gobe zan shigo in Allah yakaimu."Girgiza kai Sanda yayi yana cewa."No ina bukatar ganin ka,kasan ko baka zoba zanzo kashigo anjima." Numfasawa Abbas yayi yana cewa."Alright Allah yakaimu kahuta lafiya mutumina."Ina jiran kafa."Okay."Yana aje wayar yafara mulke jikinsa da mayuka masu kamshi da taushi,feshe jikin sa da turaruka yayi sannan yaje gaban wardrope ya dauki inners dinsa yasa jallabia ya zira white color ya koma saman gadon sa ya kwanta rufe idanun sa yayi kamar mai bacci."Thank you Sir."abinda sautin kunnen sa suka juyo masa kenan banda gizo ba abinda kyakkyawar fuskar ta ke masa a duk lokacin da zai rufe idanun sa da niyar bacci banda zazzakar muryar ta ba abinda ke yawo a cikin kunnuwan Umar Sanda musamman lokacin daya ware kansa domin hutawa,bacci ya karacewa idanun sa,tashi yayi daga kwancen da yake ya zauna ya rasa mike masa dadi pillown dake gefen sa ya dauka yai holding hannayen sa dashi ya tsurawa silin ido kamar mai nazari."Miyasa zaki addabi rayuwa ta? Miye hadina dake? tun ran dana fara saki a idanuna baki kara bari na zauna lafiya mike tare dake?baccina ke tunina ke komai ke! lived me alone."Tashi yayi ya dawo falor ya zauna ya rasa mike mashi dadi a duniya.

☆☆☆☆

"Umar kaga abu kamar wasa wankin hula na neman kaimu dare." Firzar da naunauyen ajiyar zuciya Umar Y yayi yana cewa."Nima abun nan naci mani tuwo a kwarya Ahmad abun kunya an wata da daukar Jamila amman gwamnati ta kasa komai matsayin ta na Yar Jarida a haka akeson mu saka kanmu a halaka gwamanti ba watsi da lamaruran mu." Wani kallo Ahmad yayi ma Umar Y yana cewa."Haba Umar kada ka manta kune gwamnatin nan." Tsaki Karami Umar Y yaja yana cewa."hakan ba damuwa ta bane ita gaskia ɗaya ce daga kinta sai bata dan mahaifina na governor ba zai hanani kin fadar gaskia ba." Jinjina kai Ahmad yayi yana cewa."Shikenan amman sai inga tana iyakar yinta." Cike da takaici Umar Y ya kalli Ahmad yace."Ba wani iyakar yinta dubi kaga masu garkuwa da mutanen nan da yawan su fa suna bayyana kan su,ko kaga suna ciniki da gwamnati kamar wata tsarar su kai kasan abin akwai rainin wayo a ciki, wallahi da ace za'a hada karfi da karfe da yanzun agama da mutanen nan."Murmushi Ahmad yayi ganin yanda Umar ke kwarema gwamnati baya kai kace baida hadi da ita."kaidai tunda aka dauke masoyiyarka ai dole gwamnati zatayi baki a wajen ka duk da tana iyakar kokarinta." Dan murmushi Umar yayi yana cewa."No wlh koda ba adauke Jamila ba kai kasan muna shiga cikin al'umma munajin halin da suke ciki jibi kaga rugar Hu66age tunda aka sace masu ya'ya watanni nawa suka kwasa a hannun mutanen nan an kashe wasu anyima yaran su fyade abin takaici akwai wata yarinya Jummala sunki ba data wai shugaban su ya aure ta,jibi shakiyanci har gobe inajin lamarin nan a cikin zuciya dan dai banida karfin iko da sai inda karfina yakere akan wannan case abin tausayi yarinyar ma maraniya ce ba uwa ba uba." Cike da damuwa Ahmad yake cewa."Allah ya kubutar da dukkan daukakin al'ummar musulmai baki ɗaya su kuma Allah ya shirye su."ameen addu'ar kenan."Kaga tunda mungama programs din nan kwanda intafi gida yau ba night duty."Gaskia kam kwara aje a hutama rai kuma."Oga kahuta lafiya sai dasafe."Allah yakaimu."musabaha sukayi ya tafi,shi kuma Umar ya cigaba da aiki.

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now