_*🏝️NAHIYATA AREWA🐄*_
*NA*
_JAMEEY_
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
*PAGE 63*
_UBAIDUDDEEN_
"Inajinka kwaro"yayi maganar cikin tsananin sanyin rai, daga dayan bangaren aka ce."yanzun haka maganar da nike maka ya koma tafiyar Jigiri kullum yana tare dasu a gaskia mai gida ina takaicin gayamaka wannan labarin yanzun haka." Cikin hargagi Ubaidu yake cewa."babban bala'in nan ni Kure zai cima amana? Duk yardar da nayi da 'Dahiru ya zama dole yau ko gobe in sauka cikin Sumaila.?"cikin tsananin bacin ran da bai taba fadawa a cikin sa yai maganar domin baida makiyi sama da Jigiri ya tsani duk wani abu da zai hada masoyin sa da Jigiri numfasawa Kwaro yayi yana cewa."kaina saman wuyana mai gida, dole ranka ya baci gaskia Ova 'Dahiru bai kyauta ba sam."ya isa kabar komai a hannuna idan kere na yawo zabo na yawo tabbas wata rana za'a hade indai nine nida Jigiri muzuba mugani daga nan har ranar yaumit tanadi, billahillazi la'ilaha illahuwa saina zamema Jigiri kadangaren baki tulu."Allah ya huci zuciyar ka mai gida yanzun umurnin ka nike jira."duk wani shige da ficen 'Dahiru."angama mai gida,duk muna kewar ka fa."kashe wayar yayi batareda yace komai ba wani irin bakin ciki mai tsanani ya turnike zuciyar Ubaidu ba abinda yake bukatar sha a yanayin daya tsinci kanshi kamar sigari yarasa inda zaisa kansa."Jigida."ina jinka mai gida."asamo mani sigari."kallan juna akayi tsakanin Jigida da Dila."akwai matsala mai gida bai...."ya isa."ya daka mashi wata irin uwar kara har saida falorn ya amsa kuwa yace"sigari zaku bani."shiru yayi yana kallan Umar dake tsaye gefen kafar bene ya harde hannuwansa jinjina masa kai yayi alamun su bashi."Jigau."da sauri ya mikama Jigida kwalin sigari shi kuma yaba Ubaidu, kamar marar hankali ya kunna sigari yana fara zukarta yana rufe idanunsa da sukayi masa nauyi tsabar bacin rai, wayarsa ta kuma daukar ringing da sauri ya dauka duk da bakuwar number ce hakan bai hana dauka."Yayana."wani irin razananniyar faduwar gaba ta dira a kirjin shi har saida ya dafa zuciyar shi."Ya Deeni kana jina.?"da saurin shi ya mike tsaye yana cewa."Hannatu ina kika samu waya.?"kuka tafara yi mashi ko amsa bata bashi ba maida wayar yayi cikin speaker yace."ki daina kukan nan Hannatu mi akayi maki." Cikin kuka Hannatu take cewa."Baba Ladidi ce wallahi ta tsaneni nagaji Yayana."Yar lelena ki daina kuka nakusa dawowa gareki kinji indai Ba'ba Ladidi ce ki barta da aniyar ta da sannu mugun halin ta zaiyi ajalinta."kullin cewa takeyi saina lalace sai na mutu da bakin ciki."ina Baba.?"kukan ta kumayi tace."baya zama fa kuma bata barin shi yayi magana."rufe idanuwan sa yayi ya fesar da iskar bakin shi yace."Hannatu."na'am"kina son zuciya ta ta tarwatse.?*a kidime tace."Aa."idan ko har baki son haka ta kasance toh ki daina yiman wannan kukan kina karamin bakin ciki saman bakin ciki bazan iya jure kukan ki ba, kema kin sani."toh Ya Deeni na daina.'yauwa 'yar leleta, yanzun ina kika samu waya bana hanaki fita waje ba, kin manta inada makiya bana son suyi maki wani abu.?"ajiyar zuciya ta shide tace."ba fita nayi ba Ya 'Dahiru ne ya siyo min ita ya bani."Ke! kina da hankali? kinsan abinda kike fa'da mani kuwa? ubanwa yace ki amshi abun Kure.?"jikin Hannatu ya dauki rawa tunda take bata taba ji yai mata ihu irin haka ba."kayi hakuri Yayana naga Ya 'Dahiru ne shiyasa na amsa."Dahirun banza zaki fa'daman shine ya baki! ni banfiki sanin shi ba zan ballaki Hannatu."kuka takeyi sosai tace."kayi hakuri zan mayar masa Allah."mtsww."kashe wayar yayi ya wurgi da ita saman tiles ya fasa uwar kara baisan sanda ya ciro askar dake cikin takalmin shi ba ya dabawa hannun shi ita take jini ya fara zuba da sauri su Dila sukaci dunun Ubaidu suka rike shi kam sannan Jigida ya amshe askar kasa ya zube yana kuka mai sauti, bakaramin tsorata sukayi ba da ganin yanayin Ubaidun, a hankali Umar ya karaso inda yake ya samu kujera ya zauna ya kalli Dila yace."kira mani Dr Hamid."toh Oga."Salisu akwatin gaggawa."angama Boss"cikin sanyin muryar dake nuna tsantsar tausayin shi ga Ubaidu yace."Deeni."a hankali ya dago kanshi ya kalli Diga."koma saman kujera ka zauna."tashi yayi ya zauna hawaye masu zafi na sauka saman kuncin shi."ansar first aid box din yayi ya bude ya ciro auduga da hydrogen ya riko hannun Ubaidun yafara goge jinin dake zuba yace."idan rai ya ɓaci Ubaidu bai dace hankali ya gushe maka ba, ka zama ma mallakin zuciyar ka akoda yaushe kada kabari ta zama mai mallakar ka kaifa Jarumi ne, kadaina saurin karaya irin haka."hawayen fuskar shi ya share yace."Haba Yayana kada kamanta 'Dahiru fa akace maka raunina ne tare da Kure na tsani cin amana."murmushi Umar yayi bayan ya gama tsane mashi jinin yace."kana iya zama da makiyan ka, kuma kayi masu halacci duk abinda zakayi ka dage ka tsayawa iya gaskiar ka koda kowa zai ki'ka, inada yakinin yanda ka damu da Kure shima ya damu dakai, ina so kasani idan ka bibiya tuggu aka hada maku da sannu zasu kashe kansu da kansu."sake share hawayen da suka zubo mashi yayi yace."ina fatan haka mai gida bana fatan 'Dahiru yaci amana ta."Jinjina mashi kai yayi bayan ya amsa sallamar Doctor Hamid ya nuna mashi sit ya zauna yace."kanina zakayima dressing.'angama mai gida."fara yima dressing din yayi bayan yayi mashi allura saman ciwon bai wani bata lokaci ba ya gama mashi aikin."mai gida na gama."Jigau."da sauri ya iso ya mikama Dr Hamid kudi."nagode mai gida."daga mashi hannu yayi sannan yai mashi izinin tafiya."Shaye shaye yafi komai saurin lalata rayuwar matashi, sannan shan taba na illa ga rayuwar 'dan Adam kasancewar ka Jarumi kuma matashi mai jini a jika bai kyautatu ba kasha sigari da suna samun sukuni a lokacin da kake cikin bacin rai haba Deeni ina laifin kace"Inalillahi wa'inna ilahirraji'un,yafiye maka wannan sigarin daka nema saboda ita kalmar Inalillahi wa'inna ilahirraji'un tana maganin duk wata musiba sannan tana sanyaya zuciyar duk wani mai imani, ka kiyaye Deeni saurin fushi ba naka bane, yanzun minene laifin 'Dahiru danya siyama Hannatu waya baka dauke shi 'dan uwan ka ba.?"dafe kanshi yayi yace."shidin Jinina ne kuma ina kaunar shi, nayi hakane domin na bakanta mashi rai kamar yanda ya bakanta man a halin yanzun duk abinda Kure yai mani labarin dana samu a yau din nan yafi yiman ciwo a cikin zuciya ta."kazama mai yawan yafiya, wannan itace siffar musulmi na gari"insha Allah zanyi abinda ka fada mani."shikenan kaje ka huta kada ka kuma kokarin illata kanka haramun ne."insha Allahu mai gida."ranka shidade ga wayar shi."amsa yayi yana duba wayar yace."Salisu kasa akawo masa waya wannan ta lalace."nagode ranka shidade saidai akwai abubuwa masu matukar amfani a wajena dadai angyaro mani ita."Salisu a gyarota sannan ka siyo mashi wata."toh ranka shidade."tashi Umar yayi ya wuce da'kin sa.
YOU ARE READING
NAHIYA TA AREWA
General FictionThe Story of Nahiyata Arewa is the one that comprise the most important things such as Correction,Injustice,Betrayl and Revenge including Entertainment and Education, is a Falatable and testable story.