087

6 0 0
                                    

_*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*_

*NA*

_JAMEEY_

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*PAGE 87*

Zaman Hannatu a gidan su Jamila bakaramar shakuwa bace sukayi da juna ba, sosai take jin dadin zama da Hanne a kallah satin Hannatu biyu a gidan su Jamila yau dai tunda suka tashi da wuri sukafara gyara gida sannan suka maida kalaci inda Hannatu ke soya Arish ita Kuma Jamila tana masu miyar liver with egg Koda Hannatu ta gama isowa tayi wajen Jamila tana mai cewa "Sannu Anty nah."murmushi ta sakar mata tana cewa."yauwah kanwata kin zuba dankalin a kula."? Jinjina mata Kai tayi tace "eh na zuba"d'an shiru Hannatu tayi sai kuma tace "Kai Anty wannan wace irin miyace haka tayi kyau ga taji Karas da albasa ga uwar hanta gaskia kudai y'an birni kunacin dadi,nikam dai bantabacin irin wannan abun ba,wai shi wannan ruwan Kwan soyashi zakiyi ne"? Dariya kadan Jamila tadan yima Hannatu tace."Aaa ba soyashi zanyi ba so Nike da ruwan miyar ya d'an Kara tsanewa sai in zuba Kwan saman miyar sai in rufe kamar yayi minti biyar haka,zakiga kwan duk ya taso sai in motse shi cikin miyar har saiya hade da hantar cikin miyar shikenan nagama sai in sauke shine mahadin dankalin da kika soya mana."washe baki Hannatu tayi tana cewa."Amma dai yau zamuci dadi yasin irin wannan abu."murmushi kawai Jamila ta kuma tayi tace."yanzun ki dauki wancan dankalin kikai falor ki aje sai kije ki shiga wanka Kinga yau lahadi Kuma gobe zakifara zuwa makaranta kintuna abin da yaya Umar ya fadamaki jiya a waya dai."Eh Anty natuna zanyi karatu sosai nagane duk abubuwan da kika koyaman bazan bawa Yaya Umar Kunya ba insha ALLAH"Good girl,kije kifara wankan kafin ingama so Nike dana Ida wannan aikin nayi wanka munayin kalaci zan kaiki salon."cike da mamaki Hanne ke kallan Jamila kafin tace."Anty banyi sati ba kin kaini wannan abun fa aka sakamin Kai a cikin na'ura."dariya ta kece dashi tace."Kai Hannatu kinada kayan dariya toh kwantar da hankalin kinba sakaki za'a sakeyi ba kitso za'ayi maki Nima ina so nayi sabon kitso."sihirtacciyar ajiyar zuciya Hannatu ta sauke tace."Toh Anty harnaji dadi ai wannan abun da aka samin Kai a ciki,har kunnena nema yayi ya kona mani dan ma matar nan tagani tasa na cire y'an kunnena ai da shikenan nazama mariganya ma."dariya kawai Jamila tayi tace "yanzun dai wuce kitafi na biyeki mun cinye lokacin ma dai,kinyi sauri fa."toh Anty."da haka Hannatu ta nufi dakinsu,itako Jamila dariya kawai takeyi tana mamakin kalar shirman Hannatun gata sangattaciyar gaske duk su Ubaidu sun shagwabata ga Umar ya daura da tashi sangartar hakama Umma komai Hanne yanzun itakam ta zama ya'r kallo an daina yayinta baki da'ya ma,da haka ta sauke sos din ta zuba a dish sannan ta hada masu flats da Kai falor ta daura ta dauki flask na black tea da suger takai ta aje saida ta kimtsa komai sannan ta koma daki tana shiga ta iske Hannatu tana kwalliya wanka kawai ta shiga itama bayan ta amsa sannun da Hannen ke jira mata bata wani ba'ta lokaci ba ta shige wankanta."Hannatu."Umma ta kirata wanda fitowar ta kenan daga dakin da saurinta Hannatu ta mike tana"na'am."ta nufi falorn Koda ta fito zaune ta iske Umman hannunta rike da carbi tanaja,har kasa Hanne ta duka tana mai gaishe da Umman cikeda sakin fuska ta amsa tana."Haba Auta kin shige daki abun ku gashi dai kungama hada breakfast ina laifin ki zauna kici abincin ki ba sai kin tsara jiraye jiraye ba kinsan dai Antin ki hidindimun ta yawane dasu."da sosa kai Hannatu tayi tace." Bakomai Umma yanzun ma zata fito ai ma."ai shikenan sai mu zauna jiran nata ai,yanzun fa goma ta kusama."rufewar bakin Umma ke da wuya Jamila ta fito tana gyara veil din Abayar ta kunnenta kanne da waya tana cewa."yanzun nan kuwa zamu fita ranka shidade."murmusawa kawai tayi tana mai cewa."ba matsala idan ka dawo ko zuwa karfe bakwai ne kana iya zuwa."Mai daba duban ta tayi wajen Hanne dake waya da hannunta tace."xasuji in sha Allah safe trip."morning Umma na."ajiyar zuciya kawai Umma ta sauke tace."Hmm Jamilatu kenan hala ke da Sandan ne ko."? Zama tayi tana cewa." Eh wlh shine zuwa anjima yace zaizo bayan magrib."toh Allah ya kaimu lafiya."Ameen, Baba fa."? Jamila ta tambaya tana zuba masu breakfast din."yau karfe bakwai ya fita,meeting zasuyi."Wayyo Babana bawan Allah."sannu mai Baba"Allah ya maido shi lafiya."cewar Hannatu sukafara kalacin su a nutse saida suka gama sannan suka maida kayan kitchen suka dawo suka fara yar fira da Jamila inda Hannatu ke basu labarin Yayanta kowa yana Jin yanda take ta kewar Ubaidu sudai nasu suyi dariya wani Kuma suji tausayin tabbas sunga kokarinsu da har yanzun basu hadu ba tunda tadawo gidan da zama sati biyu kenan,Jamila tace."Umma zamuje kitso."toh shagon maman Amira zakuje."Aaa umma taje Kano suna,zamuje layout ne."toh Allah yakaiku lafiya ku kula dai, Hannatu banda rashin ki fa,Kinga dai gobe zaki soma zuwa makaranta dai."toh Umma,insha Allah."Allah yai maku albarka"Ameen da haka suka tafi har sun fita Umma ta Kuma kiran Jamila tace."ga key din motar ki kin manta."?shigowa cikin falorn tayi tace."Ba da ita zamu fita ba,tana bukatar ganin bakanike zamubi a daidai sahu ne."toh ba matsala Allah ya kiyaye hanya."Ameen."da haka suka fita ba inda suka amsa kira sai layout,wannan kenan.

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now