088

6 0 0
                                    

_*🏝️NAHIYATA AREWA🐄*_

*NA*

_JAMEEY_

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*PAGE 88*

"Ƴan matana kije kiga ko angama ma Hannatun."ba yabo babu fallasa yayi maganar yanajin tsananin sonta na fisgar shi,wasa ta farayi da wayar hannunta tace."tace zata kirani a waya idan tagama."jinjina kansa yayi yace."Ba matsala, my heart star kullin kara zamarmin kike kamar bakuwa kullin kara kaunar ki nikeyi Jamila."murmushi tayi tana cigaba da kallansa don san ta gane wani abu dangane dashi tasan sarai yasan da Sanda tayi waya saidai bataga alamin fushi akan fuskar shi ba duk da tasan shidin mutun ne mai zafi saidai yakan rasa dalilin dayasa Umar Diga yake iya danne damuwar sa akanta har gobe tana kan mamakin hakan kwantar da muryar ta tayi a hankali tace."sai nikeji kamar ban kyauta maka ba."mi kikayi man Jamila"? numfasawa tayi tace."Nasan kasan da wanda nayi waya kuma agaban ka."da'ga mata hannu yayi yana mai sakar mata murmushi yace."Umar Sanda ne,miye abun damuwa Jamila? Kinga Jamila nifa banda matsala dan kin kula wani saurayi kefa budurwace kuma allura cikin ruwa mai rabo ka dauka wlh Jamila koda ace Sanda ya aureki tabbas zanji da'ci araina banaji kusa zanyi aure bayan narasaki bana fatan hakan,Ina so ki saki jikinki kiyi facing rayuwarki ki fuskanci abinda ke cikin zuciyar ki sannan kiyi addu'a ki nemi zabin Allah"taji dadin kalaman sa sosai har cikin ranta sai taji ya Kara samun mazauni a cikin zuciyar ta"ALLAH ya shige mana gaba yasa mudace."Ameen Nurul qalb I love you."cikin jin dadi tace."love you too"wayarta ta kuma ringing ta dauka tana cewa"my love angama kitson ina zuwa."toh my Beb"fita tayi ta shige cikin saloon din tace."Feenarh har angama kenan,sannu Auta kai masha Allahu kitso yayi kyau"washe baki Hannatu tayi tace."gaskia ta iya kitso Anti."Kinga waje dai daya tsufa sai azo a sake wani yanda kike da gashin nan Masha Allah."mikewa Hanne tayi tace."aikuwa dai Anty."kudi Jamila ta ciro tana cewa."toh Feenarh gashi nagode sosai."girgiza Kai tayi tace ." anbiya kudin madam."murmushi Jamila tayi tana."Haba wasa kikeyi dai Feenarh."wlh anbiya kin gansu nan a cikin Acct sannan ga text din da akaimin nan."nuna nata tayi 20k din ta cikin account bakaramin mamaki tayi ba tace."lallai kam,amma dai ki barbi wannan din dai."wato matar nan Kudi kikeji naga alama."naji dai karba."amsa tayi tace."sai yaushe."saidai kinganni"da haka suka fito suka shiga mota,key Diga yaima motar suka dauki hanya inda Hannatu ke gaishe da Umar ya amsa yana."gobe sai school ko Auta."?washe baki tayi tana."Eh yaya duk na matsu naganni a cikin Aji."good girl ki dage kiyo mani first position zan maki babbar kyauta."insha Allahu."d'an maida kallansa yayi ga Jamila yace."ranki shidade lafiya."numfasawa tayi tace."mamaki nikeyi wai har anbiya mana kudin kitso Ina al'ajabin suwa zasu biya mana kudin kitso."batare da yace da ita komai ba ya shigar da hancin motarsa cikin katon mall din yanayin parking yace."na Allah basu karewa Kada ki zurfafa bin cike,kinsan ke ta musammance."daga haka ya fita a motar ya zagaya ya bude mata door yana cewa Bismillah."fitowa sukayi batare da tace komai ba suka shiga cikin mall din kowa yafara zabar abinda yake so."kanwata ki dauki abin da yai maki kinji."toh yaya."da haka suka dinga daukar kaya har suka gama aka sawa kowa a cikin leda ya biya sannan suka fito suka tafi har kofar gida ya kawo su yai parking yace."Hannatu dauki kayan ki, kigaishemin da Umma."toh yayana mungode kwarai."da haka ta fita, ya rage su biyu yace."toh gimbiyata sai yaushe."murmushi dauke a fuskarta tace."saika fada."numfasawa yayi kawai "gashi."suka hada baki wajen furtawa daga ita har shi kowa ya mikoma d'an uwansa ledar shopping din da sukayi,tare da kafe junan su da wani irin sihirtaccen kallo mai dauke da sirrikan dake narke zuciya a hankali ta janye idonta akansa tace."dama siya maka nayi."murmushi kawai ya sakar mata yasa hannu ya amsa yace."Jazakillahu bil jannah."dan rausayar da kanshi yayi yana kwaikwayon maganar ta yana cewa."Nima gashi dama siya maki nayi."dariya tayi tace."thank you my king."ajiyar zuciya ya shide yace."ALLAH yabarmu tare babyy na saidai inajin fargaba idan Baba ya gane akwai alaqar soyayya a tsakanin mu, duk da ya zama wajibi ya sani kimani izini in fa'da mashi gaskiar son da Nike maki kinga dai Baba baisan ina son ki ba dan Umar Sanda ya sanki,idan har kika hanani sanar mashi Ina sonki ba, da hakane kadai abokin hamayyar tawa zaimin zarra,Kada ina kallan ruwa kwado taimin kafa"zansan yanda za'ayi insha Allahu bazaka samu matsala wajen Baba ba."haka nike fata ki shiga ciki take care."I'll my love bye."fita tayi tana daukar ledan daya bata saida ta shige cikin gida sannan yaja motar shi ya nufi gida.

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now