047

7 0 0
                                    

_*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*_

*NA*

_JAMEEY_

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*PAGE 47*

Banda kallan mamaki ba abinda yakema Acp Umar Sanda,shiko ko ajikin sa ya daura kafa ɗaya kan ɗaya yana shan coffee cikeda nutsuwa Abbas yace."miyasa kafiye son kanka dayawa Umar.?"cikeda kamala ya gyara zaman shi ya aje cup din hannun shi saman center table yace."bazaka fahimce ni ba inaga."dan guntun murmushi Abbas yayi yace."haka kake gani Umar taya baka taba neman soyayyar yarinya ba,zaka tura iyayen ka kai tsaye taya zaka samu soyayyan ta bayan nuna isa da kake nuna mata." Numfasawa Sanda yayi yana cewa."ba haka bane Abbas kasan tsawon lokacin dana dauka da kaunar yarinyar nan?i was thinking always about her narasa solution da zan gabatar mata da soyayya ta shiyasa na tura iyayena."gyaɗa kai Abbas yayi yana cewa."hmm you got lucky kasamu nasara.?" Ɗaga kai Sanda yayi yana cewa."kwarai kuwa tunda Abba ya aminta dani komai mai sauki ne itama Jamilan zata aminta dani."okay Allah yasa amman ka gyara sam baka iya takon kaba."murmushi kawai ya iya yiwa Abbas ya kuma daukar coffen sa ya sha a hankali kafin yace."jiya mun rasu reporting tada tarzoma da wasu yara sukayi a hayin gabas dake Sumaila."Subhanalillah mijawo rikicin yanzun matasa basu da aiki sai tada zaune tsaye kuma kada kayi mamaki akan bangar siyasa ne."no wai ance kauraye ne dayake case din yana under Sumaila Devision wallahi abun ba kyau saidai addu'a."Allah ya kyauta."cewar Abbas."ameen."shiru kowa yayi kafin Abbas yace."yanzun an kama yaran kuwa.?"Aaa wai sun gudu."Allah ya shirya."ameen."Sanda ya kuma cewa daga haka suka faɗa firar su ta yau da gobe.

☆☆☆☆

Misalin karfe ɗaya na rana bayan saukowar masallaci Ubaidu ne rike da sharbeben takobin sa tsaye a tsakiyar unguwar Hayin Yamma matasan yankin suka hau guduwa dan tsira da ransu gudun kada ya dauki fansa akan su kamar yanda Jigiri yaima Jama'ar unguwar su ba wanda ya iya tunkarar Ubaidu bare ya bashi hakuri ko ya hana shi abinda yai niyar yi.Tafe suke suna sheka uwar dariyar su kana ganin su basu cikin damuwa inda Jigiri ke cigaba da sheka dariyar sa kamar wani sabon mahaukaci su bakwai ne duk da shi na takwas shigowar su kenan unguwar suka yi karo da Ubaidu dake jiran karasowar su baki dayan su sukaja birki suna kallan kallo da Ubaidu banda faduwar gaba da razana ba abinda ke yawo a kirazan su,gyara tsayuwar shi Ubaidu yayi yace."duk wanda yasan ya cika namiji ya karaso inda nike."daga jin haka sai Jigiri ya tunkare su yana fiddo kulli a jikin shi koda ya iso suka fara fada da Ubaidu abinka da wanda bai shiryaba kuma bai son ace ya gaza ko yaji tsoron abokin hamayyar sa hakan yasa Ubaidu ya dafa mashi wuka a ciki jini yafara zuba,ganin abinda yaima uban gidan su suka rufe Ubaidu da duka haka sukaita dauki ba dadi saidai yajima da yawan su raunika kasancewar da adda a hannun shi ganin rigimar taki sanyi suka fara guduwa saidai duk abin nan da Jigiri suka gudu magashiyan shima Ubaidu bin su yayi da takobin haka sukaita gudu abinka da hayin su suka samu wajen boyewa duk yanda yaso yacimma su bai samu damar haka ba karshe yajawo takobin sa zuwa gida ranshi na kuna yaso ya kashe Jigiri amman Allah bai nufa koda ya dawo gida ba kowa saboda aranar za'a sallami su Hannatu zama yayi gefen wani icce dake gidan su wai gawar da zaiyo sai yaga takarda iska ta hankaɗo ta kamar ba zai dauka ba sai kuma ya bude papern wani irin shock ya kama shi lokaci daya ganin abinda yake ciki.

(Yau na tabbatar da cewa baka rabawa Ubaidu,kana tunanin haka nan zamu kai maku farmaki a hayin ku?alhali bamu da masaniyar kana gari,to kasani duk.abinda zakayi makusancin ka na sanar mana,kuma shine ya sanar damu baka gari, hakan ya bamu damar kawo ma Jama'ar ka far maki,shin bakayi tunanin miyasa aminin ka baije asibiti ba,ko bakayi nazari ba)
Wani irin zufa ya ketoma Ubaidu lokaci ɗaya ko gaban shi baya gani ja wani irin jiri daya rufe shi,banda zufar kan shi dake digowa mashi saman fuskar shi,kamar wanda aka tsikara ya dauko wayar sa ya danna number Ɗahiru Kure bata shiga switch off"inalillahi wa'inna ilahirraji'un."abinda Ubaidu ke fada kenan yajima a wannan situation din har ya samu jirin ya rabu dashi da kyal yaja kafa yafita wajen gari wajen yaran sa,yayi sa'a suna zaune wasu nacin kifi wasu kuma suna shan sigari yanda sukaga Ubaidu ya gigita su cikin yaran sa wani yace."Allah yataimaki Uban daba miyafaru dakai yau maza ba lafiya."zama yayi saman wani dakali dabas yana shafa sumar kanshi yace.

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now