_*🏝️NAHIYATA AREWA🐄*_
*NA*_JAMEEY_
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
*PAGE 17*
Numfasawa Fulani tayi tana kallon Faruq da kyau tana cewa." Banki ta taka ba Faruq,amman kasani kai din jinin sarauta ne,ba ko wace mace za'a bari ka aura ba,dole ne kafin a yarda da matar da ka kawo zaka aura sai ta haɗa jini da saurata ko wata mai babban nasaba,ba haka kawai zaka ga mace kace kana so ba,dan haka kabar wannan maganar daga nan karka kuskura Takawa yaji ma." Marairaice fuska Faruq yayi yana cewa." Amman Fulani shi takawa din da kanshi yace idan har zan auri Ramlah zai yarda da zaɓi na kuma ni na yarda zan auri Ramlah a barni na auri zaɓina ni Jamila nike so Fulani ya kama a duba man,kuma banga aibunta ba." Jinjina kai tayi tana cewa." Naji Faruq ina ce wannan yarinya Jamila yar jaridar Hikima station dai kake magana akan ta ko.?" Murmusawa yayi yana ɗaga kai yana cewa."eh ita Fulani nidai dan Allah a duba man wallahi zanyi adalci a tsakaninsu ba zan taɓa nuna ga zaɓi ba a cikinsu dan Allah Fulani." Kallon Faruq kawai Fulani take tana jinjina girman so wai Faruq ne yake magana mai tsawo irin haka duk dan akan so, Allah kenan da ace cewa akayi ya zauna yayi doguwar magana irin haka da ba zai taɓa yarda ba cewa ma zai yi kanshi ma ya fara ciwo, gyaɗa mashi kai kawai tayi tana cewa." To naji zaka iya tafiya zanyi magana da Takawa komai kenan zakaji Allah ya tabbatar da alkhari ya kuma yi maku albarka baki ɗayanku." Tashi yayi yana ansawa da Amin, sannan ya fice yana tunanin ta inda zai fara,waye ya dauke mashi masoyiya? Wane mai tsotsayin ne?tabbas duk wanda tsotsayi da qaddara yasa ya ɗauke Jamila ya ɗaukar ma kanshi dan tabbas ba zai taɓa barin ko waye ba zai yi amfani da karfin da yake da shi a kasar na ɗan president dan nuna ma ko waye ya dauko wutar dafa kanshi,da wanann tunanin ya shiga bangarensu , zaune ya tadda Khalid yana kallo zama yayi yana maida kallansa y wajen Khalid daketa smile harya zauna gefen shi, numfasawa Faruq yayi yana cewa."Eh itace yarinyar da aka kiddinerp this week." Firzar da iskan bakinshi Khalid yayi yana cewa."Yanzun Faruq karasa wadda zakaso sai wannan yarinyar kanason kafaɗa cikin damuwa,ka auri yar uwarka cikin kwanciyar hankali amman kaki ko.?" Girgiza ma Khalid kai yayi yana cewa."Haba Khalid minene a ciki dan nafaɗa zabin raina?ina ce takawa ma yace zai aura man zaɓina and itama ai nace zan aureta ko?"
Numfasawa Khalid yayi yana cewa." Babu laifi sai dai ina tsoron karda ka samu Jamila kace kuma zaka wulakanta Ramlat bayan kuma yar'uwarka ce." Taɓe baki yayi yana cewa." Ba wulaƙancin da zan mata nidai abu ɗaya na sani i love Jamila so much,tashi muje muci abinci Friend don't disturb you self." Bai sake cewa komai ba shima Khalid ya tashi suka fita a lot space suka shiga motarsa sukabar gidan baki ɗaya sukai cikin birnin Katsina gudu yake faskawa saman titi ko ganin suna jin wata waka..Kai tsaye wani katafaren Resturant suka danna motarsu a ciki kallo ɗaya zaka yi ma eatry din zakasan wajen ba wajen zuwa kananun kwari bane waje ne na sai wane da wane zai iya zuwa a cikin birnin Katsinq,snap din code din da zasu ga duk abinda ake a wajen Khalid yayi da wayarshi ,kallon Faruq yayi yana cewa." Mai kake bukata.?" Numfasawa yayi yana cewa."Coffee."yana damke hannun shi yana cije lips din shi na kasa, gyada kai Khalid yayi yana cewa."Only.?" Ɗaga mashi kai kawai yayi dan shi bai jin cin komai gwanma ma coffee din zai iya shan shi damuwarshi yanzun ɗaya ce ina Jamila take?su waye suka ɗauketa? Tambayar da yake ma kanshi kenan,shi kuma Khalid Black tea and burger ya saka ma kanshi,shi kuma Faruq coffee yana tura order ko five minute ba'ayi ba aka kawo masu,cikin tsafta dan komai na wajen a tsaftace ake gudanar dashi ma'aikatan wajen a tsaye suke tsayin daka wajen yin komai,a hankali yake surɓar coffen yana lumshe idonshi dan daɗin shi da yaji yana ratsa shi na coffeen, ɗagowa Khalid yayi yana kallon Faruq yana cewa." Har yanzun fa ba wani labari Faruq akan kiddneping din Jamila fa,magana ɗaya ake har yanzun ba'a san su wa suka dauke ta ba kuma har yanzun shiru basu kira ba akan maganar kudin fansar ma." Ajiye mug din hannunshi yayi yana firzar da naunauyen ajiyar zuciya yana cewa." Shine matsala ina jin kamar na shiga daji da kaina dan fiddota Khalid.?" Wani kallon Khalid yayi mashi yana cewa."Sure?kana nufin da gaske zaka iya shiga daji dan ganin ka gano inda take duk da hatsarin da ake a cikin dajin.?" Ɗaga mashi kai Faruq yayi yana cewa." Kwarai kuwa,inajin zan iya komai akan ta Khalid." Dan shiru yayi yana firzar da iskan bakinshi yana mai cigaba da cewa." Na yarda kaima har yanzun baka san irin zafin son da nike mata ba ko?" Jinjina mashi kai kawai Khalid yayi yana cewa." Gaskiya ban yarda son ya kai haka ba sai yanzun,dan nasanka nasan kuma abinda zakayi da na karanta labarin da yake fitowa a zuciyarka yana baiyana akan fuskarka na son da kake ma wannan yarinyar ni har na dan fara tsorata ai ina kuma tausayin Ramlah Faruq.?" Taɓe baki kawai Faruq yayi ba tare da ya sake cewa komai ya dago yana kallon wayarshi da keta faman ringing ganin Ramlat a jikin wayar yasa shi kin ɗagawa,dan bai san mai zai ce mata ba shi dai yasan yana son Jamila bai kuma iya rayuwa ba tare da ita ba abinda ya sani kenan kawai,sake kiranshi tayi dan kallon Khalid yayi daga mashi kai Khalid yayi alamun ya dauka jinjina kai yayi yana ɗauka,yana cewa." Lafiya dai ko.?"Haba Ya Faruq miyasa kake son wulakantani ina sonka why zaka kini minene aibuna.?" Lumshe ido kawai yayi sai kuma ya buɗe a hankali jin yanda take maganar a sanyaye,sai yaji dan tausayinta ya kama shi numfasawa yayi yana cewa."Ramlat."Bakinta na hadewa jin ya ambaci sunanta wanda yake masa wahalar furtawa tsabar tsanar da yai mata, tace."Na'am." Jinjina kai yayi yana cewa."maiyasa kike da yawan complain? Why Ramlat?" Numfasawa tayi tana cewa."Ya Faruq ka tausaya mani bazan iya rayuwa babu kaiba."Wannan karan sake kurbar coffeen shi yayi yana matsa hannayen sa,da yakeji sun masa tsami sosai,yana ganin bishi bishi a idon sa."Ya isa kibarni in rayu da wadda ta dace dani." Zaro ido tayi tana cewa."Kana nufin bandace dakai ba komi Ya Faruq." Girgiza kai yayi yana cewa."No Ramlat but itace daidai da rayuwa ta,ita nikeso kibarni in huta Ramlat."Mikewa tayi daga kwance da take saman gado da gudu tayi ɗakin First Lady,tana zaune gaban mirrow ta hango Ramlat ta faɗa saman gado tana kuka,a kidime tayo kanta."Lafiya Ramlat mi akai maki.?" Cikin kuka Ramlat take cewa."Mumy ya tsane ni wallahi ya Faruq bai sona,kinji ya samu wadda yake so abinda yake faɗa mani kenan fa."numfasawa Mummy tayi cike da kosawa da case din Ramlah da Faruq tana cewa."Daina kuka Umma ta sanar mani komae Ramlat badai yar jarida yake so ba,shine yake wulakanta ki,kibar ni dashi saidai idan bani na haife shiba."ɗago lulu eyes dinta tayi wanda suka rine suka koma ja tsabar kuka tana kallon Mummy tana cewa."nabani Mumy."Bubbuga bayan ta tahauyi tana lallashinta tana cewa."You know ke yar gata ce,gaba da baya miyasa zakina zubda kwallan ki,duk abinda kikeso shi za'ayi zan nemo wacece ita dame take gadara."share hawayenta tayi tana cewa."Thank you Mumy."Murmushi Mummy tayi tana cewa."Good girl ko kefa lastly zaki auri Faruq kinji."Rungumeta Ramlat tayi cikin jin dadi."i love you Mumy."Love you too dear."Da haka sukaita fira cikin jin dadi.
☆☆☆☆
YOU ARE READING
NAHIYA TA AREWA
General FictionThe Story of Nahiyata Arewa is the one that comprise the most important things such as Correction,Injustice,Betrayl and Revenge including Entertainment and Education, is a Falatable and testable story.