_*🏝️NAHIYATA AREWA🐄*_
*NA*
_JAMEEY_
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
*PAGE 11*
Tunda zabe ya fara gabatowa ko wace jam'iya take shiryawa da tsarawa wajen ganin komai ya tafiyar masu a cikin tsari da tsanakewa yanda komai zai tafi kuma successful har su cimma gaci,duk da a wata mahangar da saura ma tunda yana da shekara daya mai zuwa,su kuwa yan siyasar a wajensu lokaci yazo shiyasa suka fara tsara komai dan kuwa wanda akayi winning a lokacin su tuni suke ganin lokaci yayi amsa kawai ya rage suyi duba da yanda tallakawa ke kuka akan wannan mulkin na wanda suke sama, duba da yanda ake fama da tsadar rayuwa da kuma rashin tsoron da ake fama dashi ga kashe kashen bayin Allah da basuji basu gani ba,duk kowa ya gaji da lamarin shiyasa kowa ya ƙagara ranar zabe ta gabato dan kada wanda suke sama su sake wasu dan kuwa al'ummar nahiya arewa har da kasar Nigeriya baki daya suna buƙatar chanji,suna son chanji fatan kowa kenan na adai yi chanji ba tare da sun nemi zaɓin Allah ba tare da bar mashi komai dan kuwa Allah shine mai kowa mai komai.
☆☆☆☆
_KATSINA STATE_
ACP Umar Sanda ne a cikin Jihar Katsina inda yazo har gidan Jaridar da Jamila ke aiki,yana zuwa ya tambayi office Manager,kai tsaye massenger wajen yakai shi,cike da karramawa ya tari Sanda fuskar shi dauke da murmushi,yake nuna ma ACP Sanda wajen zama yana cewa""Sannu da zuwa yau manyan baki mukayi.?"Shima murmushin ACP Sanda yayi bayan ya zauna yace."Aikuwa ya aiki ya fama da Jama'a.?" Numfasawa MD yayi yana cewa."Alhamdulillah,gaskia naji dadin wannan ziyarar ta bazata da ka kawo mana,ko akwai shirin da zaka shiga ne.?" Firzar da iskan baƙinshi mai dan zafi kadan ACP Sanda yayi yana girgiza kai yana cewa."Aaa inason zan gana da Journal Jamila ne."Dan shiru MD yayi yana dan kallon ACP sanda kaɗan yana cewa."Batazo wajen aiki ba,amman neman gaggawa kake mata ne?" Ɗaga kai ACP Sanda yayi cikin natsuwarshi da kamaiwarshi yake cewa."Eh to kusan hakan gaskia" gyaɗa kai MD yayi yana cewa."Okay bari sai inbaka address dinta,amman bari inkirawo wayarta inji." Ɗaga kai kawai ACP yayi ba tare da ya sake cewa komai ba sai ma dan lumshe idonshi da yayi kadan yana kare ma MD kallo da take kokarin gwada kiran wayar Jamila bata shiga kamar wanda akayi ma dole yake ce ma MD. "Ya dai.?" Dan ɗagowa MD yayi yana kallon shi yace."Kash numberta bata shiga."Murmushi yayi yace."Nima nayi try numbernta not reachable shiyasa nazo nan."
Ajiye wayar MD yayi yana cewa."Badamuwa ga address din nata nan nasan insha Allah zaka sameta a gida." Ansar address din ACP yayi yana cewa."Nagode." cikin jin dadi,musabaha sukayi sannan ya fita,daidai kofar fita wayar shi tahau ringing fiddota yayi cikin aljihu yana duba mai kiranshi,daidai Umar shima ya taho yana waya hannun shi rike da wasu files,sukayi taho mugama.
"Sorry."Suka haɗa baki wajen furtawa,ɗan bubbuga bayan Umar yayi lokacin da idanunsu ya sauka ana juna tare da sakarma junansu murmushi kamar sun san Juna a zahiri,ba tare da suncema junan su komai ba,kowa ya kama gaban shi inda Sanda yaje baki motar shi yana mai shiga...Tsuru yaima Adress din Jamila yanajin faduwar gaba mai tsanani wadda ya rasa dalilin jin hakan,musamman idan yana kallan ID dinta,cigaba da wayar shi yayi yace."Abbas kana ganin zan iya tunkarar ta,da wannan maganar.?" Numfasawa wanda aka kira da Abbas yayi yana mai cewa."Haba Sanda kaifa ba raggoba bane nagaya maka wallahi sonta kake inba hakaba akanmi daka tuna da ita kake samun faduwar gaba musamman idan kaga hotonta,kaga Malan ka fallasa mata sirrin zuciyarka,ka huta."Shiru yayi kamar bazaiyi magana ba yana ɗan dafe kanshi sai kuma yace."Never hakan bazai faruba,nidai kawai narasa mike damuna amman taya daga ganin yarinya rana ɗaya kawai sai inkamu da sonta,kadaina wannan zancen dan Allah." Murmushi mai sauti Abbas yana cewa."Naji yanzun dai kaje ka kaimata kayanta da kanka zakayi bayani."Ɗan guntun tsoki yayi sannan yaja motar tashi unguwarsu yaje yana duna addres, yaga wasu yara na wasan ball kiran ɗaya daga cikinsu yayi yana zuwa ya gaidashi,kamar yasan yaron yasaki jikinshi tare da faɗaɗa fara'ar shi yace."Abokina inada tambaya,dan Allah nanne gidan su Jamila.?" Shima yaron murmushin yayi yana cewa."Eh amman Jamilan biyu ce wace daga ciki.?" Dan sauki ajiyar zuciya Sanda yayi yace."Yar Jarida." Gyaɗa mashi kai yaron yayi yana cewa."Eh nanne." Dan murmushi Sanda ya sakar mashi yana cewa."Yawwa abokina dan Allah kaje kace ana sallama da ita."Har yaron ya tafi sai kuma yadawo yace."Injiwa zance mata.?" Dan shiru Sanda yayi sai kuma yace."Kace mata inji Umar."
YOU ARE READING
NAHIYA TA AREWA
General FictionThe Story of Nahiyata Arewa is the one that comprise the most important things such as Correction,Injustice,Betrayl and Revenge including Entertainment and Education, is a Falatable and testable story.