077

10 0 0
                                    

_*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*_

*NA*

_JAMEEY_

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*PAGE 77*

Ajiye ruwan lemun da yake hannunshi yana kallon Jigida da yake zaune kasa yana miƙa mashi wata farar takarda,bin takardar da kallo Diga yayi can ya numfasa ba tare da ya anshi takardar ba yana cewa." Taya akayi wanann sakon ya shigo gidan nan Salisu.?"Cike da natsuwarshi gami da kamalarshi ya jefo ma Jigida tambayar numfasawa Jigida yayi yana cewa."Maigida nima ban sani ba kawai dai Hashim ya kawo man yace ya tsinta a bakin gate." Murmushi Diga ya saki yana cewa."Shi Hashim din ne yace ya ganta kenan?mai ya kai shi bakin gate da har zai tsinta takarda.?"Ƙasa da kanshi Jigida yayi yana cewa."Nima tambayar da nayi mashi fari kenan Oga,duba da yau baki ɗaya bashi da lecture." Numfasawa yayi yana cewa."Okay Good for that ba zan ashi takarda ba,kai karanta takardar da kanka kawai Salisu."Ba tare da Jigida yace komai ba ya buɗe pepper ya fara karantawa kamar haka *~DIGA idan har ka cika ka din cikakken maciyi ma'ana ne to ka anshi tayin da Hadi yayi shine karshen kuskuren da zaka aikata a rayuwarka ka jira ranar da zamu hadu daga ranar ba zaka kwana a duniya ba dan bani yafe cin amana ga kowa  idan Zomo na yawo zabo na yawo watarana zasu hadu ka guji haduwarmu~* Idanunwan Diga a lumshe suke yana sakin wani murmushi yana sauraren abinda Jigida yake karantawa har Jigida ya gama bai dago ba balle har ya motsa, ɗago kanshi Jigida yayi yana cewa."Kaji wani shirmen da ke a cikin wanann abar,har waye wanann da zai rubuto maka wannan shirmen?shin din wa?ai Umar Fatah zaki ne kuma toron gida ya gagari kowa ba wanda Umar Fatah zai ji ma tsoron haɗuwa,ina ma zan yi ido hudu da shi da sai na nuna mashi Umar Fatah yafi karfin tsayawa karawa da shi sai da iyayen gidan shi nine nan Salisu dai-dai dashi." Sai a lokacin Diga ya buɗe idonshi yana gyara zamanshi yana kallon Jigida yana cewa."Ai ko kai Salisu kafi karfin ɓata lokacinka kanshi sai dai kananun kwari amman ba dai Kai ba."Jinjina kai Jigida yayi yana cewa."Haka ne mai gida wa kake tunanin zai aiko da wanann abar.?" Taɓe baki yayi yana dage kafaɗa yana cewa."Rabu dasu Salisu sannan su waye duk ɓata lokaci ne idan ya shirya yazo har nan ya tare ni sai ya gane ruwa ba sa'an kwando bane." Dan shiru yayi yana mai cewa."kwana biyu ban saka ta a ido ba kuma ina son ganinta."Gyaɗa kai Jigida yayi yana cewa."Angama maigida bari a haɗa tafiya gidan nasu."Numfasawa Diga yayi yana cewa."Da kai ɗaya nike son yin tafiyar amman kafin ka tafi kiraman ƙanena tunda ya tafi bamu waya ba anya kuwa yana lafiya." Ɗago waya Jigida yayi yana cewa."Nima bamu yi waya da Ubaidu ba ban zauna ba shiyasa ban kira ba shima bai kira ba." Da haka Jigida ya danna ma Ubaidu kira amman bai ɗauka ba ɗagowa yayi yana cewa."Inajin baya kusa da wayar Oga." Jinjina kai Diga yayi yana cewa."Haka ne a shirya tafiyar."Da Toh Jigida ya tashi yana fita shima Umar tashi yayi shige Bedroom dan yin wanka su tafi.

★★

Yau tunda Jamila ta tashi take doki da washe baki zataji Hikima station yau dan rabonta da Hikima station har ta manta dan kuwa har ta fidda rai da sake shiga wajen,zama tayi ta shirya cikin wata marron atamfa mai leaf ba ƙaramin kyau atamfar tayi ma Jamila ba sai asobe da ta daura ɗauri mai kyau irin na yanmata jikka da gyalenta light green ne ta dauka fitowa tayi tana zama gefen hannun kujera tana cewa." Ina kwana Baba.?" Ɗagowa Baba yayi yana kallonta yana cewa."Lafiya lau Mamana,har an fito kenan." Daga kai tayi tana cewa."Eh Baba Allah ya yarda." Jinjina kai Baba yayi yana cewa." Da kyau Allah ya taimaka ya kuma yi albarka sai ki kiyaye ki kuma bi sannu kinga dai halin da kika shiga saboda wannan aiki naki dan haka sai ayi a sannu sannan magana ta karshe ban lamunce ki kula wannan yaron Faruq ba jikan sarki ban yarda ba fatan kin ji mai nace maki.?" Ɗaga kai tayi tana cewa." To Baba in shaa Allah zaka samaini mai kiyaye wa akan komai." Yauwa Allah yayi albarka zaki iya tafiya."Tashi tayi tana leka room din Umma tana cewa."Umma na wuce." Murmushi Umma tayi tana cewa."Allah ya tsare a dawo lfy."Da Amin ta ansa cike da natsuwarta take taka kasa kamar ana mata dole ko kuma nace mai tausayin kasa haka take tafiyar ga key din mota a hannunta tana wulwulawa har ta iso gaban motarta da tasa M.Idi mai gadi ya wanke mata buɗewa tayi ta shiga tana worming dinta ta yi reserve dakatawa tayi tana cewa."Ina kwana Malan." Washe baki M.Idi yayi yana cewa."Lafiya lau Jamilatu fatan an tashi lafiya.?"5k ta miƙa mashi tana cewa."Alhmdulillahi mota ta wanku ina godiya matuƙa." Girgiza kai yayi yana cewa."Allah ya sawaƙa na anshi wanann kudin Jamilatu ai ni dan Allah nayi maki ba dan wani abu ba." Ɗaga mashi kai tayi tana cewa."Na sani Malan amman Dan Allah kadai ansa nima haka nan na baka ba dan kayi man wankin mota ba."Ansa yayi yana godiya gami da buɗe mata gate fita tayi tana ɗaukar hanya dan tafiya Motar Diga ce tayi parking a unguwar dakatawa tayi da tuƙa tata motar tana zuge glass din a tare suka sakar ma juna murmushi waving tayi mashi, lumshe ido yayi yana fitowa daga cikin tashi motar yana zuwa wajen ta buɗewa yayi ya shiga yana cewa."Yanmata wannan kyau haka?duk wajen aikin akayi ma wanann kwaliyar.?" Murmushi ta saki tana cewa."Dan saurayi nawa kayi kyau matuƙa kuma duk kyauna ai ban kaika ba ko.?" Numfasawa yayi yana cewa."Idan har na fiki ya za'a kalleni Myluv?nidai nayi kishi fa." Murmushi kawai tayi ba tare da sake cewa komai ba sai shi da numfasa yana cewa."Zuwa nayi gyada Baba da Umma da na raka ki wajen aikin ai."Sauke numfashi tayi tana cewa."Haka ne amman an hutar da kai ba wani dadewa zanyi ba program din TA FARU TA ƘARE kawai zamu gabatar kuma kaga ga wannan shiyasar da ta Kunno kai a cikin wannan shekarar za'ayi ta dole ne mun yan jarida zamu tashi tsaye tsayin daka wajen wayar ma yan'uwanmu tallakawa kai su zabi cancanta." Murmushi ya sakar mata cike da zallar sonta yake cewa."Ikon Allah Journal Jamila daman dan jarida yana campaign?ko kuwa daman shi dan Jarida yana da jam'iyar da yake so yake tura ma mutune sonta a zuciyarsu saboda bukatunsu.?"Girgiza kai tayi tana cewa."Ko ɗaya Yayana kawai shi dan jarida kokarinshi ya saita ma mutane hanya ta hannunka mai sanda da su zaɓe wanda ya cancanta ya dace dasu zai iya mulkarsu a tsakani ga Allah shi ne kawai,amman shi dan jarida bai tallata jam'iyar shi sam." Murmushi ya saki yana cewa."Haka ne Allah ya taimaka ki kula da kyau kuma kibi sannu band driving din ganganci koda yake zan tura ɗaya daga cikin yarana yana tuƙaman ke dan kanki wajen aiki ma kawai." Turo baki tayi cikin shagwaba take cewa."Wayyo Allah Yayana nidai gaskiya bani son wani drive zan kiyaye kamar yanda ka buƙata ba zan yi ganganci ba." Jinjina kai yayi yana cewa." Sure zaki kula sosai.?" Ɗaga mashi kai tayi tana cewa."Yeah am really."Alright byee." Da haka ya fita a cikin motar ɗaga mashi hannu tayi tana gaba sai murmushi take saki,shima shiga tashi motar yayi Jigida ya ƙarasa dashi gidan nasu.

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now