_*🏝️NAHIYATA AREWA🐄*_
*NA*
_JAMEEY_
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
*PAGE 93*
Murmushi Muhi ya saki yana kallon raguna guda hudu manya manya da ya bada a sawo mashi a kasuwar charanci ta jahar Katsina,raguna ne ba kananu ba dan ba kananun kudi Muhi ya kashe ba dan har da kayan Baby masu uban yawa da kuma laces da atamfa kusan kala goma ya saya masu kyau da tsada banda kayan kwalliya haka ya haɗa iyayen kaya niƙi-niƙi dan kawai ya aikama Jummala tayi fitar suna,kallon Hamisu Muhi yayi yana cewa."Gaskiya Hamisu wa'annan ragunan sunyi sosai akwai mai da tsoka a jikinsu,yauwa bari zanyi dan short text da zaku tafiyar masu da ita dan su san MUHSIN yana nan raye da ranshi bai mutu ba,kuma nan gaba kadan zanzo na dauke matata da yarona dan tafiya dasu,dan kuwa ina son kayana dan su zauna shirin zuwan ranar da zai zo na dauke Khadija dan kuwa Khadija tawa ce ni ɗaya."jinjina kai Hamisu yayi yana cewa."Haka ne uban gidana ba wanda ya isa yace zai mallaki Khadija sama da kai duk wanda tsotsiya yasa zai yi kokarin shiga gonar da ba tashi ba sai dai uwarsa ta haifi wani Allah wallahi." Murmushi Muhi yayi yana cewa."Kwarai kuwa dan Khadija kaddarata ce nima haka ni kaddararta ne dan haka bari kawai a rubutu MUHI a jikin takardar kawai kuje ku kai kayan nan dan nima ubane dole nayi ma iyalaina hidimar da suke bukata." Jinjina kai kawai Hamisu yayi yana miƙa ma Muhi pepper take ya rubuta sako daga Muhi ya linke takarda ya ba Hamisu suka kashe iyayen kayan nan suka saka a cikin mota raguna kuma a cikin hilux aka saka suka dauki hanyar gidan Hajja dan kai ma Jummala kayan kamar yanda Muhi ya bukata.
Kallon Jummala Rumaisa tayi tana cewa."Gaskiya Khadijah kinyi kyau sosai wannan kumshin ba ƙaramin kyau ya ƙara maki ba har da kitson ma."murmushi Jummala ta saki tana cewa."Allah ko Rumaisa.?" Ɗaga kai Rumaisa tayi tana cewa."kwarai kuwa,shi dai little bai da rigimar ranar sai dare yayi ya nemi hana mutane bacci."kallon little Jummala tayi da yake bacci tana cewa."bari Rumaisa ai jiya hana Hajja bacci yayi fa dan ni da naji ban iyawa bar mata shi nayi na cigaba da bacci na ina dalili yaro ya ishe mutune da kuka bai duba dare." Dariya sukayi jin Hajja tana cewa."To ke wa yasan irin kukan da kikayi lokacin da aka haife ki wata ila ma hana baccin kike baki ɗaya." Shigowa Muda mai gadi yayi da sallama bakinshi yana cewa."Ranki ya daɗe anyi baƙi,amman ban barsu sun shigo ba duk da ba famar da basuyi ba na dai hana saboda ba'a gaya man zasu zo babu sunansu a cikin wanda zasu zo nace su kira waya su sanar dake zuwan nasu sunce basu da number ki kuma abun mamaki har da raguna har hudu suka zo a cikin mota."kallon Muda Hajja tayi tana cewa."Baki kuma har da raguna to su waye wa'annan ba dai Umar bane ya aiko su tunda jiya Umar ya sawo abun yankar da za'a yanka gobe suna to ko su waye.?" Ta ida maganar tana kallon Jummala,girgiza kai Jummala tayi tana cewa."Nima gaskiya ban san ko su waye ba Hajjah."numfasawa Hajjah tayi tana cewa."Kaga Muda buɗe masu su shigo wata kila ma Yusuf ya aiko da ragunan a nuna masu baya can a kai su inda aka ajiye na Umar ai basu yawa idan aka yanka aka soya sai a raba ma mutune har gidan marayu ma sai a kai ai an samu lada." Juyawa Muda yayi yana cewa."To shikenan Hajja."fita yayi yana cema su Hamisu."zaku iya shigowa."buɗe masu kofa yayi suka shigo da mota har biyu sakko raguna sukayi masu aiki suka kaisu baya kamar yanda Hajjah ta bada umarni,sakko iyayen kayan sukayi baki daya cokali basu manta ba sai envelope din da aka saka papper ciki Hamisu ya dauka ya ba Muda yana cewa."Yauwa abokina ka tabbatar kaba Aunty Khadija wannan takarda hannunka ya nata sannan kuma kace ana gaisheta sosai kayan nata ne da na Baby Umar." Ansa Muda yayi yana cewa."To shikenan ba damuwa zan bata,ba zaku shiga ba.?"girgiza kai Hamisu yayi yana cewa."A'a muna sauri ne watarana zan shigo idan na dawo."da haka Hamisu suka shiga mota suka bar gidan bayan sun tabbatar da an gama shiga da kaya cikin parlon Hajja har Hamisu ya kulle kofa ya koma dan kaima Jummala envelope din da aka bashi ya bata.
Tsaye sukayi a cikin parlon suna kallon iyayen kayan da aka tulle masu gabansu sai kace masu shirin buɗe dan karamin shigo tsaki Hajjah tayi tana cewa."ina mamakin lamarin Yusuf wallahi,ji iyayen kayan da ya aiko dan Allah duk ayi mai dasu bayan wanda Umar ya dinki sunfi hamsin fa to haka za'a ƙare wajen sayen kaya da haka su baki kudin mana ko gold ne ai sai a saya maki ko.?"numfasawa Jummala tayi tana cewa."Wallahi Hajja amman ina zamu kai wa'annan kayan ai sunyi yawa sosai."shigowa Muda yayi yana cewa."Hajia Khadijah ga wannan envelope din wa'anda suka kawo kayan nan sunce na tabbatar na baki ita hannu da hannu."kallon envelope tayi tana cewa."kuma ni suka gaya maka Muda.?" Ƙasa yayi da kanshi yana cewa."kwarai kuwa har da cewa ma na ce suna gaishe ki sosai." Cike da mamaki Jummala ta kalli Rumaisa tana cewa."ikon Allah Rumaisa su waye to wa'annan?kenan bama Daddy bane ya aiko da kayan.?"itama Rumaisa cike da mamaki take cewa."Nima kaina ya daure Khadija, amman ki amshi envelope din sai ki duba kiga mai ke ciki ko.?"numfasawa tayi tana cewa."Toh."Ansar envelope din tayi tana cewa."zaka iya tafiya Muda." Juyawa Muda yayi dan komawa bakin aikinshi, kallon Rumaisa tayi tana cewa."Ni gabana faduwa yake Rumaisa tsoron ma buɗe wannan envelope nike dan ban mai ke cikinta ba ko a bari idan Yaya Umar yazo sai ya buɗe da kanshi dan ni wallahi ba zan iya buɗewa ba."jinjina kai Hajjah tayi tana cewa."Kinga Khadija samu waje ajiye wanann envelope mu cigaba da hidimar gabanmu idan Umar din ya shigo ya buɗe yaga uwar da ke ciki,bari su Atika su maida shirgin kayan nan gefe duk sai Umar yazo duk ya gani mu ba ruwanmu dai."ajiye envelope yayi tayi akan Tv stand sannan suka ajiye kaya gefe suka cigaba da tsara yanda taron suna zai kasance dan kuwa Hajja da rigima tace sai tayi taron suna dan ba yanda za'ayi ayi haihuwa ace ba za'ayi taron suna ba wand bai fasa cewa an haifi dan gaba da fatiha a gidansu ba,idan an tashi siyasar ta rushe ita ba damuwarta bane daman ita ba son wannan mulki take ba da Yusuf take dan har ta kosa ya gama kowa ya huta Kubrah ta dawo natsuwarta kamar yanda take a da.
YOU ARE READING
NAHIYA TA AREWA
General FictionThe Story of Nahiyata Arewa is the one that comprise the most important things such as Correction,Injustice,Betrayl and Revenge including Entertainment and Education, is a Falatable and testable story.