_*🏝️NAHIYATA AREWA🐄*_
*NA*
_JAMEEY_
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
*PAGE 46*
"What did you say my Exellency."with shock take tambayar sa ɗaga mata kai yayi yana cewa."yeah bazan iyaba nagaji kwara muba wadanda muke sa ran zasu kawo cigaba ga al'ummar mu nidai daman na taɓa gaya maki na gaji da wanann mulkin ban san haka abin yake ba da tun farko ban hau ba." Murmushi ta sakar mashi tana gyara zamanta tana kallon mijin nata da kyau take cewa."haba haba darling taya zaka fara wannan maganar bayan muna shirin yin tazarce kuma kaima zaka iya."murmushin girma yayi yace."No idan ma zan iya akwai wa'anda suka fini nagarta da yawa cikin Jami'iyar nan."bata fuska tayi tace."Kaine Jami'iyar PAP ku kayi mata hidima akan mai zakace bazaka koma mulki ba.?" Kama hannunta His Excellency yayi yana cewa."calm down my first lady kada ki manta fa mulki na Allah ne sannan ki duba kiga yanda abubuwa keta faruwa kasar nan ta zama abinda ta zama bama wannan ke damuna ba yanda al'ummar Jahata suke fama da insecurities ya zanyi nagaza basu kulawa haba Kubrah sau nawa kika zauna kikayi thinking about it and then mutun nawa ke baici ba ya lafiyan su take kinje asibiti kin tabbatar da komai is enough wannan ma adalci ne?actually i decided bazan koma takara ba zan tsaida Candidate."fesar da numfashi tayi mai zafin gaske tace."idan hakane why not bazaka tsaida ɗan kaba ai shima zai iya kodan son da talakawa ke maka zasu zabe shi."Kallan mamaki yake mata yace."i think kujerar nan bata gado ba ce ko Kubrah?first of all idan Umar kike magana baida interest about democracy kema kinsani kaf ya'yana shine wanda bai siyasa aikin neman na kansa yakeyi beside da kan shi yasha bani shawaran idan bazan iya sauke hakkin talakawa naba nayi resign taya kike zatan Babana zai amshi wannan tayin? kinga wife kibari a zabi wa'anda suka cancan ta kawai."wani irin faduwar gaba ke saukar ma Momy ji take har bata gani a wani side na ranta tanajin zafin Umar miyasa zai dinga yima mahaifin sa irin wadannan maganganun kenan shike zuga shi a zahiri kuwa danne damuwar ta tayi tace."Ok i understand kace indaina wahalar da kaina kenan.?"dauke idon sa yayi daga kan tv yace."wajen me kenan.?"ahh Alhaji kenan Rali da nike zuwa Local Governments mana wai dan naga mun koma,jiyama nadawo Dimba har kaya naraba da tarin kudi kuma naje asibitoci nakai tallafi ga talakawa."murmushi ya kumayi yace."inama dan karin kanki kikai wannan taimakon badan Siyasa ba,illar ɗan Siyasa kenan komai nashi da zaiyi sai yasa Riya,nagani a tv yan Jaridu suna yadawa the governors wife of Katsina has..."haba gwamna na mikake cewa haka.?"ta katse shi ta hanyar riko mashi hannu sannan tace."muna kokari muyi dan Allah,kuma abin ne yazo agabar Siyasa data matso that's why."rungumo ta yayi yace."alright i proud of you,amman ya yarana hope suna lafiya.?" Jinjina mashi kai tayi tana cewa."eh Sagir yaje Faris,Umar kuma yaje gun aiki yau Rumaisa ke gama Exam ita kuma Hunaisa next week insha Allah."good mother itace wadda ke kulawa da duk damuwar ya'yan ta God bless you dear."Ameen my Exellency,muje ka shirya sai kayi lunch."in my side ko.?"no my company."jan hancin ta yayi yace."i have a meeting by 4 insha Allah."Okay before komai zai daidaita."Okay."da haka sukayi bedroom dinsa.
☆☆☆☆
Yaran Jigiri cike a hayin su Ubaidu suka fara sara suka ga mutane basu san hawaba basu san sauka ba,kafin kace me kowa yahau gudu dan tsira da lafiyan sa gashi kaf illahirin yaran Ubaidu sun fita dashi Ralin Shiyasa a cikin Kano hakan yabawa su Jigiri damar cin karan su ba babbaka sunjima dai dai kun Jama'a ciwuka wa'anda suka ritsa a hanya sannan sukaima gidan su Ubaidu tsinke suka afaka cikin gidan suka hau zage zage suna cewa."ku fito yau sai mun fafe cikin ku."abinda suke cewa kenan.Hannatu dake lafe karkashin gado sai raba idanuwa take banda kadawa da hantar ta keyi a lokaci ɗaya inda Baba Ladidi ke ta sakin zawo a ban daki suka ritsata takasa ko motsin kwarai saidai Isihu bai nan."Tunda basu fitowa ku shiga duk wanda kuka kama ku fefe shi."Oder Jigiri ya bada suka afka daki suna bin cike ba kowa sannan suka afka dakin Hannatu tana ta zufa bakin ta rufe ta rufe idanun ta leke sukeyi bayan kyaure har gadon sun daga amman basu ganta ba fitowa sukayi har zasu fita sai sukaji motsi a bandaki Baba Ladidi ce ta zame ta fadi garin ta haura katanfa dan guduwa janyota Daniel yayi kasa duk da warin da takeyi har gaban Jigiri yakawo ta."Ke daman kina gidan nan iyeh.?"kyakkyarwa jikin ta keyi ta gaza furta uffan."baki magana."ya daura mata adda a kafa jini yafara ɗiha kwalla ihu tayi tana kururuwa."ku yanka mani ita."har sun kayar da Baba Ladidi sukaji Jiniyar Yan Sanda da gudu suka dire ta katanga koda suka shigo basu ba alamar su aka dauki Baba Ladidi zuwa hospital da waɗanda suka jima ciwuka itako Hannatu saidai tafarka ta ganta gadon asibiti ana kara mata drip tsabar tashin hankali.Karfe ɗayan dare Ubaidu ya iso cikin Sumaila shida yaransa kai tsaye kowa gida ya nufa kana ganin su sun gama jigata domin kowa ya gaji a cikin su."Nawan saida safe ka gaishemin da kanwata."Cewar Ɗahiru Kure."to Nawan ina gaishe da Umma da jiki."Ubaidu yace daidai zai shiga gida suka sakarma junan su murmushi sannan kowa ya shiga gida tunda Ubaidu yai sallama yaji shiru ya nufi dakin Hannatu."Kanwata kinyi bacci ko?"ya leka saidai bai ganta ba shiga yayi bata fitowa yayi ya zauna yace."ko kina ban daki."zaman jiran ta yafara dan yasan koda zai kwana yana sallama Baba Ladidi bazata amsa shiba shiyasa baibi takan ta ba,kuma baiji zai iya bacci batareda yaga Hannar shi ba sannan yabata tsaraba yafi five minute shiru hakan yasa yaje yai knocking shiru banka ban dakin yayi bata da sauri yayi dakin Ladidi nan ma ba kowa waje yayi da gudu ya ga wani mai teburin shayi zai tashi yace."Ilu lafiya mike faruwa.?" Kallonshi Ilu yayi yana cewa."Dazun aka samu hatsaniya anguwar nan saidai..."fadamin hatsaniyar me?"yaran Hayin yamma suka shigo suka farma mu abun saidai addu'a."dafe kanshi Ubaidu yayi dakejin yana neman tarwatsewa lokaci ɗaya komai ya jagule mashi."suna ina?"Asibiti."da gudu ya yanki hanya baiji bai gani ya nufi asibitin duk da akwai tazara amman hakan bai hana Ubaidu sheka gudu ba ikon Allah ne kadai ya iso dashi hospital din kai tsaye emergency ya nufa,duk da dare ne amman still wajen akwai mutane,kai tsaye dakin yafada ya iske yan unguwar su kwance duk an masu dressing akalla sunkai su ashirin can ya hango Abban shi tsaye wajen Ladidi da sauri ya isa wajen su,kallo ɗaya yaima Ladidi ya kauda kai ya kalli mahaifin shi yace."ina kanwata."kallan mamaki Isuhu kema Ubaidu ganin kota mahaifiyar shi baiyi bare yai mata sannu da jiki duk da ta silarsa komai ya afku."kagaya min Abba kodai sun kashemin ita.?sauke ajiyar zuciya Isuhu yayi yace."female ward."da sauri ya fita zuciyar shi na harbawa da sauri sauri kamar zata fado kasa tsabar razana da tsoro duk lokaci ɗaya,a hankali ya bude kofar ya saka kanshi ciki malamar asibiti dake zaune tana faman gyangyadi tace."waye anan.?"tasowa tayi sukaci karo da Ubaidu baya ta koma tace."kai ne.?"bai bata amsa ba yace."tana ina.?" da yatsa ta nuna mashi gadon da take kwance akai da sauri ya isa gaban ta ya duka bisa guiwar sa yana kare mata kallo from head to toe yace."kanwata."a hankali ta bude idanun ta tana kallan shi kwalla na zirara ta gefen idon ta."ina ke maki ciwo mi sukayi maki.?"girgiza mashi kai tayi bakin ta yai bala'in nauyi sosai."Yimin magana."a hankali ta yunkura ta tashi zaune tana aikin kallan shi tashi yayi ya zauna gefen ta ya rike hannun ta yana goge mata hawayen idanun ta,fadawa tayi saman kirjin sa ta fasa kuka mai tsuma rai,bubbuga bayan ta yahau yi sifar bata hakuri."kidaina kuka Hannatu gani nazo kinji."still kukan takeyi sosai tace."nace kadaina wannan harkar amman kaki bari kaga halin da yan unguwa suka afka duk ta silar ka haba yaya Deeni''wasu kwalla masu dumi yaji at the same time jin sunan Deeni data kira shi dashi hakan ya tuna mashi da Umman sa,zuciyar shi keta faman zafi fiye da Da a hankali ya dago ta daga jikin shi ya zuba mata idanun sa yace."Kidaina kuka Hannatu sannan kidaina blaming dina bai dace suyima mutane ba,ni ya dace su tunkara amman tayi kai."a dan tsorace ta kalle shi tace."mizakayi.?"murmushi yayi wanda yafi kuka ciwo yace."zan baki mamaki kanwata."jikin ta yai matukar sanyi yace."mamakin me.?"bakin ce kina son nabar wannan harkar ba.?"eh."tace bakin ta har rawa yakeyi."Ok nakusa daina saboda ke."maida kanta tayi saman kirjin shi tana sauke ajiyar zuciya."miyasa kika kwanta asbiti sun maki wani abu ne."Aa na firgita ne shiyasa."hmmm kizama Jaruma kefa kanwar Ubaidu ce."Murmushi kawai tayi amman ranta bai kwanta da maganganun sa ba,tsoron ta ɗaga kada yace saiya dauki fansa..."kwanta ki huta kinji.?"toh."tace tana kwantawa ya gyara mata marufin kafin ya fita waje ya nufi ward din da aka aje yan unguwan tasu yafara bin gado by gado yana dubasu saidai dayawa tir suke mashi suna tsinarsa suna cewa shine ya jefa su a cikin halin ha'ula'i shidai saidai yai murmushi karshe ya koma gun Ladidi ganin kallan da Abban nasa ke masa saidai baice mata ko sannu ba ga kafarta nade da bandeji tun daga cinya har zuwa tafin kafar ta,wayar sa ya dauko ya kira Ɗahiru amman switch off yai mamaki karshe ya maida wayan aljihu yanajin dacin abinda su Jigiri suka aikata masa ga Jama'ar unguwar su da haka ya kuma komawa wajen Hannatu.
_PRESIDENCY HOUSE_
Faruq ne zaune gaban first lady tana aikin yima ɗan nata faɗa kamar zata duke shi tace."wacece ita dahar zaka dauki kafa batareda sanin matar kaba katafi wajen ta.?"shiru Faruq yayi ya sadda kanshi kasa dakejin yana sara mashi lokaci ɗaya."am talking to you."Sorry Mumy."daga haka bai kuma cewa komai ba taci gaba da cewa."saboda ka isa dakaje wajen ta,maimakon kadawo wajen iyalin ka shine ka kwana hotel saboda ka raina mutane."Mumy weather ba kyau ba yanda za'ayi fligt dinmu ya tashi shiyasa na kwana."Okay shi Khalid daya dawo ranar yafika ne."shiru yayi yana mamakin yanda Khalid ta taho ya bar shi,yarasa gane hali irin na Khalid da saurin daukar fushi dagowa yayi ya kalleta yace."i think ta train ya dawo Mumy dagske ba flight din daya tashi yesterday."wani irin kallo take jifan shi dashi kamar zata duke shi tace."Alright yanzun saika koma gidan ka,bazaka zo ka tisani gaba kajini da kyau nan Ramlat zata zauna wajena ni bangaji da ya'ta ba."yaji dadin hakan a ran shi amman a zahiri sai ya nuna damuwar shi yace."banyi hakan dai hurting din kuba kiyi hakuri hakan bazai kuma faruwa ba."maida kanta tayi kan tv dake aiki tace."nagama magana."Mumy ki....sauran maganar sa ta tsaya sakamakon shigowar Dad dinshi da sukaji cikin falorn daga shi har ita mikewa sukayi suna mashi well coming saida ya zauna sannan suka koma suka zauna maida kallan shi yayi kan Faruq yace."Son yau kai ne gidan namu da sassafe aikin fa.?"sadda kan shi yayi yace."daga nan zan wuce insha Allah."Okay da kyau."Morning Dad."ya kuma gaida shi cikeda ladabi."Morning too,how is ur family."dan satar kallan Mumy yayi daketa faman watsa mashi harara yace."she's fine."well am Faruq next monday ka shirya ina son aiken ka Katsina wajen Hon. Umar."insha Allah Dady."haba ranka shidade baccin wannan aiken da zakai mashi dan karin kanshi bazaije Katsina ba."murmushi yayi yace."ku kam mata baku gajiya da abin mamaki mizai hana Faruq zuwa Katsina tinda Fulani da Takawa nacan beside ga the great Uncle I."ya ida maganar da sifar barkwanci."hmmm."taja dogon numfashi tace."bata su yake ba,you know tunda akayi auren su da Ramlat baije sun gaida Mai martaba ba."da mamakin yake kallan ɗan nashi shidai kanshi sadde kasa ya gaza furta komai Mr President yace."baka kyauta ba Faruq almost a month ace bakaje ka gaida Mai Martaba ba totally wrong dan haka gobe goben nan ka shirya da iyalin ka kije Katsina ku gaida Takawa in yaso ko sati daya kuyi a can."Dady daman bari nayi sai wani time din sai muje."Enough nagama magana kuje gobe wannan is stupidity kasan ba haka akeyi ba amman ace kai anfara akan ka,kada in kuma jin kayi haka kanaji na."to Dad."sallamar ta suka tsinya baki dayan su suka maida duban su kan kofa banda kirjin Faruq daya bada sauti hakama Mumy dan batai tunanin Ramlat zata iya shigowa ba a tunanin ra sai goma zata tashi as usual kamar yanda ta saba,kowa cikin su ya gaza magana sai Dady daya amsa mata yana kokarin canza channel na Zee Word zuwa News.A sannu takaraso wajen shiko Faruq yaki daina kallan ta da yanda yake warning din ta to his face itako taki yarda su hada ido zana tayi gefen sa a kasa tace."Dady barka da safiya."fuskar shi dauke da annuri yace."Yawwa Daughter ashe tare kuke kodai nan kuka kwana."ya ida maganar yana kallan Mumy cikeda tsarewa,dan sosa kanta tayi tace."Eh."da mamaki yake kallan ta yace."why.?"still kallan tuhuma yake mata."am daman ni nace tadawo gida sa..."for what reason to do that.?"saboda yaje unguwa bai sanar mata ba,kuma fa kwana yayi a can."kallan Faruq yayi da har yanzun yaki yarda ya dago fuskar sa Daddy yace."he's her husband yana da right yayi tafiya but yana da kyau idan zakaje waje ka dinga sanar mata inda zakaje bcs of ur wufe is ur friend dole tasan komai naka understand.?"jinjina kan shi yayi yace."Yes Daddy."and then yanzun ka dauki matar ka kutafi gida sannan ban lamunci zuwa kuma kwana gidan ba,ku zauna gidan ku saidai idan akwai kwakkwaran dalili kunji abinda nace maku."Eh Dady"suka amsa baki dayan su yaci gaba da cewa."Lastly idan kunje Katsina ku tabbatar duk abinda ya dace kunyi musamman kai Faruq."insha Allah."Good zaku iya tafiya."yan kame kame Mumy tafara tace."why not su bari sai gari yai sanyi in yadawo Company."is not necessary ya mai data gida before ya dawo ta yi abinda ya dace a gidan ta."Okay."tace a sanyaye tana ci gaba da watsa masa kallo ta kasa kasa,kamar mai jira ya tashi yai gaba ita Ramlat din mikewa tayi sukai masu sallama sannan suka tafi bata dauki komi ba sai gyalen data yafa suka shiga mota yaja suka nufi gida ba wanda ya kuma magana kowa da abinda yake sakawa a cikin zuciyar sa.share pls
YOU ARE READING
NAHIYA TA AREWA
General FictionThe Story of Nahiyata Arewa is the one that comprise the most important things such as Correction,Injustice,Betrayl and Revenge including Entertainment and Education, is a Falatable and testable story.