016

10 1 0
                                    

_*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*_

*NA*

_JAMEEY_

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*PAGE 16*

Dan cize kasan laiɓanshi yayi kadan yana mai firzar da iskan bakinshi yana cewa."Waya kuma.?" Ɗaga kai Jigida yayi yana mai cewa."Eh Oga abinda take bukata kenan."shiru kawai yayi bai sake cewa komai ba, kuma bai motsa daga yanda yake ba idanunshi suna a lumshe kamar mai yin bacci,Jigida bai damu da shanyashi da Diga yayi ba dan idan da sabo ya saba da miskilancin Diga dan kuwa magana wahalar yi take ma Diga kafin ya buɗe baki yayi magana da wuya ko mai zai yi da yatsa koda kai yake masu magana shiyasa duk wani yaro da yake a ƙarƙashin Diga yasan da wannan miskilanci na Ogan nasu kuma sun iya yaren nashi na yatsa ko kuma kallon fuskashi kawai zasuyi su gane mai yake nufi,suna kafa-kafa da duk wani abu da zasuyi dan ɓata mashi rai dan kuwa shine uwarsu kuma shine ubansu shine gatansu gaba da baya yana kyautata masu duk da harkar daba suke, amman a hakan yake tsaye tsayin daka a kansu dan ganin rayuwarsu ta inganta dan dukansu ba wanda baya karatu daga mai degree sai mai wanda ya kusa gama degree dinshi,rayuwa suke cike da zallar kaunar juna duk a cikin yaran Diga din ba'a rasa munafukai wanda already daman daga wani dabar aka turosu dan su ringa ɗaukar sirrin Diga suna gayama iyayen gidan nasu...sai dai a banza har da wofi ma dan shi Diga inuwarshi ba yarda yake da ita ba balle kuma wani daga Jigida har Dila ba komai nashi suka sani ba hatta ɗakin baccinshi bai yarda da kowa ya shigar mashi ba,gwamna ma Jigida wata sa'in yana shiga shima a shekara baifi ya shiga sau biyu ba yana shiga da yawa ma,Jigida yafi minti ashirin a tsaye a gaban Diga kanshi a kasa yana jiran mai zai ce mashi cike da izza ba tare da ya buɗe idonshi ba yake cewa."Jigida." Murmushi Jigida ya saki yana cewa."Allah yabiya Oga."

Firzar da numfashi yayi yana jin bai son ma komai yana takaici da kuma mamakin yanda wai shi Umaru Diga kamar shi wai yake tsare da mace a gida,to wai maiyasa ma tun farko ya yarda ya dauko yarinyar mutune?yarinyar da bata ci bata sha mashi ba,kuma shi a tsarin shi babu kidinafin bai ma da lokacin da zai ɓata har yayi wani kiddneping da zai yi kidinafin da tuni yayi dan Muhi ba yanda baiyi ba dan ya shiga harkar yaƙi sai gashi wai yana ajiye wata mace a gidanshi a rasa wama za'a saka ya dauka sai mace,tsaki yayi yana cewa."Je kataho mani da ita."juyawa Jigida yayi ba tare da yace komai ba dan yasan halin Diga sam baya son bata lokaci ko tsayawa dogon zance,tafiya yayi zuwa ɗakun ta,isketa yayi kwance saman gado da sauri ta mike tsaye jin ya banko kofa,da sauri ta dire kasa tana rabraba idanu,ko kallonta Jigida baiyi ba yace."Ke taso kika koma jikin bango kamar mage." Cike da takaicinta ya ida maganar dan shi kanshi ya gaji da ganinta a gidansu dan su ba ruwansu da sabgar mata duk tabi ta takura masu ya rasa ajiyar mai Oga yake ma yarinyar,ita kuwa Jamila cike da tsoro take cewa."Dan Allah kada kai mani komai." Dogon tsaki Jigida yayi kallonta yayi cike da masifa yake cewa."Ke taso ko in wullaki inda ba'a dawowa." Yanda yayi maganar yasa,jikinta yafara rawa ko ina a jikinta karmar tsoro yake jin yace zai aikata inda ba'a dawowa ina kenan?lahira yana nufin kasheta zai yi?share hawayenta tayi da bayan hannunta,tana tasowa tana ɗararewa gaba yayi tabi bayan shi zuwa wajen Diga..A hankali take hawan stairs din har cikin makimancin falorn shi,zaune yake yanda Jigida yabar shi haka suka same shi,kasa ta duka bisa guiwowinta,inda Jigida ya duka gefen hannun damar Diga,cike da ladabi yake cewa."Ranka shidade gata." Ba tare da ya buɗe idonshi ba suna a lumshe yanda suke ya turo mata kulolin abinci ba tare da yace komai ba,ganin yanda take kallon flask din yasa Jigida cewa."ci abinci."Da sauri ta kalle shi idaninta waje,tana marairaice fuska tana cewa."Na koshi."mamaki ya kama Jigida shi kuwa Diga kauda kanshi yayi gefe ɗaya daga kallanta da yayi,kamar ba shi bane ya buɗe ido ya kalleta ba, numfasawa Jigida yayi yana cewa."kici abinci Oga baisan musu."Kallan Jigida yayi,take Jigida yabar falorn yana mai daukar da kanshi yabar masu farlon baki ɗaya. Sai da Jigida yayi minti goma da fita sanann ya gyara zamanshi yana cewa."Jamila."sai da gabanta ya faɗi jin yanda ya ambaci sunan sa a kaisashe."Na'am."wannan karan idanunta sun kaɗa kamar rushi kuka kawai ya rage mata domin muryarta kadai ta nuna hakan."Sheet."ya daura yatsan shi saman lips dinshi,yana dan gyara zamanshi kaɗan."Matso kici abinci."a matukar sanyaye yai maganar,flat ya turo mata a gabanta,a hankali ta zuba abinci kadan tana juyashi da spoon din hannun ta,share hawayen da suka zubo mata da bayan hannu tayi tana maida ajiyar zuciya tana cewa."Dan Allah kamaidani wajen iyayena suna cikin matsananciyar damuwa." Jinjina kai yayi yana cewa."Kinason ki koma gida Jamila.?" Ɗaga kai tayi tana cewa."Eh inaso Allah." Kamar wanda akai ma dole yace."To kici abinci kinji.?"Toh."tace kamar ammata dole tafara cin abincin pride rice dataji naman kaji,wasa wasa taci abincin sosai,aikin sa yake a system dake gaban shi,gefe ɗaya kuma littafi ne yana rubutu,wayarshi tahau ruri,ta gefen ido ya kalli screen din."Mai gida."shine abinda ya bayyana...Sauke ajiyar zuciya yayi yana dan jan ƙaramin tsaki ɗagawa yayi kasancewar kunnensa nada head phone yake cewa."Inajinka."daga bangaren akace."Diga ya najika shiru kayi abinda muka umurceka.?" Hankalinshi kwance cike da miskilancinshi yace."Aaa.""firgici zallar mamaki da kuma dunbun takaicin Diga yace."Why Umar.?" Taɓe baki Diga yayi yana cewa."I can't." mikewa yai tsaye yana bugun iska yace."Mikakeso ka dauke mu Umar?haka mukayi dakai yana cikin sharuɗɗan mu fa." Cikin karkausar murya irin ta zaratan maza masu jin da jarumta yake cewa."Nasani kawai bazan iya bane." Daga ɓangaren maigidan yake cewa."Umar kasan Jami'an tsaro sun bazama neman yarinyar nan ko?kasan hatsarin dake cikin wannan tafiyar mun umurce ka,kayima yarinyar nan fyaɗe shine makamar nasarar mu a cikin wannan tafiyar."Tari sosai Jamila tafarayi jin abinda yake cewa,ruwa ya miko mata a  glass cup,ba tare da ya kalleta ba yace."Jamila ungo ruwa."Amsa tayi tasha tana matsar kwallar da suka taho mata."Ashe kana tare da ita,Umar rashin bin umurnin mu shine silar tawayarka,kasani suna kake nema kuma kasamu,lokaci guɗa zamu rufe babin rayuwar ka matukar bazaka bi umurnin muba." Cike da takaicin Ogan nashi Umar ya buga tsaki yana buga table din gabanshi yake cewa."Shut-up kada kagaya mani maganar banza bazanyi mata fyaɗe ba,kuyi duk abinda zakuyi nidaku wazai gaza."

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now