_*🏝️NAHIYATA AREWA🐄*_
*NA*
_JAMEEY_
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
*PAGE 55*
"Ku shigo dashi."cewar Umar Diga ya tashi daga kishingidar da yayi saman royal chair ya gyara zaman shi cikin mintin da baifi biyar ba suka shigo tareda shi baki dayan su suka kai gaisuwa daga sama har kasa yake karema bakon nashi kallo yace."Have a sit."yace yana nuna mashi kujerar dake facing din shi."thank you ranka shidade,naji dadi haduwa dakai bansan da wane baki zan iya misalta maka farin cikin da nike ciki ba ayau."murmushin gefen baki yayi yace."me too,welcome to my Comlort Ubaiduddeen Yusuf."Murmushi Ubaidu ya sakar ma Diga yana cewa."godiya nike taurarona najima ina samun labarin ka da irin taimakon da kakema talakawa da yanda kake karfafama matasa guiwa ni Ubaidu na bayabama hazakar ka nazo neman albarkar ka uban gidana."jinjina kai yayi yace."lallai kam ka canci ka zama ɗa Ubaidu,tabbas ganin ka ne kadai da ban tabayi ba amma na yaba da hazakar ka ina abokin naka.?"Allah yataimakeka dagaske ne sama tayima yaro nisa saidai ya tada kai yai kallo,Kure nawa yana cikin aminci saidai shekarce ba daya ba."iskar bakin shi ya fesar yace."komi yasa hakan? A wane dalili."abinda nakasa fahimta kenan Mai gida."hmm Ubaidu kenan,zaka iya fadan haka saidai kasani hikimar ka ta burgeni mutun mai sirri shine wanda yafi kowa hikima zan zauna dakai next time."dubban gadiya shugabana ko ahaka na tsaya na samu cikar burina najima inaso in gode maka Allah bai nufa ba sai yau."wajen mi kenan.?"Kaine kayi silar fitowar mu daga cell bayan mungama wahala a inda ba'asan munayi ba amma ka daukaka darajar mu ka yan tamu kamar kowa amadadin mutane na muna godiya sosai samun mutun mai kishin matasa kamar ka tabbas da ancigaba."uhmm dont mentioned nan din gidane."ina kanwar ka.?"ɗan damama Ubaidu yayi yace."lafiya lau..amma." dakatar da shi Diga yayi yana cewa."kasan ina da kanwa a ina kasanta?ko ba haka zakace ba.?"Jinjina kai Ubaidu yayi yana cewa."Eh hakane ranka shidade."indai Uban daba ne waye baisan sansa da yar lelen kanwar sa ba,wannan ba abun mamaki bane."murmushi Ubaidu yayi yace."marainiyar Allah kenan tanacan tana kewar yayan ta."jinjina kai Umar yayi yana nazartar Ubaidun duk da yaune suka fara haduwa ido da ido harya fahimci nagartar Ubaidun da kuma jarumtarsa gamida tarin son dayake ma kanwarsa."Allah yataimaki uban gidana zanzo nayi maka tambaya daya idan ba damuwa."why not?you re free go ahead."dan Allah ma gida ina kasan second name dina naji kace Uban daba.?"Murmushi Umar yayi har saida hakoransa suka bayyana yace."Uban daba,Ubaidu,Deeni ba abun mamaki bane dan nasan su idan har sanin kanada kanwa Hannatu da kakarta Ladidi baimin wahalaba Ubaidu dan hayin gabas."a kidime yake kallan Umar cikeda mamaki."bissamallah ga entertaiment kaci,kada ka damu kanka Ubaidu so da kauna yasa nayi maka izinin ganawa dani and then ina son mutun mai kaifi basira ina son kasani idan har bansan waye kai ba tabbas ko inuwata saita yima ganin ka nisa kasan miye dalilin hakan.?"girgiza kanshi kawai Ubaidu yayi yace."Aa mai gida."saboda ban yarda da kowa ba hatta ni nan."zuwa yanzun Ubaidu ya daina al'ajabi saiya koma tsoro na shigar shi."kaci abinci mana."maganar shi ta katsewa Ubaidu tunanin daya lula faracin abincin yayi yana nazartar yanayin Umar din da irin luggar maganarsa.
☆☆☆☆"Allah ya huci zuciyar ki Momy."wani irin kallo ta watsa mashi ta maida kanta gefe bakaramin jin haushin halayen d'an nata takeyi ba tarasa wace kalar alaka ke tsakanin shi da Khadija yar kauyen yarinya shine sunan data bata."Ya Umar."maida duban shi yayi ga Rumaisa duk ta gama shiga damuwa aranta tace."kayi hakuri nasan bacin raine yasa Momy tayi maka haka."gyada kanshi yayi alamun gamsuwa.
Horn da ake dannawa ya maida hankulan su akan gate din yayin da convey din motocin da suka dauko Sagir suka iso har gaban part din Momy.Baki dayan su suka isa bakin farar mini cooper car din Sagir din ya fito sai sakin smile yakeyi."Oyoyo my son you are welcome."thank you Mumcy na, I really miss you."hugging dinta yayi ya sakar mata peck a kumatu."welcome home brother."thank you my cute twins."idan ka gama murnar mu shiga ciki ka huta ko.?"Ahhh Mumsy kinga cireman kunne.?" Murmushi Umar ya sakar mashi yace." Wato kai mai Mommy ko,toh sannu dan lele."am the one."dariya sukayi sannan suka dunguma zuwa cikin falorn Momy Suna shiga kowa ya samu waje ya zauna."am tired walahi."dole ka gaji brother ya fil land."? "Uhhh so fine akwai dadi am missed my friends."Gaskia kam haka sabo yake duk karame."ohh Mumcy na pressure yai yawa but any thing become normal, ina daddy."yana meeting."kwabe fuska yayi cikeda sangarta yace."amma ai yasan yau zan dawo ko jiya yabani call shine ba zai tsaya yai welcoming dina ba."Haba Sagir kadaina korafi kaima kasan Excellency baya samun zama election na matsowa so ya dace kayi masa uxuri."hakane I think angama election ma."No an kusa next month kaga tunda ka dawo sai kafara shirin rakani campaign."mummy ga Ya Faruq.?" harara ta ballama Sagir tace."manta kawai kaidai ka zama ready."OK nagane kaidai har yanzun baka son harkan siyasa"Hmm facially."big bro ya dace ka gyara."Noted.son tashi kaje ka huta kazo kayi lunch."tom Mumcy, yau akwai labari Ya Faruq hope yau dai rana tace bazakaje wajen aikin nan naka da bai karewa ba ko.?" "Yeah, koma ina da aiki I will spend all my time for you, kada kadamu kaje ka huta."thank you my big broth I proud of you"murmushi kawai ya sakar mashi, ya wuce room din shi."Momy zan wuce."Dama ni natsada ka.?" A hankali ya mike ya iso gabanta ya duka ya riko hannayen ta yace."sorry Mum nasan nayi hutting dinki kiyafe man ba haka naso ba,ki cire komai aranki ba abinda ke tsakanina da yarinyar nan."well Ashe kagane matsalar ina kakai ta, harda yo mata siyayya niki niki."iskar bakin sa ya fesar yace."Ki kwantar da hankalin ki Momy, hospital nakaita fa bata lafiya shine na siya mata some fruit na bata ba wani abu na siya mata Haba Momy kitayani rikon amanar da Allah ya daura mani mana kefa uwace."Iskar bakinta ta fesar tace."yes I know am a mother but bana son ina ganin ka tareda waccan poor girl din yarinyar, kuma maganar amana ina kai ina daukar amana wanda kai kana har yanzun kana bisa kulawar iyayen ka, look Umar ya dace zuwa yanzun kayi iyali that's all."sake rike hannunta yayi yace."toh Momy ina bukatar time ne zanyi."wane time Umar?ai yanzun ne lokacin daya dace kayi auren nan saboda shekarun ka naja idan baka da yarinyar da kake so ni zan zaba maka."girgiza kanshi yayi a hankali yace."No Momy I have my choice."OK who is she? Who is her father and then ita din minene nasabar ta."? a hankali ya mike daga tsugunnin da yayi ya zauna gefen ta yana facing dinta da kyau yace."Momyna kenan! ita din ba yar gidan kowa have anahi mahaifinta ba wani mashahuri bane."ya isa Umar kanayi mani maganar da Kaina bazai iya dauka ba ka fito fili ka fada mani ita koma wacece dame take takama dashi da har ta sace zuciyar da'na ."wannan Karin a zafafe tayi maganar."sihirtacciyar ajiyar zuciya ya sauke ya Kara kwantar da muryar sa kasa yace."kamun kanta da rikon addinin ta da sanin darajar nagaba da ita su sukajani ga kaunar ta ba wata bace face abokiyar aikina Jamila."What?"a zabure Momy ta mike tsaye cikeda kidima, shima mikewan yayi yana kallanta cikeda tarin al'ajabi."kayi kadan Umar kayi gaggawar rabuwa da waccen munafukar yarinyar wallahi badai a gidan nan ba bata ba zama surukata har abada idan har ni din uwar kace wai daman ba kacire shigiyar yarinyar nan a ranka ba Umar.?"a hankali ya koma ya zauna saman kushin yana dafe kansa da yai masa nauyi matuka."Haba Momy dan Allah kibar Ya Umar ya zabi son ransa he is matured pls."Rumaisa na kuma jin bakin ki I will deal with you know, anya Rumaisa are you in your sense? Umar din zan bari ya auri yar talaka? Poor girl din ma wannan shegiyar yarinyar 'yar Jarida 'yar sharri wadda ke hama gwamnatin mu sakewa idan akwai wadda na tsana araina bata wuce the journal girl din can.!"cikin tarin tausayawa Rumaisa ke kallan yayan nata yanda ta shiga tarin damuwa tunda ya dafe kansa bai kuma furta uffan ba saidai sauraron su da yakeyi."yes Momy you are right kada ki yarda wallahi I support you hundred percent, kada ki yarda yar talaka ta aure maki 'da"murmushin jin dadi Momy tayi tana jinjina kai alamun gamsuwa tace."I proud of you autata, wannan maganar taki ta nuna man kedin kinsan ciwon kanki."mikewa yayi tsaye ya watsama Hunaisa wani irin razanan nan kallo har saida takoma bayan Momy duk tasha jinin jikinta."lafiya kake mata wannan mugun kallan Kodai dukanta zakayi ne Faruq.?"murmushin takaici yayi yana mai girgiza kanshi yace."sorry Momy, I don't mean that."juyawa yayi zaibar falorn tace."ina zaka."am leaving zan wuce wajen aiki."ohhh don kaji dadin haduwa da 'yar jarida ko? be care ful Umar, dole ne ka aje wannan aikin dama ba wata rana yake maka ba kwakwace irin taka kawai mika rasa gata ko me.?" Haba Momy kibar wannan maganar pls ina bukatar hutu."iyeh yayi! you can go."shigowar Sagir ta katse masu maganar da sukeyi yanda ya gansu yasan ba lafiya musamman yanda gaga Umar din ba yanda ya bar shi ba yanayin sa ya sauya."Ahh Mumcy discussion din me mukeyi naganku a tsaitsaye what happen?" Barin wajen Momy tayi ta nufi dining ta zauna batareda tace komai"Yayana miyafaru.?" girgiza kanshi yayi yace."nothing ina zuwa."fita yayi yabar falorn baki da'ya."OMG! Rumaisa mi akaima yayana.?" Riko hannun shi tayi tace."bakomai baijin dadi ne, muje lunch na jiran ka."badan yayarda ba ya bita zuwa dining table suka zauna ya kalli Momy yace."are you happy? all your mood is change, wai mike faruwa? na fahimta baki son kigani a walwala ko Mumcy.?"Hmm, No kada kadamu son kaci abinci, kuma Daddyn ka zaizo yayi lunch da kai nasan zakayi farin ciki."murmusawa yayi yace. "Sosaima kuwa, but miyafaru da Ya Umar nagan shi a damuwa kuma zanso nayi lunch da da'n uwana fa."look Sagir ba wani abu bane mai amfani kuma zai dawo."Alright."yauwa son."zuba mashi abincin tayi tana cikin saving ya'yan nata suka tsinkayi isowar Excellency ya iso dining arean."OK, we should meet after asar prayer, thank you."kashe kiran yayi ya maida dubansa ga iyalan nasa fuskar shi dauke da murmushi yace. "welcome home my son."thank you Sir."I proud of you, hope bakai fushi da daddy ba naso inyi welcoming din ka,abubuwa sukaiman yawa sorry for your Dad, uhmm."? Hugging din mahaifin shi yayi yace."bakomai am happy to see you in wealth and happiness."jinjina kai exellency yayi yace."me too son have a seat."thank you Sir."komawa sukayi suka zauna bayan ya gaisa da yaran nasa saving din shi Momy tayi sannan itama ta zauna tana gefen mijin ta kowa ya fara cin abincin sa hankali kwance."Hajia Kubrah where is my son.?"Dan sosa kanta tayi tace."wai zai watsa ruwa ne."Ahh why not bazaku jira shi ba, haba Kubrah you know that Umar is back bond of this family, bana son wasa fa."sorry Alhaji nasan yanzun zai dawo."dauko wayar shi yayi ya dannawa Umar kira yana kwance saman gado yarasa abinda ke masa dadi yaji phone din shi ya dauki ringing kamar bazai dauka ba sai kuma ya dauki wayar a zabure ya tashi zaune ganin mai kiran shi da sauri yai picking cikeda girmamawa yayi sallama."where are you.?" Yanda yaji muryan mahaifin sa saida ya kuma tattaro duk wata natsuwar sa da kalamarsa yace."am in my room."Ok ina bukatar ganin ka yanzun nan a part din Momynka."toh daddy."da kallo yabi wayar hakanan yaji jikin shi yayi sanyi tashi yayi ya sura jallabiya coffee ya fita zuwa side din Ummi.Share pls
YOU ARE READING
NAHIYA TA AREWA
General FictionThe Story of Nahiyata Arewa is the one that comprise the most important things such as Correction,Injustice,Betrayl and Revenge including Entertainment and Education, is a Falatable and testable story.