040

3 1 0
                                    

_*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*_

*NA*

_JAMEEY_

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*PAGE 40*

Tura hannayenshi yayi a cikin sumar kanshi yana sakin wani killer smile da ya ƙara fiddo da ainahin kyaunshi yana cewa."Yayi interview da ita kenan.?"Tsare su da manyan idanuwan sa yayi masu narai narai kamar au duga ɗaga kai Jigida yayi yana cewa."Yes Boss."mikewa yayi daga saman kujarar da yake lilawa a hankali yace."Good yanzun wasan zai fara."baki dayan su,suka mike daga zaunen da sukayi suna kallan shi cike da takaici gami da jin haushin Jamila Jigida yake cewa."wannan cin amana ne Oga,nifa ban yarda da yarinyar nan ba kwata kwata."buɗe lunsansun idanunshi yayi yana saukesu a saman fuskar Jigida minti ukku yayi yana kallonshi yana hango yanda tsanar Jamila take kwance a saman fuskar Jigida murmusawa Diga yayi yana cewa."Hmm Salisu kenan abin yarda ce ita kadaina zargin ta,ba wani abu bane dan ta zauna da Sanda." Numfashi Jigida ya furzar yana cewa."makiyin kafa ne maigida."murmushi Umar yayi har saida fararen hakoran sa suka bayyana can kuma yace."wannan kuma tunanin ka ne,aikin shi yakeyi." Cike da son fahimtar da Diga abinda Jigida yake hange yake cewa."Ranka shidade yarasa inda zaiyi aikin shi sai kan mu."dafa kafadar shi Umar yayi yace."Da sannu idanunshi zaibar kanmu idan ya tabbatar da abinda yake bukata."Hakane Oga." Cewar Jigida yana haɗa ma Diga black tea yana jin tsanar Sanda a zuciyarshi dan bai ga dalilin da zai sa Sanda ya saka ma rayuwar Ogansu ido ba bayan shi Diga baya shiga sabgar kowa ta kanshi yake yaga sunyi nasara a rayuwarsu cikin yardar Allah.

☆☆☆☆

"Khadija ki saki jikin ki,nan gidan ku ne kinji."a sanyaye ta ɗago kanta ta kalli Umar,ya sakar mata kayataccen murmushi."insha Allah."tace tana saukar da kanta kasa,gaba yayi tabi bayansa zuwa sashen mahaifiyar sa sallamarsa ta karade illahirin falorn dake fidda wani kawataccen kamshi mai ratsa zuciya,Hunaisa dake zaune tana kallan TV ta amsa sallamar tana sakarma yayan nata murmushi."Auta ana hutawa an dawo kasar kenan.?"ya ida maganar yana zama saman kushin."zauna Khadija."ya furta yana maida kallan sa kan Hunaisa."Momy fa.?" Murmushi Hunaisa ta saki tana cewa."Welcome Yaya ai jiya muka dawo daman ba wani abu bane check up muka je ba." Girgiza kai kawai Umar Y yayi yana auna check up a cikin zuciyarshi da ƙannan nashi suka je har kasar Poland duk manyan doctors din da suke da shi a Nigeria yayi masu kaɗan da su duba su har sai sunje wata ƙasa bai ce komai ba sai ma kallonta da yayi yana cewa."Momy fa.?"Tana daki."tace tana aikawa Jummala wani kallo a kaikaice."dakin Momy ta nufa dan kiranta,tana shiga ta isketa zaune saman gado tana aiki a system."Momy Yaya najiran ki a falor."kallo ɗaya tai mata ta kauda kai."Umar matsala bazai iya shigowa nan ba."tabe baki tayi tace."taya zai iya zuwa nan,bayan yana tare da wata bush girl,Momy ina Yaya ya samo wannan yarinyar I hate her."Sauke ajiyar zuciya tayi tana mamakin halin Hunaisa yanda take kyamar mutane musamman talaka,har tsoro lamarinta ke bata.
"Hussaina kenan lamarin ki sai ke,miye naki a ciki sanin inda ya samota bazai maki amfani ba." Turo baki Hunaisa tayi tana cewa."No Momy kice ya koreta batai mani ba." Ɗaga mata hannu Hajia Kubrah tayi tana cewa."Hunaisa ya isa."Tayi maganar ba alamun wasa a saman fuskar ta,saukowa tayi kan gadon zuwa falor a sannu take sakowa saman steps din kamar bata son taka kasa,banda sautin takalmanta dake bata kara bakajin karar komai harta iso idanunta nakan Jummala dake duke kasa ta sadda kanta kasa tana wasa da yatsun hannun ta zama tayi saman kujerar dake kallan Umar tana maida kallan ta,wajen shi."Momy Good morning."Morning How was ur work."Alhamdilillah."jinjina kai tayi tana daura kafar kan daya tafara kadawa.

"Barka da safiya Momy."Jummala tace a sanyaye cikin muryar dake fita a darae."Yawwa."tace tana kare mata kallo daga sama har kasa,ɗan gyaran murya yayi yace."Momy ga Khadija."Kakaro murmushi tayi tace."naga Khadija,hope kinajin dadin zama damu ko Khadija.?" Gyaɗa kai Jummala tayi tana cewa."Eh Momy."tace tana kirkiro murmushi saman fuskar ta."Good kisaki jikin ki,kidaina dararewa."Toh."Ta kuma cewa idanunta nakawo ruwa da sauri ta goge fuskar ta,ba abinda take tsoro yanda zatayi rayuwar gida kamar wannan da ciki a jikinta taya hakan zata faru.? Shine babbar damuwarta maganar Hajia Kubrah ce ta dawo da ita daga tunanin da ta lula da taji tace."Khadija lafiyan ki kalau.?" Jinjina kai tayi tana cewa."lafiya lau."Alright yanzun zata zauna akalkashin Rumaisa kafin wani lokaci"Farin ciki ya lullube Umar jin maganar Momy baiyi zatan haka ba,ya dauka a yar aiki zata cigaba da zama kamar yanda ta gaya mashi kafin ya kawo ta amman sai gaya sabanin hakan."Thank you so much Momyna."sakar masa murmushi tayi,itama taji dadin ganin dan ta cikim farin ciki..Wayar ta,ta dauko ta dannawa Rumaisa kira,bugu ɗaya ta dauka."ki sauko falor ina jiranki."toh."tace tana barin Labrary da take faman karatun Exam.da zasu fara next week,shiyasa taware kanta dan samun isasshen lokacin da zatayi karatu yanda yakamata,sabanin Hunaisa dako kallan books din batayi bare ta shiga Library dan karatu,badan taso ba ta fito daga labry din zuwa kiran Momy,tana shigowa ta iske ylYayan ta,hakan yasa ta kara fadada annurin fuskar ta,saboda bakaramin shakuwa ke tsakanin Umar da Rumaisa ba,yana son halayen ta fiye da Hunaisa kasancewar bata son hayaniya,kuma tana ganin girma dan adam kaf kannen sa tafisu kyawun dabi'u,wannan dalilin yasa suke good time."Aki yau ba aiki ne.?"tace tana zama gefen Momy."Eh ina free."murmushin ta sake sakar mashi sannan ta kalli Momy.

Aje wayarta tayi gefe tace."ga bakuwa zata zauna kalkashin ki,kafin wani lokaci."sai lokacin Rumaisa ta kalle Jummala dake duke har yanzun taki sakin jikinta." Ta dan jima tana kallon Jummala can ta kalli Her Excellency Hajia Kubrah Yusuf tana cewa."To nagode."A sace Jummala ke kallan Rumaisa tana mamakin saukin kanta batayi zatan haka ba,ashe masu arzikima suna karrama mutane."Amman ban shaida taba." Dan yatsine fuska Momy tayi tana cewa."bakuwar Yayan ku ce."Wow kice bakuwar mu dai Momy"dariya sukayi baki dayan su tace."Ki bata masaukin ta."Momy tace tana mikewa,suma tashin  sukayi Rumaisa ta tafi da ita,shiko Umar bakaramin dadi yakeji ba yanda mahaifiyar sa ta karbi Jummala.

☆☆☆☆

Tun daga kwangwayen dake gidan ba abinda ke yawo sai bindigu kowa ya rike suna zagaye da gidan har zuwa mai gate din da zaka shiga idan ba ansan da kaiba bazaka iya shiga ba,har zuwa last gate da zai sadaka da harabar gidan yayin da manyan yaransa keta zagaye suna kai kawo a harabar gidan tsaye yake daga saman bene yana hangen yanda yaransa keta kai kawo da hannu yakira yaransa ya iso gaban uban gidan nasa ya zube."Mike faruwa haka.?"Umar yai tambayar yana maida kallan ga Jigau."Oga muna bawa komai da dangance ka tsaro."murmushi yayi yana girgiza kai."kowa yaje yayi huddar gaban sa."ya fadi alamun bada umurni.A dan tsora ce ya kalli Diga da ko ajikin sa ba alamun tsoro yace."mai gida kwanan sa biyu a garin fa." Taɓe baki Diga yayi yana cewa "Kaje kayi abinda na umurce ka."Angama Oga."tafiya yayi dan aiwatar da sakon Umar,shiko komawa yayinsaman kujerar da aka killace dan hutawa a wajen yana hangen kaf illarin area ga iska dake kadawa a hankali yanayin damina  daukar wayar sa yayi yai dailing number rafara ringing hakan yasa ya maida kansa jikin kan kujera ya jnjina yana rufe idanun sa harta tsinke ba'a daga ba hakan yasa ya ware idanun sa yana kallan side din hannun sa nadama ya dauki ruwa yasha kafin ya kuma kira a karo na biyu ya daura a kunnen sa."Jamila ga wayarki ana kiran ki."cewar Umma tana miko mata wayar.hannun ta,ta goge da karamin handkerchief sannan ta karba tanabin wayar da kallo ganin bakuwar number."Aa ki daga mana,kike kafe waya da kallo."dauka tayi ta kara a kunnen ta,ta maida kallan ta kan Umma tareda sakar mata murmushi a hankali ya shide sanyayyar ajiyar zuciya yana fesar da iskar bakin shi a sirrance."Assalamu alaikum."tace tana kara duba number jin shirun da akayi."Kyakkyawa ykk."Wani irin sautin kirjin Jamila yabada tsinkayar muryar Umar a cikin kunnuwan ta,lokaci guda bakin ta yai bala'in nauyi ta gaza furta komai."Yadai Jamila."tattauro natsuwar ta tayi tace."barka da safiya."gyara zaman sa yayi daga kishingidar da yayi."are you happy why are you silence Jamila."Bakomai."Okay."Shiru kowa yayi a cikin su,kowa da abinda yake sakawa a ransa."Jamila."ta sake tsinkayar muryar shi."Na'am."ta amsa a sanyaye."baki lafiya ko.?"Aa am felling better."Jikina yabani hakan tell me the truth."lafiya lau."Okay."Sake shiru sukayi duk jitake ta takura yanda takejin ta kamar tana gaban shi."Ya Abba da Umma.?" Wannan karan mamaki ya kara kamata."miye damurka da lafiyan iyayena,idan takai ne da ban iske su da rai ba."lafiyan iyayen ki abin tambaya ne a gareni tunda suma iyaye ne a wajena."maganar sa ta yanke mata sakar zucin da takeyi dan batai zatan yajita ba,bakin ta ya kuma nauyi tarasa mizatace mashi."Gobe zanzo dubaki."waro idanun ta tayi waje alamun tsoro."miye abin tsoro?zanzo duba ki sannan zan gaida Abba." Girgiza kai tayi tana cewa."Aa Umar karkazo gidan mu dan Allah."saboda baki son Umar yasani kome?kisaki jikin ki dan yai inter view ba wani abu bane nikaina zanso hakan."wannan karan mamakin shi ya kara kasheta."Ba wannan ba nidai idan kazo gidan mu,mi zancema Mahaifina.?"killer smile ta saki yana jijjiga kafar sa yace."kice nine wanda zaki aura nazo neman izinin aurenki."Umar kadaina fadan haka,zaice ina nasan ka bayan yasan ba wannan alakar a tsakanin mu kuma duka yaushe nadawo ina nahadu dakai.?" Ɗage kafaɗa yayi yana cewa."Wannan amsar tawace Jamila,ki daina saka kanki a damuwa saidai idan baki sona."hawaye masu dumi taji sun ziraro mata a saman fuska."Jamila."ya kuma kiran sunan ta."Na'am."Ajiyar.zuciya ya fesar yaci gaba da cewa."kibadani dama mana."tabbas tasan Umar yanada tausayi saidai aganinta akanta yake nuna tausayawarsa,bai cancanci ta guje shi ba,ahalin yana bukatar kulawa tunda harya bukaci ta shiga rayuwar sa amman taya zata bari yazo gidan su mi zatace.!?"Kiyi magana Jamila."Shikenan nabaka dama Umar amman hakan bashi ke nuna na karbi soyayyar ka,zan jaraba ka takowace siga idan kaci zan gabatar dakai a wajen mahaifina."Wace Jarabawa ce Jamila.?"Aaa nabarwa raina kadaiji abinda nace maka idan yai maka."shikenan zan jaraba zaki fahimci manufata nan gaba."

Bata kuma cewa komai ba saidai tanajin dan faduwar gaba atare da ita."take care."kashe wayar yayi yanajin dadi a ransa yarasa dalilin dayasa akan Jamila kadai yakejin hakan itako daki ta koma tabar wanke wanken da takeyi ta kwanta tanajin tsoro na shigar ta akowane sako na jikin ta ya zata karbi soyayyar Umar?taya zaibar dabi'un sa,mahaifin ta zai amince dashi,idan yasan waye Umar mi hakan zai haifar?ya akai yasan tayi zama da Umar Sanda,tambayoyin da takema kanta kenan wanda ta gaza samun amsoshin su,juyawa tayi taja blanket tayi shiru a ciki."Jamila lafiya kike ke?"banjin dadi Umma."Allah ya sauwake kizo kisha magani."To."Tace ta sake gyara kwanciyar ta,tarasa ta ina zata fara da haka baccin wahala yai awan gaba da ita.

Share pls

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now