070

7 0 0
                                    

_*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*_

*NA*

_JAMEEY_

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*PAGE 70*

take ido ya raina fata kwarara ihu tayi mai razanarwa duk irin ihun da takeyi hakan baisa Jigiri ya rangwantawa Ladidi haka ya fidda imani ya yanke mata kunne da'ya sake kwarara ihu tayi yace."ku kara danne mani ja'ira yankata zanyi."Natuba kayafe mani wallahi bazan sake munafunci ba kada kasheni Garba."maza fadi abun da kikazo kika kafada mana."toh zan fadi nidai kada ka kasheni."haka Ladidi tafara zayyana abubuwan da suka kulla ita da Jigiri akan ya kashe Hannatu duk ta fadi tas tana gamawa yace."Ya tabbata yau sai kin bakunci kiyama sai kin rigata wucewa kiyama."Na rokeka da Allah kada ka kasheni."yiman shiru makira ke kisan irin husumar da zaki hada akan wannan abun da yafaru? Ubaidu yadawo burin mu bai cikaba gashi har sun shirya da 'Dahiru wannan bakin cikin kadai ya isa yayi ajalina."Banda makyakkyarwa ba abin da Ladidi keyi ga kunnenta tana gani kasa gashi an hanata kuka."dauki kunnen saikin cinye shi."ihu Ba'ba Ladidi ta kurma tana cewa."Wayyo Allah karufamin asiri ni ba mayya bace."ku danne mani ita."koda taga da gaske Jigiri yakeyi kasheta zaiyi da gudu ta mike ta ruga  yasa suka kamo mashi ita a harzuke ya mike tsaye yace."tunda har kikayi yunkurin guduwa babu ko shakka baki da amana ya zama dole yau ki mutu Ladidi."kayiman aikin rai..."takobi yasa ya sharbar mata a ciki take Ladidi ta fadi kasa cikin mawuyacin hali."mai gida ta mutu fa! Kakar Ubaidu ce fa."tabbas nafika sani mutuwa itace tafi da cewa da makira irin Ladidi, ko ka manta ita din bataki sun mutu ba?kada ka damu makircinta ne ya zama ajalin ta muje."Nan suka bar Ladidi kwance ba rai..Koda aka isa asibiti sun samu likita ya karbi Hannatu ba a wani bata lokaci aka samata Karin ruwa bayan 'yan gwaje gwajen da akayi mata saidai an gano an shaka mata abu mai gusar da hankali ana kyautata zaton harda hodar iblis aka shaka mata hankalin su yai masifar tashi musamman Ubaidu yanzun ba abinda yake fata sai yaga Hannatu ta rayu duk wanda kagani babu wata lakka a jikin su kowa jinin su akan hakaifa."Umma zanje gida in dawo."Mi zakayo Ubaidu.?"zan kawo maku kayan bukata kafin asallamaimu."shikenan kuje tare da 'dan uwanka mana."har 'Dahiru ya mike Ubaidu yace."Aaa Umma bai dace mu tafi mu duka ba saboda makiya kai ka tsaya nima banzan jima ba."ko kadan Kure bai yarda da yanayin abokin nashi ba sai dai baiso yayi jayayya kada Umma taga kamar akwai wata matsala, da haka yasa kai ya tafi har ya shigo cikin unguwansu kana ganin shi kaga wanda ke cikin matsananciyar damuwa."Ubaidu."a hankali ya waigo yana kallan Idi mai shayi saidai baije inda yake ba kuma bai tafi ba hakan yasa idi ya isa wajen shi yace."kayi hakuri Ubaidu banda labarin abinda yafaru sai yanzun da nike shirin tafiya gida gashi dare yayi yanzun har sha da'ya tayi."fada mani damuwar ka miyafaru ko dare ba matsalata bane."toh shikenan saman akan abinda akaima kanwar kane."da sauri Ubaidu ya kalle shi yace."kasan su kenan.?"Eh amma kada kace ni na sanar maka."su waye.?"Numfasawa yayi yace."mutanen hayin yamma ne."yaran Jigiri.?" "Kwarai kuwa sune."banyi mamakin jin haka daga gareka ba nima su nike zato gashi hasashena ya tabbata billahillazi la'ilaha illahuwa akan abinda sukayima Hannatu saidai na rasa raina bana taba barin bashin gaba koma da waye."Ubaidu na fada maka ne domin na wanke abokin ka 'Dahiru daga zargi bawai dan kaje kuyi rikici ba."Nagode maka yanzun na kara samun nutsuwa da 'Dahiru na baya cikin wannan manakisar kai kuma kafita."juyawa yayi zai shiga gida Idi yace."Dan Allah kaga dare yayi kada ku da'ga hankulan mutane."idi ba ruwan ka ni a cikin dare nike neman suna bana barin kota kwana."har zai shiga gidan sai kuma ya fasa gidan su 'Dahiru ya shiga ya dauki takobin sa ya nufi sansanin Jigiri ba tared a tsoro ko shakkar kowa ba,lokacin daya shigo cikin falorn da Jigirin ke zaune ba kowa daga shi sai Tosi suna kallan ball shi kuma Jigiri nashan lemo, babu zato babu tsammani  Jigiri yaji saukar adda a jikin shi daga shi har Tosi saidai suka razana musamman Jigiri daya kwada uwar kara mai gigitarwa tsoro razani suka rufe shi ganin Ubaidu lokacin da baiyi tsammani ba duk da yasan dole zasu hadu."kasheka zanyi Garba kayi babban kuskure da hannun ka ya taba kanwata idan har ban barar dakai ba tabbas ban cika Ubaiduddeen ba."kwalalo idanuwa yayi waje tsabar razana da kidima yace."miye hadina da kanwar ka?miyasa kake son shiga gonata."ba gonar ka nike son shiga ba kashe ka zanyi kaine ka'dai kake yiman shigar sauri."naji idan kacika Jarumin gaske miyasa zakazo man tabayan gida ai saika bari in shirya bawai kayiman dirar mikiya ba".cillo mashi takobi yayi yace."kai ko ni."da kallo yabi takobin take ido ya raina fata yasan ko giyar wake yasha bazai iya karawa da Ubaidu ba sun sha haduwa baiji da dadi ba."bana kaunar ka Ubaidu na tsaneka kuma sai nayi ajalin kanwar ka naso nayi mata fyade Allah bai nufa ba amma kasani matsawar ina rate sai naga bayan ka kuma saina wulakanta kanwar ka."wani irin makoko ya tokare zuciyar Ubaidu yanajin dacin kalaman da Jigiri yai mashi yace."nabaka dama matukar kayi nasarar kasheni ko ka nakasa wani bangare daga jikina na mallaka maka duk wani abu da na mallaka."harda kanwar ka a ciki.?" Murmushin karfin hali Ubaidu yayi yace."itama din mallakina ce."takobin ya dauka suka fara fafatawa fa'da sosai akeyi tsakanin Ubaidu da Garba sun jima ana abu da'ya saidai kaf yaransa babu wanda yai kokarin shiga tunda sukaji alkawalin da akaima uban gidagidan su babban burin su suka yayi galaba akan Deeni saidai abin ba mai yuyuwa bane kururuwa sukaji Jigiri ya kwala, Ubaidu ya sarar masa kafa take ya fadi kasa gadan gadan yai kanshi zai sauke mashi kai yaransa suka farma Ubaidu sukaita fafatawa kowa na kokarin kashe dan uwansa, Sarkin yawa yafi na karfi koda Deeni yaga zasu iya illata shi da gudu ya fita daga gidan suka rufe mashi baya sukayi cikin gari da gudu nan sukabar Jigiri rai hannu ga Allah.

★★★

"Ke zonan"Hajia Kubrah ta kirawo Jummala cikeda gadara, take saida 'yan cikin ta suka ka'da tsabar kidima da tsoro duk ya rufeta."ubanwa ya baki dama shigowa apartment din Sagir.?"dukawa tayi saman guiwarta tace."kiyi hakuri Momy, wallahi shine yace dole saina gyara masa da'kin sa."iyeh ba shakka yanzun har tsaurin idon naki yakai haka? da'kin sa fa kikace? harkin isa ki shiga bedroom din da'na."kiyi hakuri ba laifina bane."kyale munafuka Momy nifa yarinyar nan bataimin ba sam wallahi."Hunaisa tace tana janyota ta hauta da duka baji ba gani."ke Hunaisa kina da hankali kika kuma ta'ba ta saikin gane kuskuren ki."cewar Umar yai maganar ranshi a matukar bace."Yaya kana ganin abinda tayi fa."Shut up you are very stupid! idan nakaraso nan saina ballaki."dakata Umar kadaina yi mata ihu akan wannan shashashar yarinyar na fahimci akwai abinda ke tsakanin ka da wannan tsintacciyar magen ka sani baka isaba wallahi, idan har kana son kanka da arziki kajamata kunne kada na kuma ganin kafarta wannan apartment din, Sagir tsaranta ne.?"take saida gaban Umar ya tsinke da yaji an ambaci Sagir tabbas yasan waye kanin nashi baida kamun kai duk da Momy bata yarda ace 'dan ta baida mutunci a hankali ya karaso inda Jummalar take duke tana aikin kuka yace."Khadija."A hankali ta dago kanta ta kalle shi tace."na'am."miya hadaki da Sagir.?"Sani yayi in gyara masa.."yiman shiru makira ke awa da har Sagir zai saka ki gyaran daki.?" Numfasawa Umar yayi yana kallon Momy cike da rashin jindadin abinda take ma Jummala yake cewa."Amman Momy da kin barta tayi magana mana,kin san dai haka nan Khadija ba zata shigo apartment din Sagir ba,ba tare da shi ya saka ta ba." Shiru Hajia Kubrah tayi tana ma Umar wani irin kallo can ya numfasa tana cewa..

Share pls

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now