019

5 1 0
                                    

_*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*_

*NA*

_JAMEEY_

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْم

*PAGE 19*

Olori (Sarauniya)Azira na kishingiɗe saman wata lallausar shimfiɗa data gaji da haɗuwa iya haɗuwa,tareda da bayinta dake mata hidima sun kewayeta,wata baiwa ce tazo ta zube gabanta cikin girmamawa take cewa."Ekaro Olori (ina kwana Sarauniya)."tace kanta a sadde kasa."Omo Oba (Yarima) Gafar ya aikoni Allah yakara maki nasara."Jinjina kai Gimbiya Azira tayi cike da gadara gami da izzah mikamata wani karamin akwati tayi cike da ladabi,da kallo Azira ta rakata sai dai bata karbi akwatin ba duk da taji dadin jin sakon daga Gafar ne,wata hadimar ta,ta amsa a nutse ta aje gefen Azira shiru ne ya karade wajen bakajin motsin komai sai na'urorin dake aiki a haɗaɗɗan falorn,izinin tafiya baiwar tayi,sannan ta tafi."Latifa."Tace a hankali kamar bata ra'ayin yin magana."Allah yataimaki uwar ɗakina."Bude akwatin tayi dake dauke da sarkar gold and diamond kana ganin kasan ta kwashi makudan kudade,wani kayataccen murmushi ta saki a saman kyakkyawar fuskar ta."Rufe."Ta sake furtawa saman labban ta,shiru tayi tana al'ajabin Gafar a ranta tasan Omo Oba din Okeke mai amsa sunan sa jarumi hadadde ba abinda bai haɗaba na rayuwa kowace mace zataso ya zama mijin ta a rayuwa,sai dai batajin alaka zata shiga tsakaninta da Abdulgafar a rayuwar ta...Duk da kuwa ɗabi'unsa na ɗaya daga cikin abinda ke burgeta,musamman ajinsa da kyawunsa wannan dalilin yasa take bashi kaɗan daga cikin lokutan ta masu matukar tsada a hankali takai hannun ta,ta dauki ayaba tafaraci a hankali tana yatsina fuska,balla ɗaya taima banana din ta aje ta,yunkurin mikewa tafarayi saidai tunkan ta ida mikewa hadiman ta sun rufa mata baya,tana gaba suna take mata baya,ba inda sauka sai bangaren mahaifin ta,ba inda suka tsaya sai bakin kofa,ba wanda yataba ketara cikin private part din Oba Ahmad (Sarki).A hankali take taku harta isa cikin falorn shi zaune ta same shi cikin kamewa irin ta jinin Sarauta,cikin yanayin dake nuna tsananin shakuwa da kauna dake tsakanin ta mahaifin tace."Allah yataimake ka Oba mai adalcina mahaifina abin alfaharina."Ta zaune gefen shi cikin tsananin farin ciki fal a saman fuskar ta natse ya tashi zaune daga kishingiɗar da yayi ya riko hannun ta cikin tafin hannun shi."Olorin Okeke naga farin ciki kwance a saman fuskar ki tell me what happen.?"Ya tambayeta cikin tsananin farin ciki."Ranka shidade mi kake hangen akan Omo Oba Gafar.?"Maida kallan ta tayi saman fuskar mahaifin nata tana sauraron amsar da zai bata."Abdulgafar mutumin kirkine ya'ta,yana da kishi ga wannan Masarauta kuma shidin Jarumi ne,miyasa kikai mani wannan tambayar.?"Murmushi ya kawata saman fuskar ta."Sako na sarkar gold mai dauke da asirkar Diamond tare da sakon gaisuwa shine abinda Gafar ya turo mani."Jinjina kai yayi yana nazarin maganganun yar sa."Azira."Ya kira sunan ta a sifar damuwa."Allah yataimake ka."kallon ta da kyau yayi yana cewa."Karki manta kece magajiya ta  a wannan Masarauta koda zan rasa komai nawa kafin inbar duniya sai naga kintabbata bisa karagar mulkin Okeke,ya kamata kizama me kamewa kefa Olori ce kuma ta Okeke kada kimanta da haka ya'ta."gyaɗa mashi kai tayi tana cewa."Bazan taba mantawa da hakan ba Babana."murmushin manya ya saki yana cewa."Da kyau Azira kullin mafarkina da burina bai wuce inga ya bayyana ba a cikin wannan Masarauta." Gyara zamanta sosai tayi tana cewa."Waye shi.?" Firzar da naunauyen numfashi yayi yana cewa."Wanda yai sanadiyar bude ma'adana ta tarihi da dukiyar wannan Masarauta."Wannan karan damuwa ta dira saman fuskar Azira,tana cewa."Baka ganin shine zai gaji wannan kujera kuma."Saidai idan bana raye ya'ta."ya ida maganar hannunsa saman lips dinta ya hanata ida faɗin abinda tayi nisa."Oba na (Sarkina)."Tayi maganar tana aza habar fuskar ta saman kafadar mahaifin nata,a hankali ya shafa kyakkyawar fuskar ta,mikewa tayi tsaye da niyar tafiya."Odaro(Saida safe)."
Tayi mashi sallama cikin farin ciki da annuri daya kawata fuskarta."Azira." Ya kira sunan ta tana gab da barin daki juyowa tayi tana murmushi,takowa yayi har wajen ta ya sake rike hannayenta yana cewa."Kada ki zurfafa a tunanin Abdulgafar kitaka asannu kinji kyakkyawar ya'ta.?"Jinjina kanta tayi alamun to sannan ya saki hannun ta ta ida ficewa a hankali ya saki ajiyar zuciya yana maimata kalaman yarsa musamman sakon da Yarima Gafar ya aiko mata dashi,da haka ya koma ya zauna saman kujera yana tunanin kalubalen dake tunkaro su matsawar kalaman mahaifin su ya tabbata.

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now