_*🏝️NAHIYATA AREWA🐄*_
*NA*
_JAMEEY_
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
*PAGE 49*
"Ina bukatar in kasance a cikin tafiyar ka."cikeda tsarewa Kure yayi maganar wani kallo Jigiri yayi ma Kure yana cewa."tafiyata fa kace.?"cikin tarin al'ajabi da mamaki gami da shakku yayi tambayar yayin da yakejin wani irin tsoro na shigarsa kadan kadan jinjina kai Kure yayi yana cewa."ko bazaka karbeni ba in canza sheka.?" Girgiza kai Jigiri yayi yana cewa."Haba Oga Kure inani inakin ansar wannan babban kayan?daukaka suna duk kafini amma ka amince zaka zauna kalkashin ikona wannan abin daukaka ce agareni."shiru yayi kamar mai tunanin wani abu sai kuma yaja numfashi ya sauke yace."wane hukunci kayan ke.?" Rungume shi Jigiri yayi yana cewa."U're welcome Sir,ina alfahari da ganin wannan rana atare dani wannan ba karamar daukaka bace agareni ba."hade hannayen sa guda biyu yayi alamun godiya baice komai ba"Amman idan ba damuwa ina da tambaya."kallan sa yayi yace."ina sauraron ka."dan shiru yayi sai kuma yace."ya zakayi da Uban daba.?"take maganar Jigiri ta tsoki zuciyar Ɗahiru Kure baisan sadda ya zaro wukar dake cikin safar kafar shi ya daurama Jigiri ita saman wuyaba banda nishi ba abinda Jigiri keyi yana zazzare idanuwa waje cike da gargadi Kure yake cewa."idan ka kuma yiman maganar Ubaidu saidai uwarka ta haifi wani billahillazi la'ilaha illahuwa."tunkudar dashi yayi gefe yana huci kamar wani zaki,shi kanshi Jigiri jibi kawai yakeyi yana zazzare idanuwa waje ranshi duk ya baci sunfi minti biyar ahaka kafin Kure ya koma ya zauna bisa kujera ya dafe kanshi dake neman tarwatsewa kowa daga cikin su yayi shiru kamar ba kowa cikin dakin Kure ya nusa yace."na fara karya dokar ka amatsayin ka na uban gidana a halin yanzun na miko maka na Annabawa."jinjina kai yayi yace."bakomai ya wuce."tashi yayi kamar zai fita sai kuma ya dawo ya isa gaban Jigiri ya daura kafarsa saman hannun kujerar da yake zaune akai yace."inada sharuddana idan kaji zaka iya i will be a member in your group idan bazaka iyaba shikenan."ina jikinka."duk abinda ya dangance ni nida Ubaidu kada ka kuma taso man dashi ba ruwanka da alakar dake tsakanina dashi,sannan inada right da zan gunar da sabgar gaba idan har bai shafi taka sabgar ba wannan sune sharuddana ko hakan yayi maka.?"Eh yayi mani dari bisa dari."da kyau nabarka lafiya."juyawa yayi ya tafi hankalinsa kwance,tunda Kure ya fita Jigiri yahau fita kamar wanda yayi dambe da zaki,zakinma bijimi."Kaina bisa wuyana Oga."mi akayi Tosi.?"kana ganin zamanka da Kure zai yiyu yana baka umurni amatsayin shi na yaron ka.?" Murmushi Jigiri ya saki yana cewa."Hmmm zai yuyu mana,kana tunanin zanbar Kure ya kubuce mani bayan damar dana samu zan rayu dashi?inaga bakasan irin nasarar dake tunkaromu bane inaga."haba Oga shidi mutun ne mai hatsarin gaske."ba wannan nike dubawa ba Tosi nasarar dai kawai."wace irin nasara ce wannan mai gida.?"daga lokacin da Ubaidu uban daba yasamu labarin amininsa kuma masoyinsa ya dawo tafiyata daga wannan ranar bazai kuma samun nutsuwa aran sa ba zai daina murmushi zai rayu cikin kunci har abada daga lokacin zan samu damar dazan kara farraka tsakaninsu zasu zama abokan gabar juna yanda Ubaidu ya cika zuciya ta da tarin tsoron sa da shakkunsa har yake yanda yaga dama a yankin mu nima haka zan cika zuciyar sa da tarin kokonto akan Kure na rantse da mahalicci kaf dinmu ba wanda ya isa ya iya karawa da UBAN DABA sai KURE."miyasa kace haka mai gida sai inga Uban daba yafi karfin Kure."Kwarai kuwa bakayi karyaba saidai Kure shine raunin Ubaidu bazai iya biye Ɗahiru suyi fada dashi ba kuma a halin yanzun ya fusata zai iya aikatama Ubaidu komai akan mahaifiyarsa."Hahhhhha kace hakarmu tacima ruwa."kwarai kuwa Tosi amma akwai kalubale."name kenan.?"Dole sai mun rike wannan sirrin."Allah yataimaki oga,wane sirri ne wannan.?"Dole mu boye mune ainahin wa'anda suka rurura wutar dake wakana tsakanin Kure da Uban daba,idan mukayi haka munci lafiya."gaskia ne Mai gida baka da matsala."da kyau."
☆☆☆☆
Fitowar shi kenan daga wanka kugunshi daure farin towel yana tsane lausassar sumar kanshi da karamin towl tsaye yake gaban tafkeken mirrow wanda baida mararraba da na mace saida ba abinda ke tashi saman mirrow din irin turaruka da man shafawa a hankali ya dauki robar mai ya matsashi a hannu yafara shafama soft din fatarshi duk da kasancewar damatsen hannun sa a murde suke kana ganin shi kasan shidin ma'abocin jim ne kuri yaima madubin yana karema kanshi kallon dake nuna akwai abinda yake nema atattare dashi."miye abuna.?"ya furta saman labbansa a hankali still yana kallan mirrow."why are you hating me uhmm.?"wannan karon maganar da yayi kamar yanayine da wani kuma yana bukatar amsa.ki soni koda kwatan son da nike maki ne!fesar da zazzafar iskar bakin shi yayi ya dauki kwalbar turare yafara fesawa jikinsa saika rantse da Allah saiya karar da turaren a sanyaye ya ajeta yana jan numfashi mai zafi ya kuma fesar cikin kankanin lokaci idanuwan shi sun rine sunyi jajir dasu kamar garwashi."i love you Jamila,i love you more pls stay with me."wannan karon duka yakaima mirron take ya tarwatse har saida karar ta karade illahirin gidan wanda yai daidai da mikewar yaransa dake zaune falorn kasa suna shan shayin buzu."lafiya.?"Dila ya tambaya yana kallan Jigida."i don't know."kallan yaransa yayi dake zaune wajen take kowa yabar falorn ya rage daga Dila sai Jigau wa'anda suka kasance manyan yaran Umar Diga duk da kowane a cikin su yanada nashi mahimmancin."akwai matsala."Jigau yace yana cire malfar dake kanshi,murmushin gefen baki Dila ya saki wanda ba lallai bane ka gane yayi shi ba yace."ya zama dole mu nemi sanin damuwar Boss na fahimci kullin yana cikin weak hakan na nuna gazawarmu kenan,hakan ba karamin illa bane agaremu kodan abokan hamayya ya dace...."Dila."Jigida ya tareshi a kausashe shiru yayi yana kallan sa cike da mamaki."ka iya kalamanka."jinjina kai yayi ya koma ya zauna kowa yai shiru duk da azahiri zakaga damuwar su saman fuskokin su."idan baki sona,bansa ya zanyi da raina ba kinyi mani illah why kika kasance tareda dani why."wannan karon cikin raunin dashi kanshi baisan yanada shiba yayi maganar jan kafarshi yayi zuwa gaban press din shi ya dauki shadda yasa sai takara fidda nasabar sa kana ganin shi kaga cikakken kamili hularsa yasa ya dauki agogonsa ya kafa bisa kansa yasa takalman sa saiya fito a Ummarul-Faruq Abdulfatah Umar cikakken bafulatanin nan na ruga mai tsananin kyau wayoyinsa ya kwasa yayi kasa tunda suka jiyo sautin saukowarsa kowa daga cikin su yagaza samun natsuwa baki dayan su suka mike jikin su na rawa suka zube bisa gwiwowin su kamar wa'anda sukayi laifi..."Boss barka da fitowa."baki dayan su suka hada baki wajen furtawa."one by one yake kallan su duk sai sukasha jinin jikin su yakai three minute yana aikin kallan nasu sai kuma ya dauke kai gefe yace."Jigida zamu fita."a razane Dila ke kallan Umar Diga shima din Jigidan cikeda mamaki yake kallan uban gidan nasu kamar yanda al'adar Umar Diga yake kowa yasan inda fitace zaiyi baida wanda ya aminta ya fita dashi kamar Dila idan kuma sirrin sane Jigida,duk wani aike kuma Jigau sai sukaga sabanin hakan shiru duk sukayi kowa na al'ajabin lamarin Umar,da sauri Dila ya sauke kansa kasa samakon shu'umin kallan dayake jifan shi dashi har saida yan cikinsa suka kada."Boss..."da sauri ya da'ga mashi hannu alamun yai mashi shiru hakan kuwa akayi Dila bai kuma gigin magana ba juyawa yayi ya nufi main entrance da sassarfa Jigida ya maye mashi baya har yana hardewa kamar zai kife kasa,yana suna fitowa sauran yaran nasa suka mike kowa na kwasar gaisuwa duk da haka Dila baiyi kasa a guiwa ba saida ya taku masu yafara shirin hada conver cikin kankanin lokaci har an fiddo da zuka zukan motaci shidai Diga baice da Dila komai ba saidai idon dayake binsa dashi."My Boss an hada komai Allah yakaika lafiya ya dawomana dakai lafiya."dan murmushin gefen baki ya saki wanda ya kara wadata kyawunsa yace."is my Secret....bana son zuga."jiki Dila ya kuma sanyi dan ba haka yaso ba duk da yasan badashi zai fitaba yaso yatafi ta convey dan yasamu information daga yaransa da suke cikin convey din Diga."Safe trip."ya furta kasan makoshi,jijjiga kai yayi yai gaba,da gudu Jigida ya bude masa zukekiyar hond accord dinshi kirar 2014 fara dal da ita sai walauniya take a hankali ya zauna saidai kafarsa na waje still yaran nasa yake kallo yace."Jigau."yes boss."take care."ur order is concense."rufe marfin motar Jigida yayi ya koma driver sit ya shiga sannan yaima motan key har zasu bar harabar gidan yayi kasa da glashing motar yace."Dila."my boss."be careful."zuge glashing motar shi yayi suka fice sukabar harabar gidan baki daya a tsanake Jigida ke tuke saidai baiyi gigin yima uban gidan nashi magana jinin shi kan akaifa saida sukayi tafiya mai nisa yace."Allah ya huci zuciyar mai gidana ina muka nufa."?cikin ladabi yayi maganar yana ci gaba da driven dinshi cikin natsuwa da takatsantsen."gidan su zaka kaini."angama ranka shidade."juya akalar motar shi yayi ya nufi yahayya madawaki way sannan ya dauki hanyar da zata sadashi da unguwar su Jamila.
☆☆☆☆
"Rundunar 'yan sanda takasa ta wakiltaka a taron da za'a gabatar yau da misalin karfe biyu na rana a babban birnin tarayya ina fatan kasan da wanzuwar wannan zaman da za'ayi.?Umar Sanda dake tsaye ya sake sarama shugaban nashi kamar yana gaban shi yace."Yes sir."yana da kyau ka shirya immediately ka tafi anyi maka booking komai da komai hope ba wata matsala."cewar Inspector General(IG)."No problem Sir."good ina jinjina maka jami'in tsaro mai adalci Umar S Umar best of luck."thank you Sir."am hearing for you."Ok sir."ya sake sara mashi sannan ya kashe wayar,da ido ya raka wayar ya koma ya zauna ya rafka uban tagumi sai kuma ya tashi daga zaman da yayi ya dauki telephone yayi kira."hurry up."abinda yace kenan ya aje phone din bai jima da gama wayar ba ya iso."Yes sir."ya kame yana sara masa."kaje ka shirya mota zaku fita by 1 flight dina zai tashi."Okay sir."fita yayi dan cika umurnin shugaban nashi.
☆☆☆☆
Shigowar ta keda wuya ta iske Ramlat nata garzar kuka kamar ranta zai fita da sassarfa ta karaso inda take ta tallobata jikinta tahau lallashinta koda taga kawar tata batasan sadda ta sake rungumeta ba tahau kuka mai sosa zuciya ba."Na shiga ukkuna Musriya bansan ya zanyi ba."sorry tashi mu shiga ciki ba girman ki bane ki dinga zubda hawayen ki a banza ba."kamata tayi sukayi cikin bedroom dinta da kallo Bilkis tarakasu tana al'ajabin halin da uwar ɗakin nata ke ciki da haka takoma kitchen domin aiwatar da aikinta. "Miyafaru kike kuka irin haka.?"ɗago jajayen idanuwanta tayi kamar rushi ta kalli Musriya tace."dole nayi kuka Musriya wallahi Ya Faruq bai kaunata karkiso kiga irin cin mutuncin da yaimin nagaji wallahi."murmushin takaici Musriya tayi tace."first of all miya hadaki dashi.?" Share hawayenta Ramlat tayi tana cewa."Mifa?daga sunyi fada da Khalid na nuna masa aibun wulakanta bako shine fa ya kira da bush girl!hakan bai masa ba ya kara da stupid! Haba Musriya what kind of nonsense Ya Faruq keson ya maidani kamar dai mace ba kalleni mina rasa usuli dukiya ko kuwa tarin nasaba."fesar da numfashi mai zafi tayi tace."OMG komai ya rushe mana mun dauko plains dinmu gashi yanzun ya rushe mana yanzun minene abinyi.?" Girgiza kai Ramlat tayi tana cewa."Bawani abun yi Musriya is over nagaji da wulakanta kaina da nikeyi akan Faruq kawai dan yaga ina son shi."idan baki bata time dinki what do you to do know?."Himm Musriya kenan saina baki mamaki idan nacika Ramlatu sunana hafaffar Abu Dabi 'ya ga Alhaji Ishaq saina bawa Faruq Umar Faruq mamaki saina zame mani rakumi da akala wallahi."the hole Faruq din taya zaki iya maida shi rakuminki?."what the hole Faruq mutun fane kamar kowa kasancewarsa president son bashi ke nuna yafi kowa ba,kema kinsan ban auri Faruq ba dan tarin dukiyarsa na aure sa ne domin in shiga tsara kasancewar shi handsome kema kinsan hakan tunda yaki biyuwa zan sauya taku."iskar bakinta ta fesar tace."minene plains din da zakiyi appying? "You should wait and see idan nayi reaching my goals zaki sani daga lokacin."shikenan my advice kidaina nuna raunin ki akansa hakan babban kuskurene."truely nima ba fahimci hakan."my lovely kawata."murmushi Ramlat ta danyi kadan."miya hada Khalid da Faruq."i don't know ina zaton da ya yabeni shiyasa."da mamaki sosai akan fuskarta tace."yabo kamarya.?"dariya Ramlat tayi tace."he said na taimaki Faruq dana aure shi i think shine ya sosa masa rai."Hmm Faruq problem,minene abinyin fushi daga fadan wannan kalman."kingani dai."tayi maganar cikin tarin takaici."nasan abinda zanyima Umar wallahi."mi zakiyi mashi.?"Bazanje Katsina ba that's all."kinyi kuskure gaskia kije kada kiyi gingin kin zuwa."Hmm idan nace ban zuwa dole Dady zaisan dalilin kin zuwana."saiki ce masa me."Hmm nafada masa gaskia mana."kada kiyi haka idan kika fada kin nemi sulhu kenan cikin ruwan sanyi idan kikaje har kuka dawo daga bisani saikiyi appying plain din da kike son yi."dan shiru tayi kamar mai nazari sai kuma."you are right zanyi anfani da shawarar ki."da kyau."fira sukaci gaba dayi rabi da kwata Musriya naba kawar tata shawarwari.
share pls
YOU ARE READING
NAHIYA TA AREWA
General FictionThe Story of Nahiyata Arewa is the one that comprise the most important things such as Correction,Injustice,Betrayl and Revenge including Entertainment and Education, is a Falatable and testable story.