_*🏝️NAHIYATA AREWA🐄*_
*NA*
_JAMEEY_
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
*PAGE 57*
Bayan sallar la'asar convey din Umar Diga keta faman tsere bisa titin babban birnin Katsina yanda suke zabga gudu kamar wasu kusoshin gwamnati ba inda suka dosa sai unguwar su Jamila tafiyar da batafi 30mint ba har sun iso kofar gidan su Jamila horn Dila ke dannawa mai gadi da sauri M. Gambo ya bude masu gate saidai duk uwar zugar jama'ar Umar din motar Dila ce kadai ta kutsa kai cikin gate din gida,a hankali Umar ya sako kafar shi kasa cikin danyar geznar shadda royal blue bakaramin haskashi tayi ba daga hannun damar shi Ubaidu ne tsaye shima cikin shaddar yake sea blue tsaye suke bayan anyi masu izini zuwa cikin falorn da ake sauke baki wannan Karon Umar da Ubaidu ne kadai suka shiga cikin gida basufi minti biyar da zama ba suka tsinkayi sallamar Baba cikeda girmamawa Umar ya sauko daga saman kujerar da yake zaune ya gaishe da Baba kanshi sadde kasa cikin tarin kamewa da kamala, shima Ubaidu yanda yaga mai gidan nashi yaba Baba girma haka shima ya bashi duk da baisan waye shiba a wajen Umar saidai daga yanda yaga Umar din na girmama dattijon yasan bakaramin muhimmanci gareshi a wajen Umar din ba."Haba da'na ka koma saman kujera mana ba na haneka zama kasa ba."cikin tarin kamala yace"albarkar ka kawai nike nema Baba nan din ma yayi mani nagode."Allah yaimaka albarka Umaru ya kareka daga sharrin makiyan ka."Amin suka hada baki wajen firtawa shida Ubaidu."Baba ga kanina nan nakawo maka ku gaisa sunan shi Ubaiduddeen"fuskar Baba dauke da annuri yake kallan Ubaidun yace."ka kyau ta naji dadin wannan ziyara taku Allah yaima rayuwa albarka"Ameen suka kuma gaisawa 'danjim kadan sukayi Baba yace"yawwa Umaru dama ina so inyi magana dakai"toh Baba"kwanaki nadawo gida na iske kayan masarufi masu yawan gaske abokin ka Salisu ya kawo su, dan Allah daga yau bana son kana kawo kaya irin haka a gidan nan, wannan girma da kake bani kadai ya wadace ni, ina fatan zaka fahimce ni.?"a hankali Umar ya dago kanshi ya kalli Baba kallan dake nuna karantar yanayin mutun duk da baiga alamun fushi ko wani sauyin yanayi daga surukin nasa ba yace"kayi mani lamani Baba duk wani 'da nagari burin shi ya kyautatawa iyayen shi, wannan shine burin zuciya ta a kullin dan Allah Baba kada ka yanke mani aikin lada irin wannan kamar yanda nafada maka tun farko albarkar ka nike nema a matsayina na 'da a wajen ka. "A jiyar zuciya Baba ya shide yace"nafahimce ka saidai ina so karage idan bukatar hakan ta taso ni kaima mai iya yimaka magana ne"badan Umar yaso hakan ba ya gyada kanshi cikin girmamawa.Da sauri ya da'go kansa ya maida saman kofa sakamakon sallamar ta data karade illahirin falorn cikin dakeken lace take sanye Royal blue bakaramin ansarta yayi ba daga shi har ita kowa kallan 'dan uwan shi yakeyi yayin da zukatansu suka samu tsinkewa da bugawar da kowa ya rasa dalilin sa a lokaci guda, takai minti ukku tsaye hannun ta dauke da tired lemu da ruwa tana kallan su kamar taga wasu baki a hankali ta tako kafarta cikin karfin hali ta tunkaro cikin falorn yanda suke kusantar juna haka zukatansu ke faman racing daga Jamila har Umar din, duk da kasancewar idonsa na kanta saidai ba lallai kagane ita yake kallo ba, a hankali ta aje masu tiren ta zuba ruwa ta kikewa Ubaidu."yauwa sannu."maganar Ubaidu ta dawo da Umar duniyar shagala da razani zuwa duniyar zahiri yayin da Jamila ke miko mashi ruwa a glass cup saidai kaf tunanin sa da nutsuwarsa ta gushe daga gareshi na wucin gadi"Ya Umar"ta samu kanta da furta sunan shi da 'dan karri, a kidime ya amsa"kanwata sannu da kokari"yasa hannu ya karbi ruwan yayin da hannun shi ya taba soft and glowing hand dinta garin ansar ruwan, wani irin shock ya tsargama Umar har cikin kanshi na wani irin bakon yanayin da bai taba jin kanshi a ciki ba har saida ruwan dake hannun shi ya samu damar zubewa kasa daga shi har ita kowa ya daburce ta silar haduwar da hannayen su sukayi da juna"sorry"dan gyaran murya Baba yayi hakan yasa Jamila ta mike a razane tana kama kanta ta hanyar tattaro da sauran jarumtar ta zuwa nutsuwarta."haba 'yar Baba ki kula mana so kike ki ba'tama da'na Niki, ke ciki ki dauko mopa daga nan kiyi kiran Umman ku ta gaisa da 'danta ko? "To Baba"jiki mace ta koma cikin gidan saidai kaf nutsuwar ta ta gallabeta ita kanta tana mamakin kalar situation din data tsinci kanta a ciki mi hakan ke nufi, shiko Umar ko ruwan ya gaza sha duk Jarumtar shi da kokarin boye yanayin da ya shiga saida hakan ya gagara agare shi"Umaru kasha ruwan mana ko bakajin dadi ne"da sauri yake girgiza kanshi saidai bakin shi yai mashi nauyi matuka da haka yafara shan ruwan yanayin wani irin test na daban dadinsa ya gauraye mashi baki har wani gardinsa yakeji sai yaji kamar shine ruwa mafi dadi daya ta'ba sha a rayuwar sa, bayan fitar Jamila da mintin da baifi bakwai ba Mama ta shigo da sallama dauke a bakin ta kujera ta samu ta zauna tana"ina babban 'dan nawa yake? Ina Ummarul-Faruqun"wani irin dadi ya lullube zuciyar Umar duk lokacin da iyayen Jamila zasu kirashi da 'dan su yakan kasance cikin tarin farin ciki a cikin zuciyar shi"Sannu da zuwa Umma na"yawwa Faruqu ikon Allah yau dai naga gwarzon da'na"murmushi yayi har saida hakoransa suka bayyana yace"ina mai farin cikin ganin wannan rana dana gana da mahaifiyata a koda yaushe albarki da addu'oin ki agareni sune babbar nasarata Umma, ina rokon zan samu albarkar ki"cikeda gamsuwa takejin dadin kalamanta tabbas tasan ta rasa 'da Umar dinta mafi soyuwa agareta sai gashi Allah ya kuma bata wani Umar din akaro na biyu kuma a matsayin 'da"tabbas Umaru indai addu'ar mahaifya ce kasamu Allah yaimaka albarka"Amin Umma na nagode...ga kanina Ubaidu"sannu Ubaidu Allah yaimaku albarka"Amin Umma"kusan a tare suka mike ita da Baba lokacin Jamila ta shigo hannunta rike da mope saidai duk abinda suka tattauna da Umma taji komai tana mamakin kalan mahimmancin da suka bawa Umar ba a garesu duk da basu sa shidin waye ba, sudai zuciyar su mai alkhairi ce yakan kyautata zato ga kowa, wannan shine babban dalilin da Baba yai saurin amin ta da Umar"ki shigo mana kika tsaya"maganar Umma ta yanke mata tunanin data zurma shigowar tayi tafara goge ruwan da suka zubda"idan kingama tsane ruwan kizo ki kawo masu abinci"toh Umma"da'na ka tsaya kaci girkin Umman ka"murmushi yayi mata yace"toh Umma na nagode"da haka suka fita ita da Baba, har Jamila ta gama goge ruwan tanajin idanun Umar akanta har ta soma tsarguwa cikin sassarfa ta juya zata fita saboda bazata iya jure kallan kurillan da yake aika mata"Jamila"cak ta tsaya saidai takasa juyowa tsabar kwarjinin daya cikata dashi"bazaki gaida yayan ki ba? Kuma ga kanin ki baku gaisa ba"wani irin nauyi ya saukar mata ji take kamar ta nutse tarasa miya shigeta ba kadan takejin takura ba duk sanda zasu hada idanu da Umar, juyowa tayi a sanyaye tace"barka da rana"murmushi Ubaidu ya samu kanshi da yi mata yace"yawwa Anti na"kamar walkiya ta fice daga falorn har tana neman kifewa"miye haka Jamila baki gudun kada kiji ciwo"Murmushin karfin hali ta kakaro tace"tuntube nayi"ki kula dai"gyada kanta tayi sallamar Dija suka tsinkaya da sauri Jamila ta rungume ta tana"Oyoyo my Dijja"Miss you my dear, Umma barka da rana ya aiki"Dijja tace cikeda girmamawa"yauwa Khadija ya Umman ki"lafiya lau"kikayi tsaye dauki abincin mana, Khadija tayata ku kaima yayan ku abinci"toh Umma"dauka tiren abinci Jamila tayi ita kuma Dijja ta dauki na fruit sukayi falorn baki kusan a tare sukayi sallama suka aje masu abinci"ina yini"Dijja ta gaishe shi a mutunce"lafiya lau...Dijja ko.?" A razane Jamila ta kalli Umar saidai ita Dijja bata kawo komai a tanta ba"Eh sannun ku da hanya"yawwa Dijja ya kawar taki hope kina kulaman da ita ko?" Jinjina kai tayi tace"sosaima"thank you so much Dijja"a tare suka mike bayan ta zuba masu abincin suka juya zasu fita"kanwata"kallan shi tayi saidai bata amsa ba"zanso inyi magana mai mahimmancin gaske dake"samun kanta tayi da gyada masa kai duk da a zuciyar ta ba hakan taso ba saidai ta gaza yi mashi musu, samun kanta tayi da komawa yayin da Dijja ta fita kujarar dake facing dinshi ta zauna tana wasa da yatsun hannayen ta duk ta takura, a hankali ya fesar da iskar bakin shi tareda sauke sihirtacciyar ajiyar zuciya ya dauki abinci ya diba yakai bakinsa take ya rufe idonsa ba kadan yaji dadin jellof din taliyar ba tasha man shanu da kifi a ciki"Ya Allah karawa mahaifiyata lafiya da nisan kwana a gaskia Umma na ta iya girki, ina fatan kema kin kware kamar haka"samun kanta tayi da murmusawa har saida fararen hakoran ta suka bayyana ba karamin dadin haka Umar din yaji ba"ban iya ba"tace a takaice saidai still a nurin fuskar ta ya gaza daukewa"tabb kice ina da aiki sosai agabana kenan"uhmm"ta kuma furtawa a hankali"Jamila baki son yin magana ne? Kodai baki lafiya ne? Ki sanar mani da damuwar ki mana."a raunaraunane yayi maganar hatta Ubaidu kallan shi yakeyi shidai kanshi ya kulle duk da ransa naba shi son Jamilar yakeyi saboda kwayar idonsa da kalaman sa ya fallasa hakan musamman raunin dake bayyane ta salon maganar sa, itama din kallan sa takeyi a tanta tana ayyana(jibe shi dan Allah kamar mutumin kirki duk yabi ya tsare zukatan iyayena koma minene damuwar sa da matsala ta ohni Jamila tawa ta sameni) "kanwata tunanin me kikeyi?"samun kanta tayi da jin kunyar sa akaron farko da Jamila taji kunyar Umar sakamakon kamata da yayi tana kallansa kamar ta samu TV saidai a wajen shi baiji ta dauwama tana kallan sa ba duk da shidin ba ma'a bocin son kallo bane"tunda Allah yasa kayi ta siri irin haka wajen Baba sai kayi duk yanda zakayi kasa ya hakura ya maidani wajen aikina tunda kaine sila nasan ba abinda zakin bakinka ba bazaiyi ba"tunda tafara magana yake kallan cute lips dinta Suna motsawa a nutse murmusawa yayi yana cewa."Wato dadin baki ne dani kenan? Well indai aiki ne kisa aranki zaki koma but da sharadi."cike da mamaki take kallansa tana cewa."duk da kaine sila kuma sai kasa mani sharadi.?" Gyaɗa mata kai yayi yana cewa."da ace zaki daina wannan ikirarin tabbas da zanyi farin ciki! sharadin ba wani bane zan sanar maki."jinjina kai tayi, a hankali ta yunkura ta mike tsaye."ina zaki.?"wajen Dijar ka."murmushi kawai yayi jin abinda ta fada."abu mai mahimmanci shi ake bibiya har asan komai akansa kada kiga laifina."murmushin karfin hali tayi ta fita, tana shiga dakin ta ta iske Umma da Dijjan Suna fira
"haba Jamila kinje kin zauna kin barta ita kadai."kiyi hakuri Umma, Ya Umar ya tsaidani wai miyasa na aje aikina, shine yace zai nema mani alfarma wajen Baba."Allah yasa ya amince"Amin"fita Umma tayi, zaunawa Jamila tayi tafara cin abincin da ta iske Dijja naci."kawata waye wannan Umar din?"A hankali ta dago kanta tana kallan Dijja, ajiyar zuciya ta sauke tace."Shine na baki labarin sa a baya."wane ciki Umar Sanda?" girgiza kanta tayi tace."Aa da'yan."dariya Dijja tayi tace."su Jamila mai Umarori."itama dariyar tayi tace".wai Umarori."eh mana ki dinga cema wannan Faruq mana kinga saiki banbance sunayen su."kinga Dijja shifa wannan Yayana ne da haka Baba ke kallansa shi kuma wancen ya gabatar da kansa wajen mahaifina kinsan dai ya nemi izinin aure na."hakane amma kwayar idanun ki kadai sun fallasa wannan din kike so."kidaina fadan haka Dijja kada Umma tajiki, kinsan Baba baisan akwai wata alaka a tsakanin mu ba."idan ya gane hakan ba."inajin shakka da tsoro."mafita itace ya fada masa gaskia yana sonki kada garin neman gira ku rasa ido."ajiyar zuciya ta shide tace."mubar wannan maganar Dijja."Uhhh alright shifa Sandan yana zuwa.?"ya fiye gadara da girman kai, yana kiran waya dai idan naso na dauka kinsan baya kasar amman acewar sa yau zaizo kuma zaiyi surprise dina."look at you, haba Jamila ki basa dama."isarsa bazata bari ya nuna son sa tsantsa agareni ba."haka kike gani ba"Hmm Dijja kenan"ba wani Dijja kenan kedai za'a cewa Jameey kenan, ni dai ba wannan ba indai da gaske yau din zaizo zan tsaya ingan shi a zahiri sabanin a tv da nike ganinsa, I see shida Umar wa yafi wani."hmm gaki ga su ai kota goyon bayan su."naji bakomai."ni ki kyaleni naci abinci na."da yake rike Mali hannu nayi."abincin taci gaba daci, a bangaren Umar suna gamawa sukayi sallama da Baba, sannan suka fita da sauri Dila ya bude mashi kofa daidai hancin motar Umar Sanda ta danno kanta a cikin harabar gidan yanayin parking ya fito jikinsa sanye da farar shadda sai daukar ido yakeyi wani irin ba haggon kallo sukema junan su cikeda tarin mamakin gami da al'ajabi musamman fuskar Umar Sanda data gaza boye hakan saidai shi Umar Diga hakan bai dimauta shi yasan yana hudda da gidan duk da baisan zahirin abinda ke kawo shi ba abinda ya dauka yana binciken Jamila danjin sirrinsa tunda shi kadai ne yasan yayi garkuwa da ita a hankali Sanda ya tako kafarsa ya iso gaban Diga kallan kallo akema juna mai dauke da tsantsar tsanar junan su da sukayi Sanda yace....Share pls
YOU ARE READING
NAHIYA TA AREWA
General FictionThe Story of Nahiyata Arewa is the one that comprise the most important things such as Correction,Injustice,Betrayl and Revenge including Entertainment and Education, is a Falatable and testable story.