_*🏝️NAHIYATA AREWA🐄*_
*NA*
_JAMEEY_
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
*PAGE 84*
*ZAMFARA STATE GOVERNMENT HOUSE*
Zaune suke a office din His Excellency Alhaji Abubakar Mudi kowa ka kalla fuskarshi cike take da jimami ba mai wani farinciki a cikinsu saboda tashin hankalin da aka tashi dashi a jahar Zamfara a karamar hukumar zulmi yan kiddneping ne suka kai masu shamame a cikin dare sukayi kan mai uwa jawabi sun kashe mutune sun fi goma banda wanda akayi ma raunika da kuma wanda aka ɗauke sunfi talatin ba karamar barna akayi ma mutunen zulmi ba, furzar da naunauyen numfashi His Excellency Alhaji Abubakar yayi yana cewa."Ya zama dole a kawo karshen wa'annan mutunen a wannan jaha tamu idan har kuwa ba haka ba sannu a hankali zasu ƙarar da mutunen jahar nan tunda ko ina shiga suke suna kisa suna ɗauka dan haka ina son a gaiyato man yan-jarida dan inason na isar da sako ga al'ummar wannan jaha tamu ta Gusau."Numfasawa secretary yayi yana cewa."To shikenan Ranka ya daɗe za'a gaiyatosu kamar yanda ka buƙata sai dai nike ga mai zaka ga ya masu ne His Excellency?Tunda Allah yasa an shigar masu gari an kuma yi masu barna ai sai suyi hakuri tunda bamu muka aika su ba bama musan su waye suke aikata wannan laifunka ba."Girgiza kai His Excellency yayi yana cewa."Amman Alhaji Kabir banyi tunanin jin haka daga bakinka ba,ko ka manta hakkin su na kainmu nauyi ne babban a kanmu na kare masu duniyoyinsu da rayukansu da komai nasu saboda haka aka zabe mu dan yin wannan kokarin da kuma yardar Allah,idan har ba'a tausashesu ba aka kuma yi masu albisir da za'a kawo karshen mtslr nan da kuma za'a anso masu wa'anda aka dauke masu dan zuciyarsu ta danyi sanyi ya kake so ayi masu?yanzun ayi wannan barnar mutun sunfi goma da rahoto yazo mana dashi an kashe dan haka ni yanzun zan saka a shirya man tafiya zuwa zulmi dan na hallaci jana'izar mamatan inason kafin na dawo daga jana'izar yan-jarida sun gama hallara."Maida kanshi ƙasa kawai Alhaji Kabir yayi sai can ya numfasa yana cewa."Shikenan His Excellency Allah ya maidoka lafiya ina ga dani za'a yi wannan tafiyar ma."Jinjina kai His Excellency yayi bai sake cewa komai ba sai tunanin rayuwa da halin da mutunen suke cike na talauci da bakar yunwa ga kuma rashin kwanciyar hankali da mai ake son talakawa suji? shiru kawai yayi yana jiran a gama hada tafiyar ya fito suje..koda Alhaji Kabir ya koma office din shi zama yayi yana kiran waya ta bada umurnin haɗa ma His Excellency tafiya zai fita yanzun sannan yasa akayi kiran yan-jarida ƙarfe 4pm His Excellency zaiyi fira dasu,daukar wayarshi yayi yana cewa."Ya zama dole fa mu ƙara mikewa tsaye mu hana His Excellency dakatar da wannan harkar idan ba haka ba ɓata mana komai zai yi fa fissabilillah,yanzun wai kaji gaisuwa zaije da jana'iza zai yi magana da yan-jaridu kuma zai kawo karshen mtslr kiddneping idan har mukayi sake kasan dai murkushe wannan harƙalar ba wahala zai yi mashi sai muyi maganin abun tun wuri ba yanda za'ayi muna samun zunzurutun kuɗaɗe irin haka yazo ya wani ɓata komai shi uban yan tausayin tallaka."Numfasawa akayi daga ɓangaren wayar ana cewa."Rabu dashi Alhaji Kabir ya gama duk abinda yake kokarin yi sai dai kace bamu ba idan takamarshi ya saka yan-sanda dan kawo karshen mtslr ai yan-sandan kansu namu ne suma ana kasawa ana basu wani abu balle ma wallahi Alhaji Abubakar bai isa ya dakatar da kiddneping ba idan har ba mune nan muka so hakan da kanmu ba kuma tunda haka ne a fara yi mashi warning aja kunnensa akan ya fita a sabgar nan kawai ya saka ido idan kuma zaiyi taurin kai shi mai gaskiya mai tausayin tallakawa to zamu saka shi kuka daga karshe bikin ciki yayi ajalinshi tun da yana da uwa tana raye kuma yana da yara mata dan haka dole ya fita a sha'aninmu kodan ya tsirar dasu daga hatsarin da yake kokarin jefa su."Wata uwar dariya Alhaji Kabir ya dauka yana cewa."Uban kowa shiyasa nike bala'in Kaunarka idan da kai bamu da damuwar komai.'shima dariyar yayi yana cewa."Ai dolenshi ya saka mana ido muci karanmu babu baibaka su waye suka ɗaura shi akan kujerar idan bamu ba?idan da bamu so ba ai da bai shiga office din da yake ciki ba a yanzun dan haka shi aikinshi singing to ya zauna yayi singing dinshi mu kuma ya barmu mu juya Zamfara yanda muke so da mutunen cikinta."Dariya suka cigaba da yi tare suna ƙara tsara komai suka kashe waya akan za'a hadu a guest house din Alhaji Sanusi dan ƙara tsara yanda kiddneping zai ƙara kasancewa a jahar...His Excellency Alhaji Abubakar Mudi shi da Alhaji Kabir da wasu manyan gwamnatin Zamfara sun hallaci jana'izar Mutanen da aka kashe a karamar hukumar zulmi sun kuma yi masu jana'iza wani matashi ne ya mike tsaya yana cewa."Bamu so bamu son wata jana'izar munafinci da aka zo mana mu ba ita muke bukata daga wajen His Excellency ba,so muke a kawo mana karshen wanann matsalar tsoron da muke fuskanta dan muyi rayuwarmu da iyayenmu da yaranmu cikin salama da kwanciyar hankali muji da wannan bak'ar tsadar rayuwar da muke fama da ita."take wajen ya ɗauka da bamu so mun gaji da mulkin zaluncin da ake mana a wannan gwamnati,take DSS din da suke tsoron His Excellency suka taso dan kama mutune dakatar dasu His Excellency Alhaji Abubakar Mudi yayi ba tare da yace komai ba dan bai ga dalilin da za'a kama mutune dan sun fadi gaskiyarsu ba ai ba karya sukayi ba dan sunce sun gaji da mulkin zaluncin da ake masu girgiza kai kawai yayi suka tashi suka tafi ba tare da yace komai ba bayan kara yi masu gaisuwa da yayi, take jahar Zamfara ta ɗauka da karfe hudu na marece His Excellency Alhaji Abubakar Mudi zai yi magana da yan-jarida kai tsaye za'ayi firar tun karfe 3:30 mutune suka fara kunna rediyon su wasu kuma suka zauna a gaban akwatin television dinsu dan jin mai kuma zai ce masu?dan kuwa baki ɗaya mutunen yakin Zamfara a wuya suke akan wannan kiddneping din da ake masu a jaha, kiddnepers sun bi sun maida masu jaha a hirgitse sun hirgitsa masu jaha sun hana kowa zaman lafiya da kwanciyar hankali kullum cikin dauke dauken mutane ake da kashewa sun gaji da wannan rayuwar da suke yi a Zamfara..karfe hudu dai-dai aka fara gabatar da shirin kai tsaye da Alhaji Abubakar yace zai yi, numfasawa yayi yana cewa."Assalamu alaikum jama'an al'ummar wannan jaha tamu ta Zamfara ina maku sallama irin ta addinin musulunci da farko dai ina mai ƙara yi ma mutunen zulmi gaugauwa da kuma jajanta masu akan abinda akayi masu da kuma mutunen jahar nan tamu ina mai ƙara basu hakuri da su yi hakuri kuma su ƙara yi mana hakuri akan wannan halin da ake ciki a wannan jahar tamu muma abun yana matuƙar damunmu yana hanamu sukuni kuma muna maku albisir da cewa in shaa Allah da kuma yardar Allah zamuyi iyakar kokarinmu dan ganin mun kawo karshen kiddnepers da yardar Allah muna nan muna kokarin abunda muke bukata a wajenku shine ku ƙara hakuri ku kuma tayamu da addu'a Allah ya bamu nasarar kawo zaman lafiya da tsoro a wanann jahar tamu,sannan ina kira ga yan-sanda duk wanda suka kama da laifin kiddnep karda suce zasu wani kai shi station ayi wani tsugunne tsugunne kawai a kashe shi take na bada wannan datar take za'a kashe a kawo gawar haka ma informers suma hukuncin kisa ne ban yarda da kai su wani station ba kawai a kashe take anan zan dakata." Take mutunen jahar Zamfara suka fara saka ma His Excellency Alhaji Abubakar Mudi albarka saboda ba ƙaramin dadi suka ji ba da yace idan an kama a kashe take daman suma a ganinsu hakan ya dace da ayi amman da ance sai anje station to ɓata lokaci ne kafin a gama wani investigation anyi bell din kiddnep din wanann kenan.
YOU ARE READING
NAHIYA TA AREWA
General FictionThe Story of Nahiyata Arewa is the one that comprise the most important things such as Correction,Injustice,Betrayl and Revenge including Entertainment and Education, is a Falatable and testable story.