066

5 0 0
                                    

_*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*_

*NA*

_JAMEEY_

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*PAGE 66*

Murmushi dauke a saman yalwatacciyar fuskar shi mai tarin haiba da kwarjini yace."Baba ya amince ki koma aikin ki."kamar a mafarki haka Jamila takeji wani irin farin ciki ya lullube kasan zuciyar ta batasan sanda ta saki murna ba tsabar farin ciki take cewa."Alhamdulillah Allah nagode maka bansan da wane baki zan fara gode maka ba Allah ya saka maka da alkhairi tabbas ka cancan matsayi mafi girma a wajena."shima murmushin jin dadi ya sakar mata ba karamin farin ciki bane ya rufe shi yanda yaga masoyiyar tashi na farin ciki daga mata gira yayi yana cewa."kinfi komai a wajena Jamila kada kimanta ta silata kika rasa wannan aikin naki, dole nayi duk yanda zanyi domin kici gaba da aikin ki, kaunar da nike maki bazai bari in samu sukuni a raina ba matsawar zan ganki cikin matsala."wasa tafara da dogayen yatsunta tanajin dadaden kalaman sa masu sanyaya zuciya tace kallanshi tayi tana cewa."nayarda dakai Yayana tabbas kai mutumin kirki ne kuma kana da karamci."OMG kalaman ki sunfi man komai dadin sauraro musamman sanyayyar muryar ki a lokacin da take rero karatun alqur'ani mai girma nakan manta kaina."dariya kawai tayi har saida sautin muryanta ya fita, shima kallan ta yakeyi kamar ya samu television yake cewa."kinyi kyau ba karamin kyau hijab din nan yai maki ba."da gaske.?" jinjina mata kai yayi yana cewa."ki daina kokonto Jamila duk abinda zai fito daga bakina ki tabbata daga nan yake fitowa."ya ida maganar yana pointing heart din shi."gyaɗa kai tayi tana cewa."ina tareda kai saidai." Furzar da numfashi yayi yana cewa."me?kada kice kina kokonto akaina.?" Girgiza kai tayi tana cewa."Aaa bana son kana wannan al'adar ta  zugan matasa dayawan mutane zasuyi maka kallan  'dan daba ne."ajiyar zuciya ya shide a sirrance yace."yanzun haka kike man kallo.?"Girgiza kanta tayi tace."Aaa."good a da fa.?"haka nikeyi maka kallo."a hankali ya mike tsaye ya zuba hannun shi cikin aljihu yace."duk abinda zakiyi ki nemi yardar Allah da sannu al'umma zasu yarda dake saboda yardar Allah tafi ta kowa."Jinjina kai tayi mikewa yayi ya cigaba da cewa."zan wuceAllah yasa aci gaba da aiki cikin nasara."Amin nagode."ki kulaman da kanki."insha Allah, safe journey."thanks bye."da haka ya fita yana jin nishadi a cikin zuciyar shi yana fita yaransa suka bude mashi mota ya shiga."Jabir."yes my boss."gidan Alhaji Hadi."Dan damama Dila yayi kamar baiji abinda Umar din yace mashi ba yaci gaba da driving din shi, daukar wayar shi Umar yayi ya kira Salisu yana dauka yace."ka taho mani da Ubaidu ku iske ni gidan Alhaji Hadi."angama boss."cigaba da operating wayar shi yayi saidai kaf hankalin shi nakan Dila ya fahimci tun da yace ya kaishi gidan Alhaji Hadi hankalin shi ya'ki kwanciya."Ranka shidade, Jabir ya turo sa'ko yanzun nan."miya ce.?"cewar Muhsin dayake saukowa daga saman bene zuwa falor hannun shi dauke da cup yana sipping tea."yace yanzun haka mai gidan sa yana kan hanyar zuwa gidan Alhaji Hadi saidai bansan abinda zaije yi ba."take saida Muhsin ya saki cup din dake hannun shi take saida ya tarwatse saman tiles a forgice yace."ka fada mashi ya tabbatar duk abun da zasu tattauna anyi a gaban idon sa."angama Oga."turama Jabir sakon yayi kamar yanda mai gidan nasa ya bukata, karar sa'ko ya shigo daga wayar Dila ta glashing mota yake satar kallan Umar saidai cikin rashin sa'a idanuwan su suka hadu dana juna da sauri Dila ya cire nashi ido ya maida kan titi."Jabiru mikoman wayar ka."wani irin katsawa cikin Dila yayi kamar zaiyi zawo haka yaji ya kasa furta uffan."da kai nike."toh mai gida."jikin shi na rawa ya mikama Umar din wayar ga hasken notification tanayi kallan wayar kawai Umar yayi ya kauda kanshi gefe yana kallan window yace."anyi maka notification idan mun sauka ka duba, last warning da zaka dinga driving kana wasa da waya bana bukata understand.?"yes sir  zan kiyaye."hurry up"ok Sir."cigaba da zunkuda gudu yayi har ya isa kofar gidan Hadi already ansan da zuwan sa securities ne suka tarasu bayan Umar ya fito daga cikin motar daga shi har yaran nasa suka maye mashi baya already su Jigida sun rigasu isowa kasancewar daga cikin gari suka taho."Sannu da zuwa mai gida ya hanya.?"Alhmdulillahi Ubaidu nayi kewar ka hope baka da wata matsala.?"Aa babu."Jigida, Jigau ku jirani anan, kai Jabir ku biyoni kaida Deeni."take farin ciki ya lullube zuciyar Dila har saida ya gaza boye hakan a saman fuskar shi."ka fito lafiya mai gidana."cewar Jigida, d'aga mashi hannu kawai yayi suka wuce ciki har cikin katafaren falorn gida wanda ya gaji da tsaruwa da sauri Alhaji Hadi ya mike tsaye ya taro Umar a jikin sa yana."you are highly welcome my lion."thank you sir."have a sit."am appreciated."zama Diga yayi saman two seater Dila na tsaye daga bayan shi yasha uban suite a jikin shi kamar wani SS inda Ubaidu ke daga gefe."this is my brother."Umar yace yana nuna Ubaidu  da yatsantsa manuniya, cikin sakin fuska Alhaji Hadi ya kalli Ubaidu yace."dan samari ga kujera ka zauna mana minene sunan naka?"UBAIDUDDEEN"wow kace kanin naka sunan Jarumai ne dashi."murmushi Diga yayi yace."kwarai kuwa shidin gwarzone kuma jajirtacce."ina alfahari da kai Umaru."godiya nike mai gida." dan gyaran murya Alhaji Hadi yayi yace"da ganin yanayin ka kana cikin tarin farin ciki zanzo inji ingantaccen albishir daga gareka."wannan haka yake kasani saura kiris  girgije ya zubar da ruwa albarka zata sauka saman kasa abinci zai yawaita marayu zasuyi dariya yayin da makiya zasuyi kuka marar adadi daga karshe zuciya zata raunana wannan shine labarin dana zo maka dashi mai gida."Alhamdulillah tabbas wannan bakaramin albishir bane Umaru idan haka ya tabbata tabbas za'a samu iri mai kyau kuma mai usuli."hakane ranka shidade musamman idan wannan iri ya hadu da albarkar taki shikenan komai zaiji zam zam kamar yanda ake bukata."Allah yasa albarka ya gwada mana lokaci lafiya."Amin."suka hada baki wajen amsawa shida Ubaidu hakan yasa  Umar ya kalli Deeni duk da yanayin fuskar shi kadai zai shaida maka kwata kwata bai fahimci kalar yaren da sukeyi ba, musamman  Dila da bai iya gane komai ba, shiru ne ya sake biyowa baya sannan Umar yace."Ranka shidade na tsaya nayi nazari akan tayin da kukajima kunayi mani a matsayin ka na shugaban wannan jam'iya ta NPC ina so ka shaidawa jama'arka ni Umar Fatah Umar na zama cikakken 'da a cikin wannan Jam'iyar taku mai farin jini da sanin darajar talaka."wayar dake hannun Dila ta subuce kasa har saida suka kalle shi baki dayan su cikeda tuhuma."ka kula da kyau Jabir."tuba nike mai gida."sake kallan Umar yayi daga kallan da yakema Jabir yace."ka tabbata tayar motar ka mai inganci ce Umaru.?"kallan Jabir ya kumayi kallan dake nuna yana neman wani abu daga jikin shi yace."kwarai kuwa shiyasa nafi aminta da kafata ta dama"jinjina kai yayi yace."hakane yana da kyau lokaci zuwa lokaci ka dinga yi mata service kafin ka hauta."Jabir kaji abinda mai gidana yace fatan zaka kula."zan kiyaye."yace saidai ba kadan kanshi ya daure mashi ba ya rasa inda zancen su ya dosa."yau bansan kalar farin cikin da nikeji ba Umaru a matsayina na uban jam'iya ya zama dole na tara 'yan Jaridu domin su shaida kalar nasara da babban cigaban da wannan Jam'iyar tamu tayi sannan zaka gana da mai girma gwamna dole ya jinjina ma namijin kokarin ka."godiya marar iyaka Umar na godiya."Allah yataimake ka, ina mai farin cikin wannan karamci da kayima Yayana Allah yasa kafi haka"Amin Ubaiduddeen kaima ai tafiyar mu daya ce dakai."kwarai kuwa inda Yayana yake nima ina nan."murmushi Umar yayi yana jin Ubaidu har ranshi, cikin kankanin lokaci aka fara gabatar masu da kayan makulashe iri iri kamar za'ayi wani party akaci aka sha daga bisani sukayi sallama da shugaban Jam'iya har gaban mota saida ya rakasu da kanshi ya budewa Umar kofa ya shiga sannan ya rufe suka tafi.

★★★★

Tsaye yake bakin morrow yana gyara neck tie din shi yayin da yake daurama tsintsiyar hannun shi agogon Rolex  sai daukar ido takeyi a hankali yake shafama sumar kanshi mai sai daukar ido takeyi yayin da kunnen shi ke makale da headphone  yana waya saidai fuskar sa ba yabo babu fallasa yace."No Abbas na shiga busy da yawa ni kaina nasan ina da sukaci dayawa."you should change tunda har kasan you have a problem."I will try, still itama da nata laifin inaga."haka kake gani Kaidai kafara duba naka before kagano nata, I will tell you this since." Taɓe baki Sanda yayi yana cewa."naji idan na dawo daga wani program zan wuto ta gidan ka hope kana available.?"ko saboda kai na fasa fita."okay later."da haka ya gama wayar yana gama sanya takalmansa ya fita kai tsaye sashen mahaifiyar sa yaima tsinke ya iske zaune tana kallan TV gefen ta ya zauna cikin tarin ladabi da biyayya yace."Mamma ina kwana.?"yauwa Umaru har an fito?"wallahi harna kusa makarama."Kaidai baka da wani lokaci sai na aikin ka ina kafito aiki ina zaka aiki haba Sanda ka hutawa kanka wannan walahar haka nan mana."murmushi yayi yace."komai yana da nasa lokacin zan huta ai."haba ina wani hutu aikin nan duk ya maida mani dakai baya kwanaki kamar abun arziki kace min zakayi aure girma girma da arziki na tada magabatanka suka tafi ashe duk labarine har yau baka kuma cewa dani komai ba haba."ba haka bane Mamma yarinyar ce tafiye nuna isa dayawa, nifa bana son haka mata sun fiye sa mutun cikin damuwa."lallai kam Umaru dama ba auren kake son yi ba ai dole ta nuna maka isa kaifa ke nema a wajen ta wai nikam bazaka kama kasuwa ba ka aje wannan aikin 'dan sandan nan ba wallahi harda shi yasa kaki kayi auren nan shekarunka ke ja fa cikin arba'in biyu ke babu."Mamma kiyiman addu'a mana tunda mahaifin yarinyar nan ya yarje man kisa aranki zan  aure ta."aaa bata anan taya yarinya zata yarda ta soka bayan baka da lokacinta aikin ka kawai kasani fa muma kanmu muna iya sati ukku bamu saka a idon mu yau baka Germany gobe baka England  jibi kana China yoh haka ake rayuwa iyeh Umaru? ita fa 'ya mace kulawa take bukata da tattashi ka tarairayeta kamar kwai sannan zaka samu zuciyar ta kudi basu magani kulawa da damuwar ta shine zaisa ta soka ba tarin mukami ba ko kuma tarin dukiya ba, dole ne ka gyara Umaru indai kana so kafin na mutu inga jikokina haba."ajiyar zuciya ya shide cikin tarin lallama da rarrashi yace."zan gyara Mamma kuma insha Allah soon zanyi auren nan idan hakan zai faran ta maki."ba damuwa Allah ya ida nufi."Amin Mamma na."kiran wayan sa aka kumayi saidai bai d'aga ba ganin shima kiran daga wajen aikin sane sarai tana ganin ya maida wayar silent tace."nasan dai akan aiki ne tashi kaje Allah yabada abinda ake nema ya tsareka daga sharrin zamani."yaji dadin addu'ar ta kamar jira ya mike tsaye yace."nagode maki Mamma na, idan auta ta dawo kice ta Kirani a waya."toh shikenan adawo lafiya."Allah yasa."yana fita guards dinsa suka bude mashi mota ya shiga suka fita daga gidan.

Share pls

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now