027

7 1 0
                                    

_*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*_

*NA*

_JAMEEY_

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*PAGE 27*

Kowa ya gama hallara bakaji motsin kowa saidai zukatan su cike suke da fargaba,ba karamin abu kesa Umar ya tara yaransa ba a lokaci ɗaya kuma a filin da bamai fatan kiran Umar ya riske su wajen sunsan ba lafiya,kowa ka kalla a cikinsu yana cikin tashin hankali da tarin damuwa sai dai kowa da irin tashin hankalin da yake cikinsu wasu na ɓatan Jamila ne wasu kuma tashin hankalinsu karda allura ta tono garma dan mudun Diga ya gane su din masu leƙen asiri ne  bazasu kwana a duniya ba,zaune yake yana nazarta kowa gyaran muryar da yayi ya tabbatar masu da isowar shi kasancewar kowa ya sauke kan shi kasa kamar baisan dasu wajen ba ya dinga binsu ɗaya bayan daya da ido yana nazarta su,har tsawon minti goma kafin ya fara magana a nutse cike da kamewa duk da haka muryar shi kadai ya sanarmasu damuwar da uban gidan nasu ya shiga."An sace ta,bata gidan nan duk kuna aikin mi.?"Shiru ya karade wajen ba wanda yace uffan saima sake soke kai da sukayi kasa, firzar da iskan yayi yana cigaba da cewa."Wannan shikenuna cewa da dan gari kanci gari ni za'aima zamba cikin amimci ko.?"Baki ɗayan su suka maida kallan su kan Diga jin kalaman da yakeyi."Within one hour duk wanda yasan yanada sa hannu ga batan Jamila ya hanzarta maido min da ita tun kan ranar dana sani ta tsaya,kusan bani yafiya kuma bana mance ranar daukar fansa."Yana gama fadar haka ya juyaya koma apartment dinshi bayan ya gargadi kada kowa ya shigo side din shi ranar yaran Umar sun shiga damuwar marar misaltuwa neman Jamila suka bazama cikin katan gidan lungu da sako amman ba alamunta Jigida da Jigau ba irin bin cikar da basuyima yaran su ba amman kowa yace bai ganta ba,haka kowa yaci gaba da zama cikin zullumi.

☆☆☆☆

Faruq ne zaune a cikin Garden dake shake da kayan alatu na more rayuwar yau da kullum,ya harde kafarsa yana aikin kallan wayarsa ko kaftawa baiyi,kana ganin sa kasan abinda yake dubawa a jikin wayar yanada matukar mahimmanci a gare shi duk abin nan da Faruq keyi baisan Khalid na tsaye saman kan shi ba yana mamakin duniyar da abokin nashi ya lula da har baisan da zuwan sa wajen ba."Yawan tunani na haddasa cuta kwara kadawo hayyacinka ka daina jiran gawon shanu a inda ba'asan kanayi ba." sai lokacin Faruq ya maida kallan sa kan Khalid dayaja chair ya zauna yana facing dinsa sanyayyar ajiyar zuciya ya shide a sirrance yace."ashe damuwa ta zata zama taka,miya sauya ka har haka.?"fuskar shi dauke da murmushi yayi maganar dan ba karamin dadin ganin Khalid yayiba atare dashi,sanin mahimmancin sa agare shi."Kana tunanin damuwar ka zata dameni.?" Jinjinawa Faruq yayi yana cewa."Hmm Khalid miyasa zaka dauki zafi kasan bazan juri fushin ka agareni ba." Numfasawa Khalid yayi yana cewa."Ya isa Faruq ba wannan ya kawoni wajen ka ba,duk abinda ka zaba ya rage naka."Da kallan mamaki Faruq yake bin Khalid ganin yanda ga sauya a lokaci  ɗaya."ka daina wahalar da yar mutane tunda ita kasan tanayi ba wai haukan banza takeyi ba."Ban fahimce ka ba."Cike da tsarewa yai maganar."Ramlat ka daina wulakanta ta ya isa  ita macece mai daraja,ka aje girman kai ka bata kulawa."murmushi yayi yana mamakin yanda Khalid ke tada jijiyoyin wuya akan Ramlat."Kaima kadaina goyon bayana ni ba wanda zai considering tawa damuwar kenan.?" Firzar da naunauyen ajiyar zuciya Khalid yayi yana cewa."Muna da aikin yi,ba zamu zauna muna damuwa a inda ba'asan munayi ba kowa ba kalan ka bane." Murmushi Faruq ya sakar ma Khalid yana cewa."Khalid kaji tausayi na mana komi Ramlat na amince zan aure ta miyayi saura?maimakon ka taimakeni na shigar da nawa kudurin gun Dady shine zaka dinga kware mani baya."Enough Faruq ba zan shiga wannan shirgin naka ba,yarinyar nan fa batasan kanayi ba,sanin waye kai bashi ke nuna zata soka dan nasabar kaba,shi so ba ruwan sa da nasaba,dan haka ka tsaya inda ake kaunarka miye laifin Ramlat kana dagula mata lissafi." Dan shiru Faruq yayi yana nazarin maganar Khalid can ya numfasa yana cewa."Naji sai dai kasani inada yakinin Jamila zata soni badan nasaba ta ba,saboda....katseshi Khalid yayi da cewa."saboda me.?"Dani ta dace an halicce ta dan ta zama uwar ya'yana ina kaunar ta,kuma inada yakinin zata soni kamar yanda nike son ta."Kallan baka da aikin yi Khalid kema Faruq yace."yarinya da aka batar da ita bata ba alamun ta shine kake tada jijiyoyin wuya akan ta?kaga ka kama dahir tunda wuri."Kai ke ganin haka kasani ko zan rasa komai nawa saina dawo da Jamila hannun iyayen ta sannan zata zama mallakina komai daren dadewa."Matsalar ka,kadaina daukar kai kana ganin kafi kowa kadinga wulakanta Ramlat itadin mai daraja ce."Uhmm."Faruq ya furta yana rufe idanin sa ahankali."Idan kayi lokacina kayi amfani da abinda na faɗa maka idan bakayi ba ya rage ruwan ka"Mikewa yayi yai tafiyar shi sai a lokacin Faruq ya bude idanuwan sa ya raka bayan sa da kallo."yanzun bakaji dani Khalid baka damu da damuwa taba wannan shine amincin."?Sake maida idanin sa yai ya rufe kamar mai bacci.

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now