_*🏝️NAHIYATA AREWA🐄*_
*NA*
_JAMEEY_
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
*PAGE 39*
An daura auren Faruq da Ramlat kamar yanda addini ya tanada dubban mutane suka shaida daurin auren a cikin garin Zaria dake kalkashin Jihar Kaduna a katan masalacin Juma'ar dake unguwar yayan mahaifin Ramlat,Jama'a sun taru manyan mutane da Sarakuna Jami'an tsaro da sauran manyan mutane daga kowane sassa na abokan Faruq da sauran yan uwa da abokan arziki tinda aka gama daurin auren ake daukar pictures na girma banda Videotin da akeyi a gefe guda kuma yan Jarida ne keta nasu bikin na daukar rahotanni..Faruq ne cikin dakakkiyar shaddar shi white sai daukar ido takeyi shida abokan sa a ciki kuwa harda Umar Sanda shima fararen kaya yasha sun yimashi kyau sosai daga wajen daurin auren wani katan gida suka nufa cikin gidajen abokan su sukayi reception gwanin burgewa kowa yaci yasha shiko Ango fuskar shi sake take yanata hudda da Jama'a ana fira irin ta abokai,Sanda dake gefen Faruq shida Khalid sun hadema Faruq kai sai zolayar sa sukeyi."gaskia ne ango ka iya zabe Allah yasa mudawo suna."cewar Sanda.Dariya Khalid ya fashe da ita yana cewa."gaya mashi amman da yazo yana son maso wani koshin wahala inda ba'asan kana yi....Faruq ya katse Khalid ta hanyar cewa."am My man ya maganar yarinyar nan kun sameta kuwa.?"Dan shiru Umar yayi kamar mai nazarin maganar Khalid can kuma ya numfasa yana cewa."yeah last monday yau kwana biyu kenan."Murmushi ya kubcema Faruq yana cewa."Really.?" Ɗaga kai Sanda kawai yayi yana latsa waya yace."Yes offcourse."Amman nawa aka bada kudin fansa.?"Dan kishingidawa Sanda yayi yace."basu bukaci komai ba."with suprised a saman fuskar shi yace."Bangane ba miye anfani daukar ta.?" Murmusawa Sanda yayi yana cewa."I don't kasan tunda nakaita gida ban koma nazauna da ita ba,amman gobe zanyi interview da ita."Okay i promise akan ni zan bada kudin fansar ta amman na tsorata da basu bukaci komai ba I think da wata akasa." Cewar Faruq cike da mamakin yanda akayi ba'a tambayi kudin fansa ba aka saki Jamila,jinjina kai Sanda yayi yana cewa."Gaskia kam."Shiru ya karade wajen kowa da abinda yake sakawa a ransa karfe ukku Umar yatafi shida Jama'ar sa...A wajen amarya kuwa ansha kyau karfe hudu daidai aka dauketa zuwa dakin ta dake cikin Wonder line Estate nan Faruq yasa Ramlat,gida yayi kyau komai yaji zauzau masha Allah.wannan kenan.
_NEXT DAY_
Hankalin Umar ya kwanta ganin Jamila tadawo yanzun ba abinda yarage mashi irin ya fallasa mata sirrin sa Karfe shabiyun rana ya fito daga side dinshi zuwa side din mahaifiyar shi akayi sa'a yana shiga ya isketa zaune a falor tana kallan New sannan hannunta rike da Jarida tana dubawa sallamarsa ta amsa ya samu kujera ya zauna."Her Exellency barka da gida."yawwa."tace tana maida kanta kan Jarida."Ashe abakiyar aikin ka tadawo.?" Ƙasa da kanshi Umar Y yayi yana cewa."Eh Momy."cire glashin idonta tayi tace."well naga Journal and tv channels abinda ake nunawa kenan,abin nan nabani mamaki kamar ita aka fara daukewa."Murmushi yayi yace."saboda tana yar jarida inaga." Taɓe baki Hajia Kubrah tayi tana cewa."Uhmm." Dan shiru Umar yayi can ya gyara zamanshi yana cewa."Momy ina tsaraban bikina."ya tambaya da sifar zolaya,Murmushi tayi tasan raharsa ce ta motsa."tana nan na aje maka."thank you Momu na."aje Jaridar tayi ta maida hankalin ta kanshi tace."Daganin ka akwai magana mike faruwa?nasan zurfin cikin ka."ajiyar zuciya ya shide a sirrince yace."Momy jiya bakya nan na dauko Jummala amman..."what ka dauko ta fa kace?miyasa bazaka bari indawo ba.?" Dan shiru yayi yana kallonta ganin kallon kai nike saurare da take mashi yasa shi numfasawa yace."Sorry Momyna dana ga kinsan da zancen shine kawai na dauko ta." Taɓe baki tayi tana cewa.Okay,hope zata zauna BQ ne ba cikin gida ba.?"Shiru yayi baice komai ba."dakai nike magana fa." Numfasawa yayi yana cewa."No Momy ina laifin ta zauna kusa da Hunaisa da Rumaisa." Zaro ido waje Hajia Kubrah tayi tana cewa."wajen ya'yana kaima kasan Hunaisa batasan hayaniya kada kamanta yarinyar nan da kake zancen akai she's a savent girl." Kallon mahaifiyarshi kawai yake yana mamakin yanda ta chanza take gudun tallakawa bayan da ba haka Momynshi take ba komai ya chanzata haka?har kullum yana mamakin yanda Hajia Kubrah Yusuf Umar ta chanza hali daga hali mai kyau zuwa wani na daban dan shi har a zuciyarshi yana ma zargin ba ita ta saka aka dauke Jamila ba?duba da irin tsanar da tayi mata,kwantar da kanshi yayi cikin son fahimtar da ita yake cewa."Ummi koda na sati biyu ne pls."Okay i have a meeting for now kasan siyasa ta kunno kai ana shirin fara Primary Election yanzun."Allah yaimana zabin kwarai."yace a sanyaye."mu kenan ai,ko mu bana kwaran bane.?" Dariya yayi yana kama baki yana cewa."Ba haka nike nufi ba Momy addu'a kawai nayi."Uhmm."tace tana mikewa."And then gobe aftar 9 tazo inasan ganin ta."insha Allah."Nan tabar shi ya cigaba da kallan news ta shige daki.
YOU ARE READING
NAHIYA TA AREWA
General FictionThe Story of Nahiyata Arewa is the one that comprise the most important things such as Correction,Injustice,Betrayl and Revenge including Entertainment and Education, is a Falatable and testable story.