_*🏝️NAHIYATA AREWA🐄*_
*NA*
_JAMEEY_
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
*PAGE 83*
Rungume Jummala Hajja tayi tana cewa."Oyoyo oyoyo ƴata Khadija sannu da zuwa sannu kinji yar'albarka ga waje nan zauna."Murmushi Jummala ta saki tana samun waje zata zauna a kasa tarota Hajja tayi tana cewa."Ina taya zaki zauna ƙasa keda gidanku? a'a maza ki hau saman kujera kina fama da wannan lalurar zaki zauna ƙasa salon ki wahalar da kanki."Murmushi Jummala ta saki tana kallon Hajja tana cewa."Ai ba wata matsala a ƙasan ma ya isa."Girgiza kai Hajja tayi tana cewa."Na hana daga yau dan ni ba ruwana idan ina saman kujera kema hau kiyi zamanki ba wani abu bane."Ɗaga kai tayi tana zama a saman kamar yanda Hajja ta bata umarni shima Umar zama yayi Hajja ma ta zauna tana cewa."Hafsat."Shigo mai aikin Hajja Hafsat tayi tana duƙawa tace."Gani Hajja." Nuna mata kayan Jummala Hajja tayi tana cewa." Kwashe wa'anan kayan ki kaisu a dakin dake kusa da nawa ki jera mata kayan a cikin wardrobe ki shiryasu suyi kyau sosai,ki gyara dakin dai baki ɗaya." Tashi tayi tana cewa."Toh Hajja."numfasawa Hajja tayi tana cewa."Rabi a kawo ma Khadija ruwa da abinci mana sai na ce a kawo yau ga ikon Allah."Kallon Hajja Umar yayi yana cewa."Wato Hajja ba tani kike ba ko?ta Khadija kawai kike ba ko mijin ya hanya gaskiya tun yau zan fara fushi ana neman anshe man mata."Kama baki Hajja tayi tana kallon shi can tace."To Umar ya hanya? Shikenan dai ko ai ban lura da kai ba shiyasa ayi hakuri mijin wake yadda miji in banda abunka."Hajja kenan wato ma baki lura dani ba ko?shikenan bakomai ni zan tafi daman sauri nike zanje wajen aiki sai na dawo ko Khadija." Maida kanta ƙasa Jummula tayi tana cewa."To Allah ya tsare ya bada sa'a."Da Amin ya ansa ya tafi cike da farinciki ganin yanda Hajja ta anshi Jummala sai rawar jiki take a kanta daman gidan Hajja ne karshen hope dinshi dan shi bai san maida yarinyar kauye saboda ya tabbata ba zata taɓa jindadin zaman kauyen ba aiki za'a dinga saka ta ga ciki da yake haihuwa ko yau ko gobe..kallon Jummala Hajja tayi tana cewa."Khadija."Ɗagowa Jummala tayi tana cewa."Na'am Hajja."Numfasawa Hajja tayi tana cewa."Inason ki saki jikinki dani nan ma gidanku ne Khadija zaki kuma haihu lafiya a cikin amincin Allah ki daina saka ma kanki damuwa kuma komai kike so bance kice zakiyi da kanki kisa Hafsa ko Rabi suyi maki suna masu aikin gidan kinji Khadija.?"Ɗaga kai Jummala tayi tana cewa."To Shikenan Hajja Nagode sosai da karanci Allah ya ƙara lafiya da daukaka."Amin Khadija ai bakomai ɗa ai na kowa ne ita wancan giyar mulki ce ke kwasarta shiyasa tayi maki haka,amman da kafin su samu mulki ba haka Kubrah take mutunniyar kirki ce ya halinta ya halin mijinta,sai ki maida komai ba komai bane kinji dan watarana sai labari."Murmushi ta sakar ma Hajja tana cewa."Bakomai Hajja daman ban riƙe ta a rai ba wanda ya riƙe ka ai ba ƙaramin taimako yayi maka ba a rayuwa nagode kwarai."Abinci Jummala ta zuba taci sosai daman yunwa take ji bayan ta gama Hajja da kanta ta kaita dakinta tana cewa."Ga daki nan idan kuma yayi maki girma baki iya zama ke ɗaya zaki iya dawowa nawa dakin."A'a Hajja wannan ma yayi."Kin tabbata Khadija.?"Ɗaga kai tayi tana cewa."Eh Allah Hajja."shikeban ai tunda yayi maki shiga kiyi wanka ki kwanta ki huta ko?anjima munyi fira."Da Toh gami da godiya Jummala tayi ma Hajja tana shiga ɗakin tsaye tayi tana kallon girman dakin da kuma haduwarshi kamar dakin Rumaisa na gidan gwamnati dan kuwa makeken gadone sai wata kujera ɗaya wanda zaka shinfida dan kawai hutawa idan kwanciyar gadon ta isheka sai kwatuwar wardrobe da mirror da shoerak da babban stool da take a wajen mirror sai kuma tv da ke aiki ita ɗaya a cikin dakin ga sanyin Ac da kuma kamshin conditioner da suke ratsa mutun lokaci guda a saman mirror kuwa jere yake birjik da kayan kamshi sunfi iri nawa tun daga kan kwalarca da humrah da perfume da spray da sure da roll da mayamayai iri iri tun daga kan cream da lotion da vasilene bangaren su hoda kuwa ba'a magana ga janbaki nan iri-iri ga lipsgloss nan iri-iri ga kuma wani katon kit nan daga gefe mamakin kayan saman mirror kawai take tana jinjina ma arzikinsu sauke ajiyar zuciya tayi jin ta fara jin bacci ta shiga toilet da yake zaman da tayi a gidan su Umar Y ta iya amfani da duk wasu kayan amfani na toilet bata ba kanta wahala ba ta fara using dasu danyin wanka a tsanake tayi wankanta da soap masu dadin kamshi da tsada banda gel din da suke baje a toilet different flavors sai kuma shamfo daga gefe kuma ga handdry nan gefe numfasawa tayi tana dauro sabon showel ta fito zama tayi saman stool din ta tsane farar fatarta ta murja lotion kawai ta samu wata doguwar riga marar nauyi ta saka tana fesa turare ta murza Humrah ta kwanta ko addu'a bata gama ba bacci yayi gaba da ita.
YOU ARE READING
NAHIYA TA AREWA
General FictionThe Story of Nahiyata Arewa is the one that comprise the most important things such as Correction,Injustice,Betrayl and Revenge including Entertainment and Education, is a Falatable and testable story.