_*🏝️NAHIYATA AREWA🐄*_
*NA*
_JAMEEY_
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
*PAGE 37*
Wayarsa dake ta faman ringing saman dressing mirrow harta tsinke ba ba'a ɗaga ba,alamun bai kusa da wayar maida kallansa yayi saman fuskarta da dake dauke da dannuri ba yabo ba fallasa yace."bana maimaita kira,kinga yau ta tashi kenan sai wani jikon."bakaramin faduwar gabane ya riski Jamila ba jin abinda Umar yace,tasan bazai sauya magana ba girgiza mashi kai tayi cikin sanyin da jikinta yayi tace."Kataimaka mani zan iya komawa gida da kaina kaji tausayina."girgiza kafarsa yayi a tsanake yace."I think nagaya maki zaki koma gida bisa ka'ida so kike inbarki ki koma ke kadai kome kike nufi.?" Jinjina mashi kai tayi tana kasa da kanta gami da wasa da yatsun hannunta tana cewa."Eh."murmushi ya saki wanda ba lallai kagane yayi shi ba,kallanta yayi yana cewa."zaki iya tafiya." Narai-narai tayi da idanuwa tana niyar sakar mashi kuka daga mata hannu yayi yana cewa."kina son saman ciwon kai ne.?" Girgiza kai kawai tayi bata ce komai ba firzar da naunauyen numfashi yayi yana cewa."Okay I said you can go Okay.?" Juyawa kawai tayi ta bar mashi dakin zuciyarta ba dadi,da kallo Diga ya bita yana sakin sahihin murmushi tabbas ya yarda yana son yarinyar kuma da ita yake fatan yayi rayuwa ta har abada, lumshe ido yayi ya buɗe a take yana shafa gefen sajenshin gami da cire kaya ya faɗa bathroom dan yin wanka, wanka yake yana sakin Murmushi dan zuciyarshi cike take da tunaninta yana son komai nata yana fitowa yafara tsane jikinsa da karamin towel mai taushi a hankali yake tafiya cikin natsuwa data zame masa ruwan jiki,kai tsaye dressing mirrow ya isa,ya janyo stole ya zauna daukar cream yayi mai kamshi yafara shafama jikinshi yana gama shafaman ya mike tareda daukar wayar shi dake faman kawo haske alamun burus yayi da kiran har sai da ya gama duk abinda yake sannan ya dauki laptop din shi ya fito babban parlonshi da ya ƙayatu da kayan more rayuwa zama yayi yana buɗe laptop ya fara aikin da ya dace dan kuwa shi Umar Diga kullum cikin aiki yake baya zaman banza bai son kuma yaga matashi yana zaman banza a rayuwarshi,ya yarda komai nashi ya chanza ba iyakar shi ba har yaranshi yana son ya chanzasu daga rayuwar fat suke ta bangar siyasa su koma rayuwa mai inganci ta yanci duk da daman su tasu bangar ba irin ta ƙananun kwari bace suna banga a cikin ilimi da waye basu yi ma kowa rauni idan sun tabaka kwagilarka aka basu kuma suna karatu ba wanda bai shiga University ba duk wanda yake yaron Diga kuma shi yake daukar nauyin karatun zai matsa sai anyi degree master kuwa idan kaine kake da ra'ayin cigaba kayi mashi magana zai yi sponsor dinka har ka gama kuma kowa da irin sana'ar zahiri da yake gudanar gujema zaman banza damuwarshi ɗaya a yanzun shine Ubaidu yana son rayuwar yaron da yaranshi ta chanza ya zama mutu taya?taya zai iya sauya Uban daba Ubaidu?yana son yaron har cikin ranshi kwazonshi da jarumtarshi yasa yan siyasa suka riƙe shi tamau sun hana kowa ya rabeshi, amman zai san yanda zai yi ya samu yaga ya maida Jamila wajen iyayenta farkon abinda zaiyi shine chanza Uban daba ko yana so ko baya so.
☆☆☆☆
Kwanan Sanda biyar da dawowa Katsina yaje Niger ya ƙara bincikar case din kisan CP ADAM kuma Alhmdulh ana dan samun cigaba duk da wanda sukayi kisan ba kananun kwari bane sai da suka shirya kafin suka aiwatar shi damuwarshi ma a yanzun ta ina zai fara neman Jamila tabbas Jamila ba normal kidinafin akayi mata ba kuma babban abinda yake daure mashi kai dawowar Jamila daga Niger batayi wata biyu ba aka ɗauketa kuma ai har dakatar da ita aiki akayi a hikima station saboda ɓacewar joter baiyanar fingerprint din Cp Ahmad da sati biyu aka dauke Jamila mai hakan ke nufi? Tabbas akwai lauje a cikin nadi yasan waye Cp Ahmad yasan hatsabibancinshi balle ma ta silar Jamila ya kusa samun matsala a wajen aiki ba dan yana da sama ba da tuni yana prison dan a cigaba da bincikarshi akan kisan CP ADAM idan kuma har haka ne Cp Ahmad yana da saka hannu a ɓataman Jamila,to wa zai saka yai mashi aikin? Murmushi Sanda ya saki yana jinjina kai yana cewa."DIGA." Wani murmushin ya kuma saki yana cewa."Tabbas ba wanda za'a saka ya dauke Jamila ta ɓace ɓat idan ba Diga ba dan hatsabibancin Diga ya wuce duk inda mutun yake tunani ina ya kai ta? Tabbas Dagi ne suspect dinmu akan dauke Jamila yana ina yanzun? Yana Niger ko Katsina.?" Tambayar da yayi ma kanshi a zahire kenan last ganin da yayi ma Diga a Katsina ne to mai ya kawo Diga Katsina?duk da asalin Umar Diga dan jahar Katsina ne amman yana iya shafe shekaru bai kwana a cikin Katsina ba dan bai da case da ita yafi zaman Niger, numfasawa yayi yana cewa."Tabbas da wata a kasa Diga koni ko kai mudun suspect dina ya zama gaskiya kaine ka ɗauke Jamila anan zaka san true colar dina,anan zaka san wanene Umar Sanda." Ringing wayarshi ta maidoshi a duniyar da ya lula kallon wayar ganin new number ce yasa taɓe baki yana ajiyewa da bai cikin mood din da zai dauki wata waya,tashi yayi ya fita daga room din ko zai dan sha iskan waje yaji saukin zafin da zuciyarshi take mashi...Zaune ya iske mahaifiyarsa,tana karatun alqur'ani mai girma,samun waje yayi ya zauna gefen ta,yana danna wayar sa,notification ya shiga ya dailing number dayaga ankira shi,ringing tafara har ya fiddaa rai za'a dauka sai kuma aka ɗaga daga."Jami'in tsaro Umar Sanda barka da warhaka."Murmushi ya kawata fuskarshi kamar suna ganin junan su yace."Yawwa,wake magana."shu'umin Murmushi ya saki yana mai fadin."Ba abin mamaki bane dan baka gane mai magana ba,saboda hakan baida wani amfani agareni, amman abinda nake tafe dashi nasan zai maka amfani."mikewa Sanda yayi ya fita compound din gidan,cikin garden ya shiga yaja sofa ya zauna yana cize kasan lip dinshi yana cewa."Diga kenan atunaninka muryarka zataimin alayi fadi bukatar ka."jinjina kai yayi yana yaba basira irin ta Umar Sanda musamman yanda ya kware da lakaitar muryar dan adam matukar yataba jin muryar ka,ko inane idan kayi magana zai gane ka ɗage kafaɗa Diga yayi kamar Sanda yana kallanshi yace."zinariyar daka jima kana bata dare da rana wajen neman ta,zaka iya samun ta idan kana bukata."Da sauri Umar ya mike yana cewa."mikake nufi.?" Murmushin Diga ya saki kamar Sanda yana ganinshi cike da izza da gadara Diga yace."harta gama maku amfani kenan.... Dakatar da shi Sanda yayi cikin zafi da hayagaga kamar suna gaban juna yake cewa.keep quite zan iya halaka ka,matsawar kaima yarinyar nan wani abu."cikin kankanin lokacin bugun numfashi Sanda yafara sauyawa,yasan hatsabibancin Umar.
YOU ARE READING
NAHIYA TA AREWA
General FictionThe Story of Nahiyata Arewa is the one that comprise the most important things such as Correction,Injustice,Betrayl and Revenge including Entertainment and Education, is a Falatable and testable story.