_*🏝️NAHIYATA AREWA🐄*_
*NA*
_JAMEEY_
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
*PAGE 35*
Tunda Alhaji Ma'azu yabar office din Sanda bai sake zaune ba balle tsaye dan ba inda bai buga ba dan ganin yayi bailin din ɗan sa da ake a hannun Sanda amman duk wata hanya da zai bi Sanda ya rufe ta gashi shine aka fiddo a matsayin dan takarar gwamna na jami'ar DNP,ba shi ɗaya ba duk wanda yake a jami'ar DNP hankalinsu a tashe yake akan case din gashi basu keda gwamnatin ba balle su murkushe case din take dole sai sunbi a sannu kuma ta kalkashin kasa dan karda abokan hamayya suji halin da ake ciki su aiko masu yan jarida a watsa case din,dan al'ummar jahar Katsina suna jin halin da ake ciki ba zasu taɓa zabarsu ba,yanda suke ganin alamun kamar mulkin zai dawo hannunsu duba da tallaucin da rashin tsoron da ake fama dashi a jahar ya shafi siyasar su Alhaji Yusuf Umar ba zama laila ya maimaita ba duba da tallakawa a wuya suke kiris suke jira dan kawo chaji,zagaye babban parlonshi yake yana cizon hannu can ya numfasa yana cewa."Ya tozartani yaci mani zarafi wannan mutumin so yake ya keta rigar mutunci na."Alhaji Ma'azu yayi maganar a fusace, furzar da numfashi mai zafi Alhaji Sale yayi shima cike da damuwar halin da Cp Sanda yake kokarin jefa su yake cewa."Ranka shidade yanzun ya zamuyi da wannan bauɗaɗɗan mutumin ko a shirya mashi kudade masu nauyi akai masa? Dan mudun ba kudi aka sakar mashi ba keta mana rigar siyasa zai yi." Murmushi mai ciwo Alhaji Ma'azu yayi yana girgiza ma abokin nashi kai yana cewa."Bai karbar cin hanci da rashawa,wlh akan Hafiz ba abinda bazan iyaba dan ya wulakanta dan talaka har wani abune zaisa a kama mani ɗana dan yaci zarafina,ni na lura harda adawa yasa CP Sanda ya rike man ɗa fa." Numfasawa Alhaji Sale yayi yana cewa."idan kuwa har bai ansa kudi yana bukatar kuwa mu bi mashi ta bayan gida dan ya zama dole a saki Hafiz ba za'a barshi a wajen yan-sanda ba kamar Hafiz yafi karfin aci ko second talatin yayi a hannun police." Jinjina kai yayi yana cewa." Haka ne kam tunda har haka ne kuma haka shi Cp Sanda ya zaba ai aiki sai ya koma a hannun Buba ko.?" Gyaɗa kai Buba yayi yana cewa."Umurnin ka nike jira Mai gida."wani shu'umin murmushi ya saki yace."Buba inason kasa Sanda ya shiga ukku inason ahada mashi gadar zaren da zaisa ya tsani aikin dayake gadara dashi,inason kowa sai ya yarda cewa shi munafuki ne ba aikin Allah yake ba takansa kawai yakeyi." Dariya Buba ya fashe da ita yana cewa. "Angama mai gida za'ayi komai cikin kankanin lokaci." Jinjina kai Alhaji Ma'azu yayi yana cewa."ina sauraron ka."Sallamarsu yayi yanata tufka da warwara ba abinda yake so sai yaga bayan Sanda tunda yaki yimashi alfarma yana neman fallasa shi yaketa rigar mulkin sa tabbas sai yaga bayan Umar.
☆☆☆☆
Shigarshi keda wuya ya iske Buba zaune cikin garden yana shan fruit ga waya makale a kunnen sa yana sheka dariya da alama wayar tai masa dadi ainun saukar marin da Umar ya watsama Buba ne tadawo dashi hayyacin shi,a kidime ya saki wayar yana shafa kuncin shi,kafin ya saki bangaren haggun da ya mara ya sake daura masa wani sabon marin saida Diga yaima Buba marika ukku kyawawa sannan ya daura kafar sa saman hannun sofar da yake zaune akai yace."kaci sa'a ba abinda yasame ta kaci sa'a digon jini ba sauka daga jikin taba!kaci sa'a mutuncin ta bai mata gargada ba!ka gode Allah UMAR bai cimma mugun kudurin kaba tabbas yauda saika bakunci Kiyama azzalumi ka gayama iyayen gidan naka,nayi masu rata,sannan ina baka albishir karen baren dake maka hidima nakara mashi mako biyu ya nemi sa'a."Galele Buba yayi yana kallan Umar hannun sa rike da kuncin sa yana shafawa,ga wani irin kunya data gama dirar masa jin yanda fitsari ke sauka a cikin wandon sa agaban idon yaran sa,amman ba wanda yai yunkurin wani abu har Umar yagama ci masa zarafi,karar kofar da yaji saida takara kadawa Buba yan ciki tsabar razana jiki mace ya mike yafada daki yana buga kofa yaje yadawo haka ya dingayi ya rasa mike masa dadi,miyasa Umar ya zama dodon su,miyasa gaba zata shiga a inda akafi karfin su....wayar sa ta dauki ruru da kallo yabi screen din Mai gida ya bayyyana."Ranka shidade."Buba yai magana a sanyaye."lafiyar ka."?Alhaji Sale ya tambaya cike da damuwa."Bakomai Mai gida banjin dadi ne."Okay ya kamata kaga Doctor."insha Allah."Anjima ka nemeni."Angama Ranka shidade."yana kashe wayar yayi wurgi da ita yana tunanin ta ina zai fara daukar fansar abin da Diga yai mashi,ranar Buba bai runtsaba tsabar bakin cikin daya tsaya mashi a kahon zuciya.
YOU ARE READING
NAHIYA TA AREWA
General FictionThe Story of Nahiyata Arewa is the one that comprise the most important things such as Correction,Injustice,Betrayl and Revenge including Entertainment and Education, is a Falatable and testable story.