_*🏝️NAHIYATA AREWA🐄*_
*NA*
_JAMEEY_
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
*PAGE 97*
Jama'a kowa yayi kokari yayi register mu Samu team ya cika zuwa karshen wata mu fara kwasar romon demoradiya,Kunga dai irin salary din da muke rabawa sunata yi mana Addu'a da sam barka suna fatan Alkairi akan wannan team work kowa yayi receiving alert Yana kwance, bugu da ka'ri kana a gefe Da'ya account Dinka Yana budewa ka ringa kwasar naira 100k a hakan ma Idan baka kawo kowa bane zaka Samu 100k Amma idan kayi kokari ka kawo jama a zaka ringa samun Sama da haka duk da haka fa akwai arias na 600k bayan budewar account dinku Alhamdulillah 🙏💃💃💃 maraba da 52u,godiya ta tabbata ga Allah 52U Alkairi ne💸💸💸💸 🥰🥰🥰💃💃💃💃💃
Contact us via
07034464517
08160508316Zaune suke baki ɗayansu saman dinning suna dinner baka jin motsin komai sai na spoon dan kuwa ko wane a cikinsu cin abinci yake cike da natsuwa da makaiwa,daman already ansan ba'a magana idan har ana cin abinci dan ka'idar His Excellency Alhaji Yusuf Umar ba'a yin ko wace irin magana ce a wajen cin abinci sai an gama ankoma parlo sai ka fadi duk abinda kake son fada,bayan sun gama Rumaisa ta kashe foodflask din ta kai kitchen ta fito ta samu waje ta zauna tana latsa waya,kallon Umar His Excellency yayi yana gyara murya yace."Babana."Ajiye wayar hannunshi Umar yayi yana ɗagowa yace."Na'am Dady."murmushi His Excellency yayi yana cewa."Munyi magana da Hajja yau akan aurenka da Khadija nan da wata biyar za'a daura auren in shaa Allah sai a fara shiri."maida kanshi ƙasa Umar yayi yana murmushi bai dai ce komai ba,wani kallo Hajia Kubrah tayi masu tana cewa."His Excellency ban gane mai kake cewa ba,ko dai Nafisa kake son cewa kace Khadija.?"Maido da hankalinshi wajenta yayi yana girgiza mata kai yana cewa."Ko ɗaya Momyn Umar yanda kunnuwanki suka jiye maki to haka ne Umar yace yana son Khadija kuma Alhmdulh Khadijar ta yarda zata aureshi shine muka tsada ranar bikin nida Hajja nan da wata biyar ba sai ki fara shiri."Tashi Hajia Kubrah tayi tana girgiza kai tana cewa."Ina ai abinda ba zai taɓa sabuwa bane His Excellency ba zan taɓa yarda ina kallo a ɗaura ma ɗana saura,yarinyar da ta gama yawon ta zubar har haihuwar gaba da fatiha tayi fa,kuma a rasa wa za'a liƙa ma ita sai Umar wallahi ba zan yarda ba gwamna tun wuri a sake shawara ama bar wanann maganar dan Umar bai da mata sama da Nafisa."gyara zaman farin glass din His Excellency yayi yana cewa."Ni kuma nace Umar bai da mata sama da Khadija, Kubrah ki fita idona na kulle fa ina ruwanki ko duka duniyar ta haifa ba ta hanyar aure ba?nace ina ruwanki?ɗa ba na kowa bane?ke idan Hunaisa tsotsayi irin na Khadija ya faɗa mata kenan ba za'a aureta ba ko Kubrah.?"Turo baki tayi tana cewa."Nidai Alhaji kabar danganta Hunaisa da irin wannan masifar nidai ba zan taɓa bari Umar ya haɗa jini da ƙashin tsiya ba kashin talauci dan haka Kai Umar da Nafisa na sanka."Girgiza kai Alhaji Yusuf yayi yana cewa."Ke karshen zamanki gidan nan da sunan Matata ya kusa zuwa karshe kenan Kubrah,mudun kika ce zaki hana auren Umar da Khadija wallahi kema karshen naki auren kenan,shashancin banza kawai da wofi in banda shirme irin naku na mata talauci da arziki duk ba na Allah bane kuma wa yafi karfin qaddara da zaki dauki karan tsana ki daura ma yarinya to naji wani magana ta tashi bayan wannan sai ranki yayi mugun ɓaci tunda har yanzun bakiyi hankali ba."Kuka kawai Hajia Kubrah ta saka tana cewa."Yanzun His Excellency akan Khadija kake neman datse igiyar aurenmu da shekara da shekaru bata taɓa girgiɗi ba?har da su zagi dan na tsaya akan gaskiya ta?ya za'ayi a duki mutun kuma a hanashi kuka?ga yarinya mai hankali da tarbiyya kamar Nafisa ka natsuwa banga makusar Nafisa ba tafi Khadija komai nasaba da asali,amman a dauki yaro a ba karuwa dan nayi magana ya kuma zama laifi."Tasowa Sagir yayi gatse-gatse ya tsaya a gaban Hajia Kubrah yana cewa."Wai Momy wace Nafisa kike maganar a haɗa Yaya Umar da ita.?"
Cikin kuka take kallon Sagir tana cewa."Har akwai wata Nafisa bayan ta gidan Momynku Khadija Sagir.?"Furzar da naunauyen numfashi Sagir yayi yana cewa."To gaskiya Momy gwanma ki barshi ya auren village girl din nan tunda shi yace yana so da kanshi,dan gaskiya ni ke son Nafisa tuni nike son Nafisa fa sai kawai kizo kice zaki haɗa Yaya Umar da Nafisa ni kuma nayi ya kenan Momy?nayi ya da zallar son da ni....Dallah can shut up ur month Sagir." Kubrah ta dakatar da sagir ta hanyar kwatsa mashi tsawa nuna shi tayi da yatsa tana cewa."Ba zaka auri Nafisa ba,Umar shine zai auri Nafisa in yaso sai ka samo wata matar ba dai Nafisa ba dan shekara sama da ashirin da wani abu mukayi alkawarin haɗa auren Umar da Nafisa tun randa aka haifo Nafisa a duniya."Girgiza kai Sagir yayi yana cewa."Allah ko Momy ko shekara dubu kukayi da yin alkawarinku ni ba ruwana da wani alkawari idan ma baki aure man ita ba har gidan Yaya Umar zan iya bin ta tunda zaɓin raina ce ita."Sagir kana da hankali kuwa? Sagir anya kuwa baka shawu ba.?"waigowa His Excellency yayi yana cewa."ba shi bane ya shawu ba Kubrah sai dai inda kece dai kika shawu kuma duk magana tazo karshe tunda shi Sagir yana son Nafisa komai yazo da sauki daman ai alƙawarin haɗa yaranku ai kuke son kuyi ko?to ga Sagir nan sai ayi dashi bai zama dole sai da Umar za'ayi ba, gobe da kaina zanje gidan Alhaji Musa muyi magana dashi sai ayi auren rana ɗaya da Umar din." Numfasawa Hajia Kubrah tayi tana cewa."Nagode sosai Umar da nuna man matsayi yina da kayi a wajenka,nagode da nuna man da kayi ban isa da kai ba ban kai matsayda in da zan baka umurni kabi ba kAceh kana so kuwa ko baka so, Khadija dai ce ko?kaje kaga gata nan alhmdulh da ba kai ɗaya na haifa ba da ace kai ɗaya na haifa da na tabbata a yau baƙin cikinka zai kashe ni,ga Sagir nan zai share man hawaye na Alhmdulh da haka,ba zan taɓa yi maka baki ba sai dai ba abinda zance maka sai nagode sakaiyar haihuwar da nayi maka kenan."Tasowa Umar yayi yana matsawa a gabanta yana cewa."A'a Momy dan Allah karda kiyi man baki karda kace haka Momy kinsan ina bin duk umurnin da kika dinga man Momy haka na kawo maki Jamila kika ce baki yarda ba na hakura ba dan ina so ba sai dan farincikinki, wallahi ban son Nafisa da ace ina sonta ba zan taɓa kin taki maganar ba sai na haɗa su da Khadija wallahi Momy ban san Allah ya kamani akan kin yi maki biyayya akan auren Nafisa da naƙi ki yafe man dan Allah Momy."
YOU ARE READING
NAHIYA TA AREWA
General FictionThe Story of Nahiyata Arewa is the one that comprise the most important things such as Correction,Injustice,Betrayl and Revenge including Entertainment and Education, is a Falatable and testable story.