079

7 0 0
                                    

_*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*_

*NA*

_JAMEEY_

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*PAGE 79*

Zaune take jigum ta buga abun tagumi tana nazarin duniya,nazarin yau da gobe hawaye suka zubo mata ba tare da ta sani ba sai dai taji saukarsu a saman fuskarta bata damu da ta dakatar da zubowarsu ba kuma bata yi yunkurin goge su ba,zaune kawai take ita dai tunda Iya Zulai ta shigo take mata magana amman shiru bata amsa mata ba numfasawa Inna zulai tayi tana duƙawa tana taɓa ta gami da kiran sunanta tana cewa."Khadija lafiyarki kuwa qlau kike kuka." Dan kallon Inna zulai tayi tana numfasawa gami da share hawayenta tana cewa."Bakomai Inna kawai ina tuna yau da gobe ne." Zama Inna zulai tayi tana cewa."Hakane Khadija sai an ringa saka ma rai hakuri duba da irin yanayin da kike ciki Khadija kuma ai yau da gobe sai mai duka." Murmushi kawai ta saki ba tare da ta sake cewa komai ba sai ma shafa cikinta da tayi tana lumshe ido jin yanda yake yi mata motsi,furzar da numfashi Inna zulai tayi tana cewa."Khadija kina buƙatar abinci ne.?" Daga kai tayi tana cewa."Eh Inna." Tashi Inna tayi tana cewa."Ga babu saura anan,amman bari naje bangaren Hajia na duba nasan ba'a rasa sauran abinci acan."kallon Inna tayi tana cewa."To Inna Allah yasa a samu bari naje da kaina na dubo." Tashi Inna zulai tayi tana girgiza kai gami da cewa."Haba keko Khadija baki ganin halin da kike ciki ai yanzun cikinki bai boyuwa ko da ƙatuwar hijab zaki saka sai an gane dan haka yi zamanki ban san wani abu yaje ya dawo kina fama da kanki bari dai naje."Toh Inna nagode sosai." Ba tare da tace komai ba ta nufi cikin gida zaune suke a parlon kasa su duka gidan Alhaji Yusuf ne kawai babu shi Umar wani abu yake dubawa a cikin system din shi yayin da Sagir yake famar danna waya Hunaisa da Momy da kuma Rumaisa suna kallon news duk da Momy kadai take da buƙatar kallon news din su dai suna zaune ne kawai ba dan ransu yana so ba,turo kofar Inna zulai tayi tana shigowa da sallama bakinta ɗagowa Hajia Kubrah tayi tana cewa."Zulai mai kika dawo yi ne a yanzun?wai ba na hanaku shigowa man parlo ba idan ina zaune da iyalaina.?" Dan dabarbarcewa Inna zulai tayi tana cewa."Hajia daman amm daman..buga mata tsawa Momy tayi tana cewa."Wai mai Zulai?zaki buɗe baki kiyi man magana ko kuwa?kina ta wai wai to ina ruwana da wani wai daman wai magana ce.?"Girgiza kai Zulai tayi tana cewa."Yi hakuri Hajiya daman Khadija ce take buƙatar abinci shine nazo na ɗaukar mata na wajenmu ya ƙare." Tunda ta ambaci Khadija baki ɗayansu hankalinsu ya dawo kanta suka zuba mata ido,maida kanta ƙasa Inna zulai tayi jin yanda idanunsu suke yawo a jikinsu ji tayi Hajia Kubrah tana cewa."Ita din Khadija take jin yunwa shine ke kuma kika kwaso kafafu ɗaukar mata abinci ga yar gold tana jin yunwa ko.?"Girgiza kai Inna zulai tayi tana cewa."Ba haka bane Hajia kawai dai haka nan nazo ɗaukar mata da kaina kuma banyi tunanin kuna hutawa ba ai da ban shigo ba." Tsaki Hajia Kubrah tayi tana cewa."Maza kije ki taho man Khadijar yanzun nan,haka zata zauna ana ciyar da ita ba tare da tana koda wanke plate a gidan ba ko?ina sane da ita tafi wata bata shigo nan ba dan har mantawa nike da akwai ta a gidan nan ma."Da toh kawai Inna zulai ta ansa tana juyawa ta fita jiki a sanyaye, kallon Hajia Kubrah Rumaisa tayi tana cewa."Haba Momy maiye dan tazo ɗaukarma Khadija abinci? ina ce kyautatawa ce kawai yasa tayi hakan kuma idan Khadija bata fitowa aiki ai sai naga ba wani abu bane tunda daman ita ba house help bace Yayanmu fa ya kawota gidan nan." Banza Hajia Kubrah tayi da Rumaisa inda ma take bata kalla ba.. koda Inna zulai ta turo kofar ta shigo Jummala take kallonta take kuma kallon hannunta dan maida yawu tayi tana cewa."Inna har kin dawo?kuma ba abincin ko.?" Zama gefenta Inna Zulai tayi tana cewa."Ko ɗaya Khadija." Dan shiru tayi tana maida numfashi tana ci gaba da cewa."An samu matsala ne Khadija." Dafe kirji Jummala tayi tana cewa." Innalillahi wa'innalaihirajiun Inna matsala kuma?kamar wace kenan?Allah yayi mana maganinta."

Dan kama hannun Jummala Inna zulai tayi tana cewa."Kwantar da hankalinki Khadija ban ana juna saka ma kanki damuwa har ta daura maki wata matsalar kinga dai yanayin da kike ci kuma tunda har kika ce innalillahi wa'innalaihirajiun ai kin gama magana duk da yau dai nasan zata faru ta ƙare ne Khadija dan cikin nan naki bai boyuwa kuma Hajia tana bukatar ganinki."tashi tsaye Jummala tayi tana dafe kirji tana cewa." Na shiga ukku nazo kuma Inna.?" Numfasawa Inna tayi tana cewa." Baki shiga ukku ba Khadija kuma ranar wanka ai ba'a biyan cibi."Da haka Inna ta tisa Jummala gaba dan tafiya da ita a hanya Inna take ta tausar zuciyar Jummala dan kwantar mata da hankali a haka suka isa har apartment din Hajia Kubrah a tunda suka shigo Hajia Kubrah ta tsira ma Jummala ido gabanta yana faduwa saboda mugun ganin da tayi bata san sanda ta mike tsaye ba tana nuna Jummala da hannu tana cewa." Innalillahi na shiga uku na bani ni Fadimatul-Kubrah mai idanuwa suke gane man haka?ciki a gidan nan?cikin haihuwa ne ko dai hanji ne suka yi maki yawa a ciki Khadija.?" A tare suka tashi tsaye duka mutunen parlon kowa da irin nashi tashin hankalin sai dai Umar duk yafi su shiga tashin hankali da masifa dan kuwa irin wannan ranar yake tsoro sai da daman Ahmad tace ya gaya ma Momy Khadija tana da ciki shi tsoronshi karda ya gaya ma Momy taki ansar Jummala,su kuwa su Momy duk kallon Jummala suke suna jiran jin ansa daga bakinta,tasowa Momy tayi tana wanka ma Jummala mari tana cewa." Ba dake nike ba Khadija?nace cikin haihuwa ne a jikinki ko mai.?"kuka kawai Jummala ta fashe dashi tana cewa." Innalillahi wa'innalaihirajiun dan Allah Momy kiyi hakuri walla...buge mata baki Momy tayi tana cewa."nayi hakurin ubanki?zaki bani ansa ko sai na saka an sakaki a kejin karnuka sunyi man yaga-yaga dake.?" Umar Y ne ya taso yana cewa."Eh Momy cikine a jikin Khadija."wani kallo Momy tayi ma Umar tana cewa."Umar ka kuwa san kalmar da bakinka yake furtawa?ciki fa kace to naji kace ciki na haihuwa ko dai fabarous ne ya fito mata a cikin.?" Girgiza kai yayi yana cewa."A'a Momy ba wani fabarous ciki dai na haihuwa ne a jiki..saukar maruka kawai Umar yaji a saman kumatunshi shaƙar kwalar shi Momy tayi tana cewa."Umar ni kake kallon kwayar idona kake gaya man wai cikin haihuwa ne a jikin Khadija?har nayi lalacewar da zakayi kwarin gayan haka." Girgiza kai yayi yana maida kanshi ƙasa yana cewa."Momy dan Allah ki tsaya ki saurareni mana kiji mai zance."In saurareka fa kace Umar ni zan tsaya na saurari yanda kayi ma mace ciki komai.?" Rintse idonshi Umar Y yayi yana cewa."subuhanalillah Momy wallahi bani ne nayi mata ciki ba dan ban taɓa zina ba a rayuwata kuma bani fatan nayi ta a rayuwata."komawa wajen Jummala Hajia Kubrah tayi tana wanka mata mari tana cewa."To dan ubanki ubanwa yayi maki ciki?da cikin shige kika shigo man gida daman ban sani ba." Ita dai Jummala komai ba tace ba sai kukan da take maruka kawai Hajia Kubrah take watsa mata tana cewa dole sai ta gaya mata wa yayi mata ciki Umar ganin yanda Momynshi take cin mutuncin Jummala yasa ya shiga gabanta yana cewa." Ya isa haka Momy dan Allah, Momy Khadija fa marainiya ce bata cancanci haka daga gare ta ba koda kuwa iskanci taje tayo cikin a waje bata cancanci haka ba balle kuma qaddara ce ta faɗa mata fyade akayi mata kuma kema nasan kin san watanni baya da suka ce anyi kiddneping din wata baiwar Allah Jummala yar rigar Hubbage nasan kin san labarin tunda har maganar kiddneping din munyi dake wanda kika kama jimami da kika ji an saki wa'anda aka kamasu tare amman banda ita saboda aurenta da shugaban yan kiddneping din yayi kin tuna ko Momy?idan har kuwa kin tuna to ba kowa bace Jummala face Khadija gata nan a gabanki kuma wannan cikin ba kowa yayi mata shi ba sai shugaban kidinafin din."shiru Hajia Kubrah tayi tana kallon Umar Y tana kuma kallon Jummala da take duke tana kuka dan Umar ya sosa mata da inda yake mata kaikayi kuka Rumaisa ta fashe da shi dan kuwa ko ita tasan labarin yarinya Jummala da akayi kiddneping ashe Khadija ce,tsaki Hajia Kubrah tayi tana cewa." To ni ruwana idan itace jummala nidai abinda na sani ba zata taɓa haifa man dan zina a gida ba dan haka sai ka maida ta inda ka dauko ta uban yan tausayi." Cikin kuka Rumaisa take cewa." Wayyoo Allah Momy ya kamata kiji tausayin Khadija ki duba a halin da take ciki kuma bata da uwa bata da uba idan kika ce a maida ta kauye wajen wa zata zauna.?"Fita idona ki kulle Rumaisa karda kema ranki ya ɓaci taje ta zauna duk gidan uban da zata zauna amman dai ba a gidana zata haife wanann cikin ba." Murmushi Umar Y yayi yana cewa." Ina mai neman afuwarki Momy akan abinda na aikata maki tabbas nima ba zanso Khadija ta haihu a gidan nan dan kuwa mai haihuwa kulawa take bukata idan ta haihu ba tashin hankali ba rikon da kika yi mata ma a yanzun nagode da hakan Momy a yau ba sai gobe ba Khadija zata bar gidan nan Momy kamar yanda kika bukata." Taɓe baki tayi tana cewa." Da dai ya fiye maka." Da haka tabar dakin zuciyarta cike da ɓacin rai,kallon Jummala Umar yayi yana cewa."Khadija tashi ki daina kuka kinji?nayi maki alkawarin daga yau ba zaki sake kukan bakin ciki ba." Tashi tayi tana cewa."A'a Umar dan Allah ka barni na koma kauye na karasa rayuwa a can dan daman tuni ni tawa rayuwar ta lalace nagode da kulawarka a gareni Allah ya saka ma da mafificin alkhari Allah ya ƙare gabanka da bayanka Umar." Girgiza mata kai Umar yayi yana cewa."Jummala kinzo birni kenan ba zan taɓa barinki ki koma kauye ba dan haka kije Inna zulai ta tayaki haɗa kaya ban san na sake jin komai a bakinki." Da to kawai ta ansa tana bin Inna dan haɗa kaya kamar yadda Umar yake bukata.

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now