_*🏝️NAHIYATA AREWA🐄*_
*NA*
_JAMEEY_
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
*PAGE 69*
Wani irin kallo ya watsa ma Ba'ba Ladidi yana cewa."Ina Hannatu.?" Yai maganar cikin kausassar murya take saida kirjin Ba'ba ya yanke ya fadi tsabar razana da kidima duk a lokaci guda ya dirar mata a cikin zuciya sake lafewa tayi bayan kofa tanajin gabanta na faman dukan tara tara."Wai Ba'ba ba dake nike magana ba?naga sai wani lafewa kikeyi sai kace kinga abun da zai kashe ki nine Ubaidu Isuhu nace ina kanwata.?" A hankali ta fito daga cikin da'kin tana kare masa kallo tace."Au ai naga tsoron ma halas ne kaida akace ba yanzun zaka dawo miye ya maido ka a fujajan irin haka.?"kallan mamaki kawai yake mata yace."a kanki nike zaune? Kinga tsohuwa ki bani amsata."tana tana tan..."wai lafiya kike abubuwa kamar dai marar gaskia Anya Ladidi? Ohhh Allah dai yasa ba wani abu bane ya samu marainiyar kanwar nan tawa ba."Furzar da naunauyen numfashi Ladidi tayi tana cewa."ai fa wannan yarinyar ko kanta aka fara maraici sai haka kai ka kirata da marainiya ubanka ma haka yake kiranta sai waccen kasashshen abokin naka shima yace da ita marainiya wai kam su sauran marainun duniya suyi yayane? Ko su su mutu." Ɗaga mata hannu Ubaidu yayi yana cewa."Ya isa Ladidi ina Hannatu.?" Tafa hannu Ladadi tayi tana cewa."Aifah tijara ta dawo da 'da tana gidan Baban ku." Cikin rashin yarda da maganar da Ladidi tayi yake cewa."wajen Babana kuma? yaushe harta fara zama a can.?"Jiyane fa kawai."OK bari in karasa ta gidan."Ya juya zai tafi da gudu Ladidi tasha gaban shi tace."banda abunka baka ganin dare yafara tara ta gota fa kabari ka huta ina laifin safiyar Allah tawaye sannan sai tazo gida kamar haka zaifi."kallan up and down yake watsa mata bawai dan ya gamsu da maganar da takeyi mashi bane ya hakura ne saboda baison ganin matar Baban nashi ne da haka yaja jakunan shi ya fa'da da'kin shi yafara rage kayan jikin shi sai ya samu kanshi cikin wani irin yanayi na daban Allah yasani yaso yafara ganin Hannatun shi saboda akwai tsarabobin da yayo mata zaiso ya batasu yana isowa 'dan kwanciya yayi yana kallan silin can kuma sai ya dauki wayar shi yace."kai bari in kirawo mai gida in shaida mashi na iso."har zai kira Umar sai kuma ya fasa yace."Aff ya dace in bari sai Hanne ta dawo daga nan saita gaishe shi."ajewa yayi sai kuma ya kara dauka yace."uhmmm kodai na hau media inga abinda ke faruwa rabona da online tun safe."da haka ya kunna data ya shiga WhatsApp saidai messages keta faman tsere fita yayi ta koma Facebook ya hau duba abubuwa can kuma ya fita ya koma WhatsApp zuwa lokacin komai ya gama shigowa fara duba sakonni yayi gasu nan rititu har zai fita sai yaga bakuwar number tayo mashi sa'ko da bazai shigaba saidai yana duba profile picture din yaga hoton Tosi hakanan ya shiga sai yaga video loading ya danna tafara kokarin budewa."yaron nan baida aikinyi ko videon minene wannan kuma mtsw?"yaja dogon tsoki saidai tana budewa yafara kallo da sauri ya mike daga kwancen da yake har jikin shi na rawa tsabar kidima voice din cikin vedion yafara saurara domin idanunsa da zuciyar sa basu iya jurar kallan videon baya fatan idonsa ya nuna masa fuskar wadda ake kokarin cewa Hannatunsa ce kara wayar yayi a kunne yafara sauraron voice din kamar haka."Uban daba kenan tabbas zakayi mamaki idan kaga abinda aminin ka 'Dahiru ya akaitama kanwar ka yaci amanarka tunda har zai iya yima kanwarka fyade idan kana kokonto ka kalli faifan videon dana turo maka kahuta lafiya."wani irin sauti kunnun Ubaidu yabada har saida yasa duka hannayen sa ya dode kunnen yayin da yake faman ka'da kai kamar na kadangare yana."karyane wannan nasan 'Dahiru ba zai taba tozartani ba."kuka ya kece dashi wiwi kamar wata mace sai kuma wani bangare na zuciyar shi yace."banda abunka ka kalli videon mana."hannun shi na rawa ya danna videon yarinyar ce kwance cikin riga da zani jikka tsaye sai gefen kafafunta jini duk yabata mata jiki saidai bai ga fuskar ta ba kuma baiga fuskar wanda yayi fyaden ba saidai yaga bayansa babban abinda yakara d'aga mashi hankali kayan jikin shi na Kure ne saboda shima sune a jikin shi saboda kusan kayansu iri dayane kasancewar anko sukeyi bai ida kallan videon ba ya kurma uban ihu mai gigitarwa har jikin shi 'bari yakeyi tsabar kidima kamar wani zautacce ya mike tsaye kai tsaye cikin lokar shi ya nufa yana cewa."yau ko ni ko kai 'Dahiru wallahi sainayi a jalinka yanda ka yagani kaci amanata saina yaga ka billahi."sharbebiyar addarshi ya dauko sabuwa dal da ita sai daukar ido yakeyi ya nufi waje."Ladidi."Ya kwadawa Ba'ba Ladidi kira bai jira fitowar ta ba yasa kafa ya halbe kofar da'kin ta har saida kyauren da'kin ya cire shiga yayi cikin da'kin ya fisgota da karfi yai wulli da ita tsakar gida yace."ina kanwata zan kashe ki."Ya d'aga takobi zai daba mata ita a hannu ta ruga a guje tana ihu, wani irin kukan kura Ubaidu yayi ya fisgota Ladidi ya dauketa da mummunan mari yace."Duk abinda yasamu kanwata saina kashe ki Ladidi babuni ba munafuki."cilar da ita yayi ya fita daga gidan kai tsaye gidan su Kure ya nufa duk wanda ya hadu da Ubaidu sai a gudu yanda yake jan dalleliyar takobi zindir da ita lokacin daya isa gidan su Kure karfe tara da kwata na dare ba kowa tsakar gida sai hasken farin wata daya haske illahirin gidan."Dahiru kana ina fito munafuki yau koni ko kai"da'kin 'Dahiru ya nufa baiyi wata wata ba yasa kafa ya halbe da'kin cikin bacci 'Dahiru yaji kururuwar kiran da Ubaidu ke auna mashi daga shi har Umma dake kwance cikin da'kin ta da gudu suka fito da sauran makota kowa yasan ba lafiya saboda muryan Ubaidu ya karade duka unguwar, wani kallo suke aikama junan su daga sama har kasa Kure ke karema Ubaidu kallo tabbas yasan ba arziki yakawo shi wajen shi musamman daya ganshi dauke da Adda tana daukar ido."lafiya ka fadowa mutane gida ko sallama babu.?"bashin dakaci shine nazo karba yau koni ko kai."tabbas gaban 'Dahiru ya fadi baitaba ganin Deeni cikin fushi irin na yau din ba."wanda ya fasa ni da kai muzu..."tun kafin 'Dahiru yakai karshen maganar shi yaji saukar adda saman kafadar shi."kam bala'i ni ka sara.?"Sara kadai? Kasheka zanyi ni kaza ketawa haddi karasa wadda zakayima fyade sai kanwata."duk irin zugin da Kure keji take ya daina jinsa kwata kwata jin abinda Ubaidu yace, wani irin bakin ciki ya tokare zuciyar Kure baisan sadda yayi kukan kura ba ya cakumi Ubaidu ya kai mashi duka a baki a take bakin shi ya fashe duka in duka suka soma kowa na kokarin yaga ya nakasa dan uwansa musamman Ubaidu ya gama hassala akan abokin nashi."Inalillahi wa'inna ilahirraji'un mi idanuna ke gane mani Deeni 'Dahiru mi kukeyi haka na shiga ukku ni Hajara Jama'a ku taimaka mani zasuyi kisan kai."Umma ta kwada uwar kara cikin kankanin lokaci har unguwar ta cika tab kamar rana zuwa lokacin sun gama galabaita junan su kowa zuciya saman makoshi ba Ubaidun ba ba 'Dahirun ba, da kyal aka rabasu sama da matasa ashirin suka rike su."ku kyale saina kashe shi, matukar bai fiddo mani kanwata ba."kowa kallan mamaki yakema Ubaidu, Umma tace."Haba Ubaidu wace magana kakeyi yau kwana biyu kenan ana neman Hannatu fa shi kanshi 'Dahiru da yamma ya dawo garin nan yana farauta."yiman shiru Umma bakisan komai shi ya dauke mani kanwata sannan yai mata fyade."Wannan kalma na kara batawa 'Dahiru rai duk sanda Ubaidu zai furtata sai yaji kamar ya kashe shi."fyade."mutanen wajen suka hada baki wajen furtawa masu salati nayi masu tafa hannuwa nayi."Kai matsiyaci ina ka kaiman kanwata."Sai naji duka sannan zan fa'da idan kai ka cika kuma ka amsa sunan ka uban daba ka sauke kaina."wani irin kukan kura Deeni yayi ya cakumi 'Dahiru suka sake rikicewa da fada sune har waje tsabar dokuwa da sukeyi duk yanda mutane sukaso su raba fadan Lamarin yafi karfin su, itako Ladidi daga kofar gida take hangen kicimillin da take faruwa tsakanin Deeni da Kure tabbas taji dadin tasan zasu iya kashe junan su farin ciki na daban takeji a ranta..Da gudu Umma ta koma gida ta dauko wayar ta zata kira mahaifin 'Dahiru saidai wayar na da'kin Kure caji hakan yasa ta nufi da'kin da gudu ta dauko wayar garin ta fito taji tayi tuntube da kafar mutun ba kadan ta razana ba da sauri ta haska wayarta a kidime taja baya ganin Hannatu kwance kamar gawa ihun data kwada shiya dawo da hankulan Jama'a zuwa cikin gidan danko Ubaidu da 'Dahiru har yar rige rige sukeyi wajen shigowa suna isowa sukayi turis ganin Hannatu kwance su dukan su suka duke kowa na kokarin daukar ta."Kada ka kuskura ka tabaman kanwata bayan ka gama kashemin ita."Deeni ya ida maganar yana rushewa da kuka mai tsuma zuciya yana duƙawa yace."Hannatu na ki tashi dan Allah kada ki mutu kibarni kinji tashi.?"rungume yake da ita yana garzar uban kuka shi kanshi 'Dahiru ya dimauta da yaga Hannatu cikin da'kin shi taya akayi hakan yafaru? yana ina hakan takasance? tambayar da yakeyima kanshi kenan, take wajen yafara daukar kuskus na mutane kowa na fadin albarkacin bakin shi."Gaskia ne dagani biri yayi kama da mutun dama mugu baida kama...."Ku fita daga cikin gidan nan munafukai."cewar Ubaidu ya daka masu gigitattar tsawa mai ka'da yan ciki."Ubaiduddeen daukar ta muje tsakar gida tasha iska." Cikin kuka yake kallon Umma yana cewa."Ya kashemin ita Umma shikenan rayuwata ta tagayyara."kallan Kure tayi cike da tuhuma tace."daina fadin haka Deeni muje."daukarta yayi suka kaita tsakar gida cikin hasken wata kwanyar suka kwantar da ita, kuka kawai Deeni keyi hannunta cikin nashi yana murzawa yana cewa."ki tashi Hannatu kada ki mutu nadawo gareki bazan kuma yarda nayi nisa dake ba na tuba kanwata."shima 'Dahirun kukan yafara yanajin wani irin bakin ciki ya tokare mashi zuciya a hankali ya dafa kafadar Deeni yace."bazan taba iya cin amanar ka ba Ubaidu bazan taba iya yima kanwarka fyade ba, wallahi badan kana jinin ta ba tabbas da nace nafika son Hannatu ina mata so na haki'ka son da mutun kanyima mace domin tazama jigon sa uwar ya'yan sa taya zan iya cutar da Hannatu ina kaunar ta har kasan raina dan Allah Deeni ka fa'da mani waya ce maka ninayima Hannatu fyade.?" Da rinannun idanuwan sa yake kallon Kure duk da dare ne amma hakan bazai hana ka kasa ganin rukidewar da idonsa yayi ba take taji wani irin tsanar aminin nashi ta sokar mashi zuciya musamman da yaji kalamansa wanda yakema kallan rainin wayo yace."Allah ya tsareni hada jini dakai 'Dahiru, kasani Hannatu bata da makiyi irin ka tunda har zaka iya aikata wannan kayan kunyar akanta bazan taba yafe maka ba kaicona ina ma banda wata alaka da kai! Inama ban kaunace ka ba kayi amfani da yardar da nayi maka kaje har cikin gidan mu ka sato kanwata kayi mata fyade! idan har bakai bane miyakawota cikin da'kin ka.?" A hankali 'Dahiru ya mike tsaye zuwa lokacin Kure yakai karshe ga hasala baisan lokacin daya dauke Ubaidu da gigitaccen mari ba cikin kunar zuci da tasafar zuciya yace."Duk abinda zakayi kayi naje na aikata."Murmushi mai ciwo Ubaidu yayi yana gyaɗa kai yana cewa."kaje ka aikata kace.?"Eh kayi abinda kake ganin ka isa kayi."kwantar da Hannatu yayi a hankali ya kalli 'Dahiru shima ya daura mashi mari mai rudarwa yace."Kure kake ni kuma Uban Daba idan ka haihu mu hadu waje yanzun nan."da'ki 'Dahiru ya fada shima Ubaidu takobin shi ya dauka ya fita waje yana jiran fitowar Kure."Dahiru ka Dubai girman Allah kada kabiye ta Ubaidu kaga yafika gaskia miyakawo kanwar shi da'kin ka.?"dakatawa Kure yayi yana kallon mahaifiyarshi yana cewa."Umma kema kina zargina kenan?"Girgiza kanta tayi tace."ina shakku ne kada kabiye sa kaga a halin da yake ciki baya cikin hankalinshi komai yake faɗa yana faɗa ne a bisa dokin fushi kuma ko waye haka zai yi."kuka ya fashe dashi yace."Dole na aje duk wani so da nikema Ubaidu mu kece raini koda zai kasheni kamar yanda ya fa'da."bai jira cewar ta ba yaja takobin sa shima ya fita, lokacin goman dare yayi duk da haka mutanen uguwa basuyi kasa a guiwa saboda sunsan yanda rikicin kaurayen yake idan har ya tashi wani bi ko 'yan sanda basu isa su kwantar da tozarma ba dama Ubaidu shine fitinannan cikin su bai gajiya da fa'da Kure na fitowa mutane suka rike shi a ciki kuwa harda mahaifin shi a shitatan ya iso wajen labarin rigimar ya iske shi inda yake, shima Isuhu isowar shi kenan ya iske mutane rike da Ubaidu yana saiya kashe Kure."ku cika shi."kowa ya sake shi Isuhu yace."idan ka fasa kashe 'Dahiru tabbas kai ba 'da bane Ubaidu tabbas zina nayi na haifeka."sai kallo ya koma kan mahaifin Ubaidu da 'dan nashi, tsaye yayi yakasa motsawa kalamin mahaifin sa ya gigita shi matuka bai taba ganin ranshi ya baci ba kamar lokacin sakin addar hannun shi yayi ya duke kasa yahau rusa uban kuka, shima 'Dahiru yarda takobin sa yayi yazo ya rungume Ubaidu shima ya fashe da kuka mai sosa zuciya yana cewa."wallahi bazan iya cin amanar ka ba Nawan kayarda dani bansan wa'anda suka aikata man haka ba."shima rungume 'Dahirun yayi suka hau kuka kamar wasu kananan yara ba kadan suka ba mutanen wajen tausayi ba sunjima a haka da kyal Isuhu ya d'aga su suka nufi gidan su 'Dahiru sai kuka suke faman shekawa."Oga plains dinmu ya rushe yanzun haka mahaifin Ubaidu ya sasanta su tabbas bamu ga tsuntsu bamu da farko"kam uban can yanzun kana ina.?"Yanzun nan nabar kofar gidan su Kure komai a gabana akayi shi."maza kazo ka sameni yanzun nan."Angama Oga."Waya fa'da maka shine yaimata fyade.?" Cewar Isuhu cikin tarin haushin dan nasa yai mashi tambayar, still kukan yakeyi babu abinda ke bala'in daga masa hankali yanda yaga ko motsi batayi har yanzun kamar gawa."Baba wannan ba itace matsala taba ka taimaka mani ka cetomin rayuwar Hannatu kada in rasata."saika fa'da mani makirin dake neman rayukan ku."malan Isuhu abin da Ubaidu ta fada shine daidai baki da'ya kanmu ya daure mu kaita asibiti can zamu ji komai."Baba wallahi banyima Hannatu fyade ba yau kwana bakwai rabona da ita tunda naje gida! kwanaki na dubo lafiyar ta harna siya mata waya kuma har yau bata taba kirana da ita ba wallahi Baba banayi maka karya Ubaidu ka amince dani."dauke kan shi yayi gefe har baisan ganin Kure tsoron sa da'ya kada zarginsa ya tabbata akan abokin nasa saboda kayan dake jikin Kure sune a jikin videon da aka turo masa take tsoro ya kara kamasa."shikenan bari akaita asibitin."Ku kwantar da hankalin ku nidai na duba yarinyar nan banga wani alamun fyade a jikinta ba, amma muje wajen likita kila bangani da kyau bane."ajiyar zuciya Ubaidu ya shide a hankali yace."muje,Allah yasa haka Umma."Amin."mota Baban Kure ya fiddo aka sata sai asibiti. "Ka tabbata har sun shirya.?"Tabbas Oga ni gano ne ba jiyau ba yanzun haka an kaita asibiti."dawa dawa aka tafi asibitin.?"Su dukan su kowa na kukan rauni a cikin su."Wannan tsohuwar fa.?" "Banda ita."da kyau muje."ina Oga.?"Idon matambayi."Sorry Sir."dalleliyar takobin sa ya dauka suka shige mota sai cikin gidan Ladidi lokacin ta fito daga ban 'daki ta iske su tsakar gida tsaitsaye bakaramar razana da kaduwa ta tsinkayi Ladidi ba."A'uzubillahi mi nike gani haka? Lafiya kuka fado mani cikin gida."ku dauko mani ita."wayyo Allah Jama'a ku kawo mani dauki."da gudu ta nufi 'daki tun kafin ta isa Tosi ya cafkota har gaban Jigiri ya direta sai raba idanu Ladidi keyi."haka mukayi dake? Dama kinsan 'dan iskan jikan nan naki zai dawo yau baki sanar mana ba? Saida komai ya rushe mana yau zaki kwashi kashinki a hannu kin dauka da wasa nikeyi.?"kayiman aikin afuwa Garba na tuba wallahi bansan zai dawo ba."kwantarman da makira inyi mata yankan rago."waiyo nashiga ukkuna kaimin rai."yau tara zaki shiga ba ukku ba."takobi Jigiri ya daga ya daurata.
Share pls
YOU ARE READING
NAHIYA TA AREWA
General FictionThe Story of Nahiyata Arewa is the one that comprise the most important things such as Correction,Injustice,Betrayl and Revenge including Entertainment and Education, is a Falatable and testable story.