_*🏝️NAHIYATA AREWA🐄*_
*NA*
_JAMEEY_
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
*PAGE 34*
Tafiya sukeyi cikin nutsuwa da sanin makamin aiki sai jiniya dake tashi saman titin yayin da kowanan su ke dauke da bindigu kirar Ak47 ba inda suka karkata akalar motocin su sai cikin garin su Jummala Hubbage har gaban gidan mai gari kamar yanda kowane bako kan fara sauka tacan dan isar da gaisuwa gamai gari wanda ya kasance kakane ga Jummala kuma mariki gareta,saboda gidansa gidane na gandu dake dauke da ya'ya da jikoki a ciki sunayin parking da sauri suka bude masa kofa,bai wani bata lokaci ba ya ziro kafar sa waje a hankali yake taku zuwa fadar mai gari,shida abokan tafiyar tasa suka maye masa baya har cikin fadar...Tara mai kyau mai gari yai masu sannan suka nuna masa ID CARD dinsu na aiki.Murmushi dauke a saman fuskar sa."Sannu da zuwa CP munajin labarin namijin kokarin da kakeyi akan aikin ka Allah ya dafa maku ashe zamu ganka ido da ido har cikin alkaryata."Jinjina kai Sanda yayi cikin jindadi yace."nagode ranka shidade idan ba damuwa inason ganawa da Jummala."Badamuwa."Iso yai masa har cikin gidan sashen da Jummala take,zaune suka isketa ta zauna makure da katan hijab da take yini da ita tunda ciki ya bayyana gareta ko bacci da hijab takeyin shi."Sannun ku da zuwa."Tace tana sauke kanta kasa tsabar kwarjinin da Umar yai mata."Yawwa."ya furta yana kafeta da ido saidai yarasa ina yataba ganin Jummala.
"Dafarko dai sunana Umar Sanda nine Commissioner of Police na wanan Jahar ta Katsina,munzo jajanta maki abinda yafaru dake sannan muna son mujadadda maku cewa hukumar Yan Sanda tananan tana iya kokarin ta dan ganin takawo karshen waɗannan mutane,ba hukumarmu kadai ba,kowa ne force suna iyakar kokari dan ganin sun tabbatar da harkar tsaro muna rokon Allah yai riko da hannayen mu akan daidai."Ameen."Suka amsa cigaba da tambayoyi yaima Jummala kuma ta amsa masa daidai gwargwado su dan jima kafin su tashi zasu tafi,kudi ya aje mata bandir biyu gaban ta."Allah yasaka da...."da gudu tayi magudada tana sheka amai kamar hanjin ta zasu zubo."Bata lafiya."Sanda ya tambayi kakan Jummala cikeda damuwa asaman fuskar shi."Eh."yace cike da sanyi."Ayyah ya dace akaita asibiti, ta shirya mukaita a dubata."Aa yallabai ai jiyama taje."bawani nan taya zamu kwasa muje asibiti bayan munsan abinda ke damun ta."Asabe tayi karaf tasa baki cikin maganar da ba akasa da itaba."mike damun ta.?"Ya tambaya dan neman sani."cikin shegene da ita dole a dinga boyo ai."Saida Sanda ya kauda kai gefe yanajin tsananin tausayin Jummala saidai ko ba'a tambaya ba yasan Asabe ba itace ta haifi Jummala koba komai kowa yasan inda ta dauki cikin yana cikin qaddarar ta.
A bangaren zuciyar sa yana jin inama bai kasance jami'in tsaro ba Allah kadai yasan mutanen da suka faɗa a cikin hali irin na Jummala koma fiye da haka amman sun gaza bada kyakkyawan tsaro a cikin al'umma baki ɗaya duk da shi aikin shi an tanaje shine dan kwantar da tarzoma a cikin al'umma da sasanci tsakanin junansu da karesu daga yan ta'adda a cikin muhallin su."Sannu Jummala."Da kyal ta ɗaga mashi,bai kara cewa komai ba yayi gaba suka fita daga gidan."Mai hali irin na uwarta aina gaya maki saikin kunshi abun kunya gashinan kin gani,kuma wadannan kudin saidai kiji kamshin su sisi bakici yar banza."Ta ida maganar tana dungurin ta hau lissafi naira dubu dari cas ta shige daki abinda,hawaye masu zafi suka ziraroma Jummala."Ki zauna tare dani,mizakiyo gida keda baki aje kowa ba...."kuka ta saki mai ciwo tuna kalaman Muhi akan zama dashi tafi mata alkhairi sai gashi ba abinda Baba Asabe ta rage wajen gallaza mata saima abinda yai gaba..gashi kullim itace ke komai a gidan tun daga sanwa har gyaran gida da wanke wanke gashi Allah ya qaddara mata laulayin ciki da yawan shi'awa barkatai amman ko tasamu kudi itake kwacewa ga girki koda batasan kamshin abu dole saita girka shi koda zata dinga amai ne,sannan idan ta fahimci Jummala nasancin abu saita hanata haka take zaune gidan cikin kunci da tarin fargaba."Kayi hakuri akan gazawarmu wajen ceton jikarka sannan insha Allah sai mun kama masu laifin nan."Umar yace da sifar kwantarwa kakan nata hankali."Bakomai Yallabai."yace yana maida kallan sa kan motar da aka rufe,take ya gane Umar Y Umar ne shida Ahmad,saboda yawan zuwa duba Jummala da Umar keyi har yagane su duk da akwai yar tazara a tsakanin su suna isowa suka gaida mai gari sannan sukayi musabaha da junan su.
Murmushi dauke saman fuskar Umar yace."Ranka shidade naji dadin haduwa dakai ashe zamu sake ganin ka cikin sauki har haka."Shima murmushin Sanda yayi suka kara musabaha da Umar cikeda sakewa kamar sun saba da juna sallama sukayima mai gari Sanda yakira Umar suka kara gaisawa yace."Journal Umar Y Umar nice to see you again."Thank you sir."Am kazo daukar rahoton yarinyar nan ne.?"girgiza kai yayi alamun aaa."najima da gama wannan aikin nazo dubata ne."gaskia kam najinjina maka samun jajirtattun yan jarida irinku da kasar nan taci gaba yawo kuke ba dare ba rana dan ganin kun kai koken al'umma inda ya kamata yaje lallai na jinjina maka Umar."Sake sakin murmushin yayi."Saida gudumuwar ku hakan ke tabbatuwa ranka shidade nagode."Ya batun abokiyar aikin ka.?" Numfasawa Umar Y yayi yana cewa."aiki sai mashi Cp."jinjina kai yayi ya saka hannun sa cikin aljihu kamar wanda zai fiddo wani abu a ciki."insha Allah kwanan nan zamu sameta."Allah yatayaku cika wannan aiki na alkhairi ina maka fatan nasara."Nagode kwarai."Har an budema Sanda mota zai shiga sai kuma ya juyo ya kalli Umar yace."can we exchange our contact.?"nudding kanshi yayi alamun.eh sannan ya sama Sanda number,sukayima juna sallama ya dawo wajen mai gari ya zauna suka sake gaisawa.
YOU ARE READING
NAHIYA TA AREWA
General FictionThe Story of Nahiyata Arewa is the one that comprise the most important things such as Correction,Injustice,Betrayl and Revenge including Entertainment and Education, is a Falatable and testable story.