051

11 1 0
                                    

_*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*_

*NA*

_JAMEEY_

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*PAGE 51*

"Morning Momy." Kallonshi Hajia Kubrah tayi tana kauda kanta gefe tana cewa."Morning kafito kenan.?"jinjina kai yayi."eh wallahi ya sanyi.?"yana lokaci."kujera yaja ya zauna yafara danna wayar shi."Umar."maida dubansa yayi ga mahaifiyar shi yace."Na'am."wai yaushe yarinyar nan zatabar gidan nan.?"take ya samu kanshi cikin damuwa tareda tsanantacciyar faduwar gaba har saida ya kasa boye hakan a saman fuskar shi mai da kan shi kasa yayi yana cewa."Sorry Momy ko akwai wani halin Jummala wanda baiyi maki ba.?" Taɓe baki tayi tana cewa."banda kwanciyar hankali idan ina ganin tana gittaya a cikin gidan nan infact ban aminta da itaba kuma kaima kasan gobe Sagir zai dawo bana son yarona na ganin poors girl kamar Jummala a gidan nan."Numfasawa Faruq yayi yana cewa."Haba Momy kiji tausayin marainiya mana bata da kowa saimu sannan dan Sagir ya dawo minene a ciki yan aiki nawa ke yawo a gidan nan sai Khadija.?" Ɗaga mashi hannu tayi tana cewa."ya isa Umar kada ranka ya baci su yan aikin da kake magana akai fadamani wadda ta fito cikin ruga kuma suna aikin su ba ruwan su da ahalina itafa Khadija? yarinya kamar aljana tabi ta tsafe mani ku daga kai har Rumaisa tausayin ta kukeji harma abun ya wuce misali ka kiyayeni Faruq." Gyaɗa kai yayi alamar to sai kuma ya haɗa hannayenshi yana cewa."na rokeki Momy kibar Jummala ta zauna tunda kinga a BQ take zaune."sallamar ta suka tsinkaya ta shigo hannunta dauke da moper tafara aiki duk da ita bata gansu kasancewar suna zaune a dining area ne zasu fara break suna jiran Exellency ne kasancewar yau week end yana tareda iyalan nashi na wasu kayyadaddun awanni da yakan ware a ranar domin zama da iyalan nashi,daga Umar har Momy Jummalan suke kallo tana aikin ta tasa katuwar hijab data wuce mata guiwar ta."Momy ina kwana.?"cewar Rumaisa dataja kujera ta zauna gefen Yayan ta,kusan atare Hunaisa da mahaifin nasu suka iso dining din baki dayan su suka mike tsaye saida ya zauna sannan kowa ya zauna."Daddy ina kwana."lafiya lau the Journal Umar Y Umar yau akwai aiki ne.?"Ɗaga kai yayi yana cewa."Eh Daddy amma sai after asir prayer."Allah yataimaka."Amin."Autata how are you.?"am fine Daddy."good Rumaisa ya naganki haka what happen.?"numfashi kawai Rumaisa ta furzar tana cewa."Bakomai Daddy."really.?"yes Daddy."good,my wife hope baku cikin damuwa.?"murmushi Momy tayi tace."yes Excellency."masha Allah."Rumaisa ta mike tafara zuba masu abinci."kallonta Hajia Kubrah tayi tana cewa."bazaki bari suyi aikin su ba.?" Girgiza kai Alhaji Yusuf Umar yayi yana cewa."rabu da ita mana zuba abinci ne fa?kin fiso ayi masu komai haba Kubrah hakan ba daidai bane yakamata ace daga Rumaisa har Hunaisa su zasu dinga girkama wannan family din abinci basai ma'aikatan gwamnati sunyi maku ba."Sorry Sir za'a gyara."da kyau."Daddy mi kake so."duk abinda yai maki zanci."toh Daddy."farfesun hanta da arish patoto ta zuba mashi."Ya Umar kaifa."saman wanda kika sawa Daddy."shima zuba mashi tayi."Momy fa."moimoi."zuba mata tayi sai ferfesun kifi daya kasance shine hadin alalan."Husaina fa."ya mutsa fuska tayi kamar taga kashi tace."ba abinda yaimin."baki dayan su suka kalleta hatta Daddy daya fara cin abinci saida ya kalli yar tasa."for what reason.?"ya jefa tar tasa tambaya cikeda tsarewa."Daddy jifa abinda aka girka mana as break no any bread nifa sandwish zanci."ke Hunaisa."yanda taji ya kira sunan sa a kausashe sai ta shiga taitayin ta."you are very stupid waike wace irin yarinya ce mai yawan girman kai da ɗagawa?ki sani ni ubanki Yusuf Umar ba kowa bane face talaka kada kiyi amfani da wannan rigar mulki dana ara na yafa ki dinga ganin kinfi kowa bana son sakarci kike raina wannan abinci mutune nawa kike zatan suna neman wandama bai kaisa ba basu samu ba wanima tunda yake bai taba cin girki makancin wannan ba,ki kiyayeni wallahi idan  har bazakici abinda Allah ya azurtamu dashi tashi kibar wajen nan matukar kikasa wata tayi maki abinda kike son ci saikin hadu da fushina sakaryar banza ana nuna maku rayuwa kinama mutane hauka,ba mamaki wani nacan baici ba duk a cikin mulkin uban ki ya kikeson inkai wannan alhakin?ya zama dole ko saboda ke da Sagir nabar wannan mukamin."haba Alhaji."da sauri Momy ta tareshi,saboda ta tsani taji yace zaiyi murabus ko kuma yace baxaiyi tazarce ba, ɗaga mata hannu yayi yana cewa."kada kisamin baki anan."kayi hakuri."sakarcin wofi duk bake ke lalatamin yaran ba indai akan mulkine kun dauki kowa sakarai."mikewa yayi da sauri Umar shima ya mike yace."Sorry sir fushin fari ba baka bane Daddy anyi kuskure kuma insha Allahu za'a gyara wannan itace damar mu da muke samun dama da kai a matsayin ka na uba agaremu bai dace kabar wajen ba."ajiyar zuciya ya fesar yanajin dadi aranshi ya koma ya zauna."Allah yaimaka albarka Umaru ina alfahair dakai Babana."thank you Sir."cigaba da kalacin kowa yayi a sirace saiga Hunaisa ta zuba dankali da kwai tanaci a matukar sanyaye..Jummala dake moping har ta iso falorn da suke zaune sai yanzun tagan su zaune a dining kasancewar kamshin abincin daya daki hancin ta wanda yai silar yamutsawar cikinta zuwa zuciyar take taji amai na neman kwace mata ga falorn da girma ko kafin ta yunkura ta gudu zuwa waje ya kubce mata,batasan ta tsugunna bisa guiwowinta ba sakamakon wulakantaccen kallan da Momy ta auna mata,saboda kowa yasan dokar Momy idan tana tare da iyalanta ba Sarvent din dake gigin shiga side din musamman idan Exellency  na nan."Momy ina kwana."baki dayan su suka waigo suna kallanta hatta Rumaisa da tabata baya saida ta kalli Jummala jin aman da take kwararawa a cikin falorn daga ita har Umar da sauri suka mike Rumaisa tayi kanta."Jummala lafiyan ki,miyasa meki.?"Wacece ita.?" Daddy ya jefa masu tambayar yana kallan Umar da Momy."yar yar aiki ce."cewar Momy tayi maganar tana inkikina."miyasa batayi wearing uniform dinta ba,wannan taka doka ne."shiru sukayi daga ita har Umar saidai hankalinsa nakan Khadijan."daku nike magana kukai man shiru."sorry Daddy za'a gargadeta akan haka."is better ta taka doka."ya ida maganar yana mikewa."zanje wajen Hajia."bai jira cewar su ba yai gaba,Momy ta aikawa Umar wani irin lalataccen kallo tace.

☆☆☆☆

"Miyasa zaimin haka waya kawo shi gidan mu,wai mi Umar ke nufi da ni.?"a lokaci ɗaya Jamila ke jeroma kanta wa'annan tambayoyin tanajin tsananin tsoro na shigarta."Jamila ga Umar ina so ki dauke shi matsayin yayan ki...maganar Baba tadawo mata sabuwa dal da sauri ta mike tsaye tana dode kunnuwanta da takejin kamar yanda yake mata zancen."Na shiga ukku  ni Umma Jamila mike shirin faruwa dani mi Umar ke nema agareni anya baida wata manufarsa akaina?anya dagaske yake son da yake cewa yanayi mani ba so yake ya kasheni ba nida ahalina ba,taya yasan gidan mu na bani."kuka ta kece dashi ba karamin razana tayi ba ganin Umar tareda mahaifin ta,ta gilgiza ganin matsayin da Baba ya bashi cikin kankanin lokaci."Ka ɗaga mana."taje ta dawo ta rasa inda zatasa kanta tsabar takaici."jefar da wayar tayi saman gado ta shige bathroom zatayi alwalla tana farayi sai kuma taji kiran wayarta da sauri fita ta dauki wayar jikinta har rawa yakeyi."miyasa zakayi mani haka?miyasa zakazo wajen mahaifina?mikace mashi?wa'anne irin kalamaine ka faɗa mashi da har sukayi tasiri agareshi cikin kankanin lokaci.?"duk a lokaci ɗaya take jefo mashi wa'annan tambayoyin."kayiman magana kayi shiru."wani irin kuka ne ya kubce mata har cikin zuciyar shi yakejin sautin kukan ta."daina kuka rabin raina."bazan daina ba kasan  halin daka jefani mi kake son in fadama Baba?hala ce mashi kayi kana sona ko me.?"shiru yayi yanajin yanda take masa bala'i tana kuka duk a lokaci daya."calm down nifa ba abinda nacema Baba kenan ba,bakiyi farin ciki ba da nakasance yayan ki.?" Girgiza kai tayi kamar tana gabanshi tace."Banji ba karabu dani dan Allah kada ka shigo cikin ahalina ka tarwatsamin duk wani farin cikina ka daukeni hakan ma bai isheka ba sai ka biyoni har gaban iyayena ka kuma cin zarafina."Jamila ki saurareni."babu abinda zaka fadaman Umar ka kyauta dakazo wajen Baba,a haka zan so ka kana son yaudarar mahaifina.?"maida kanshi yayi saman kushin ya fesar da iska mai zafi yace."am so sorry."datse wayar yayi yanajin tsananin zafi a cikin ranshi."Hello ka kashemin kira hello..."jefar da wayar ta kumayi saman gado taci gaba da rusar kukanta."na shiga ukku mi Umar keson aikatawa! Miye hadin shi da mahaifina naga takaina."cigaba da rusar kukanta tayi kanta har ciwon azaba yakeyi mata."Jamila."ta tsinkayi kiran Umma"Na'am."kizo Baban ki na kira."to tace tana share hawayen fuskarta ta,karar sako taji a wayarta da sauri ta dauki wayar tafara karantawa.
(Miyasa zaki razana dan kinga masoyin ki a lokacin daya dace,ko kinyi mamaki dan kin ganni tare da mahaifina?Jamila kenan kada ki manta yanda zuciyata ta shagala da tarin son ki,ba abinda ba zanyi ba dan ganin na kyautata maki keda ahalin ki,ki saki ranki masoyiyata ina kewarki daga naki Umar Fatah Umar,fatan alkhairi) wani irin sauti zuciyarta tayi data gama karanta sakon Umar sai takara rikicewa cikin tashin hankali."wai ko baki kusane Jamila."gani nan Umma."Jikinta a matukar sanyaye ta isa wajen mahaifin nata ta zauna saman kafat tana facing din shi tace."Baba gani."Jamila."Na'am Baba."nasan zakiyi mamakin wannan kiran da nayi maki,akan maganar bakon da kikaga nayi ne dazun da yamma kamar yanda na fada maki sunan shi Umar yazo ne domin ya gaisheni sannan shidin mutumin kirki ne ya bukaci na zame masa mahaifin sa kuma na yarje masa...cikeda razana take kallan mahaifin nata kamar yaune ta soma ganin sa."saboda haka kema ki dauke shi matsayin yayan ki kuma dan uwan ki kinajina.?"bakinta yai mata nauyi ainun kanta ya daure."ya zanyi da wannan matsalar data kunno mani kai inaga dan Baba baisan waye Umar bane shiyasa ya amsa masa wannan alfarmar saboda baisan shine ya sace ni ba da bazai karbe shi ba nabani ni Jamila miyasa Umar ya gana da mahaifina."tunanin mi kikeyi ya'ta.?"a daburce ta kalli mahaifin nata a karo na biyu tana kakalo murmushin karfin hali tace."ba ba bakomai Baba."shikenan,bakice komai ba akan maganar Umar kodai bai kwanta maki arai bane naga kin gaza samun nutsuwa."Aa Baba yayi mani kuma nagode da wannan karamci daga ganin shi shidin mutumin kirkine."nima haka nagani yanada kalama,Allah yaimaki albarka."Amin Baba."je kiyi hidimar gaban ki."toh Baba dama  idan ba damuwa ina neman alfarma agareka."inajin ki ya'ta."akan aikina ne dama akwai...."je kiyi hidimar gaban ki."Baba."ya isa Jamila bazakiyi wannan wahalallan aikin ba akansa na kusa rasaki,kina tunanin zan barki kiyi wannan aikin?kullin sainayi tir da wa'anda sukayi silar salwantarmin dake,idan masu shiryuwane Allah ya shirya kedai bake ba aikin Jarida aikin hatsarin tashi kije."a sanyaye ta tashi ta tafi tana kwallan bakin ciki.

Share pls

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now