103

5 0 0
                                    

_*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*_

*NA*

_JAMEEY_

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*PAGE 103*

Jama'a kowa yayi kokari yayi register mu Samu team ya cika zuwa karshen wata mu fara kwasar romon demoradiya,Kunga dai irin salary din da muke rabawa sunata yi mana Addu'a da sam barka suna fatan Alkairi akan wannan team work kowa yayi receiving alert Yana kwance cikin aminci, bugu da ka'ri kana a gefe da'ya account dinka Yana budewa ka ringa kwasar naira 100k  a hakan ma Idan baka kawo kowa bane zaka Samu 100k Amma idan kayi kokari ka kawo jama'a zaka ringa samun Sama da haka duk da haka fa akwai arias na 600k bayan budewar account dinku da company ta baku Alhamdulillah 🙏💃💃💃 maraba da 52u,godiya ta tabbata ga Allah 52U Alkairi ne💸💸💸💸 🥰🥰🥰💃💃💃💃💃

Contact us via
07034464517
08160508316

Haka rayuwa taci gaba da kasancewa a gidan M.  Fatahu babu wani dadi saidai godiyar Allah idan yau anyi yar dadi gobe akasin haka ne mussamman tsakanin Dago da Dije babu sauki an sace zanin mahaukaciya...kullin da kalar musiba da jifa'in da suke bijurowa da shi a gidan,malan Fatahu  yana so ya tsawatawa matan nasa, amma Baba Hinde bata barinsa, badan komai ba saboda ta tsani taga laifin Dije a gidan duk da ita ce marar hakuri, saidai ta maida duk wani laifi akan Aishatu, bayan ko cacar baki bata tabayi da kowace abokiyar zaman nata ba tun daga kan Dago har Dije, amma hakan bai hana Ba'ba Hinde ta daura laifin akanta ba,ba inda Indo kejin dadi sai a wajen mijinta shine ke bata hakuri yana nuna mata ribar hakuri da juriya wata rana sai labari.

A wajen kishiyoyin nata kuwa bata jin dadin su sam, ko wace tana iya nata kokarin dan ganin sun kuntata mata, musamman ma Dije tunda taji labarin Aishatu bata haihuwa sai ta dauki aniyar cuzguna mata kullun bata da aikin yi sai  goranta mata, tana kan yi mata habaice habaice na safe daban na dare ma daban,ita dai Aishatu ko kallo Dije bata isheta bare har tarama, saboda a ganin ta idan har tayi  fa'da da kishiyoyinta kamar ta wulakanta mijinta ne wanda bata fatan haka ta kasance ace itace zatayi silar rushewar gidan da aka raya da ita,tun shekaru talatin da suke wuce take tare da malan Fatah, ya aureta ne tun tana ya'r karamarta bata wuce shekaru sha ukku  b a duniya, yayin da shi yake da shekaru ashirin da biyar a duniya, wanda ya bata shekaru sha biyu cif a duniya, a i ya lissafin ta shekarun su talatin daidai dayin aure, gashi yanzun girma ya kamasu daga ita har shi malan Fatahun, tunda yazun ita tana da shekaru arba'in da ukku ne a duniya, shi Kuma malan yana da shekaru Hamsin da biyar daidai, shiyasa bata yarda tayi duk wani abun ashsha ko tir a rayuwarta kodan mutunci da martabar malan, ko ba komai yana sonta yana kaunar ta tun bai da komai take tare dashi tun gidan sa yana da ginin bukka Aishatu ke zaune da malan Fatah balle yanzun da yayi arziki yayi ginin tubali da rufin kwano sabanin Da dayake da rufin azara. Abu da'ya ke da'gawa Aishatu hankali shine gorin  da dangin mijinta ke yawan yi mata na rashin haihuwa gashi har karfinta ya fara karewa tafara tunkarar shekara Hamsin, amma dai shiru ALLAH bai nufa ba, ita kanta tasan malan na cikin damuwa da rashin haihuwar tata saidai bai taba nuna mata ba ko yaya ne saboda yanda yake kaunar Aishatu bako shakka zaiso yaga ya samu iri daga jikinta yaga jinin shi a cikin jikin Aishatu sannan ya gan shi yana yawo a bisa doron Kasa tabbas wannan shine babban burin malan Fatah saidai tasan hakan ba mai yuyuwa bane tunda ga abokan zaman nata nan  duk sun dauki cikukkuna daga Dago har Dije ciki ne dasu wanda ya shiga wata takwas takwas baifi wata mai kamawa ba su haife cikin dake jikin su, Aishatu bata taba nuna bakin cikinta ba akan karuwar da Allah yabawa abokan zaman nata ba, duk wata dawainiya itace ke yi masu komai a gidan hatta gyaran 'daku nansu itace ke mayi masu har abincin itace me girka masu amma a banza basu godewa sai tsina da zagin da sukeyi mata ko ina babu dadi, ga Baba Hinde itama jau! ba sauki hakama sauran abokan zaman nata saidai hakuri wanda shine ta maida abincin ta.yau ta kama litinin da safe Aminatu ta tashi da nakuda daga malan har Indo kowa ka gani hankali a matukar tashe bakaramar wahala Dago take shaba da taimakon Indo da ke ta famar jero mata sannu ta tallabeta a jikinta tana sannu Dago Allah ya sauke ki lafiya ki daure kin kusa haihuwa kinji sannu Aminatu." Duk irin wannan bala'i da Dago ke ciki Bai damu Dije ba ko keyarta bata leko waje ba bare har ta samu arzikin sannu duk da itama tana jiran nata ranar saboda cikinta ya tsufa ko a yau tana iya haihuwa, a wajen malan kuwa lekowa dakin yayi yace." Ya jikin ta nata."? Numfasawa Indo tayi kai kace itace mai nakudar tace." Da saura dai har yanzun dan ALLAH malan kayi mana Kiran Ba'ba Hinde kila ko akwai wasu y'an dubaru nasu irin na manya da zatayi mata kaga dai Ni bansan ya haihuwar nan take ba,tun dazun naje nasar mata amma shiru har yanzun bata iso ba."nauyayyen ajiyan zuciya Malan ya shige yana mai girgiza kanshi cikeda tausayawa halin da Amina ke ciki yace."bana zaton Ba'ba zatazo kan Dago kin dai san halin ta ya'r dauka da ajewa ce,amma bari in tura Bala yaje ya kira mana Hassu unguwar zoma inaga yanzun ta dawo gonar da akecemin ta tafi,sannu Aminatu ALLAH ya sauke ki lafiya ,wai nikam Khadijatu bata cikin gidan nan tun dazun banga wulginta ba,kodai ta tafi taho da Ba'ba din ne."? Ya ida maganar yana maida duban sa kan Indo da take faman yima Dago fita tace" tana cikin dakinta kasan dai ance jiki da jini kuma gashi ba wani kwarin kirki ne da ita ba." Dakin Dije ya nufa batare da ya Bata amsa ba ya shiga cikin dakin da saurin ta koma ta zauna tanajan numfashi daidai Jin takon mai gidan nasu ya nufo dakinta"Dije lafiya kike tun da asuba ban sake saki a idona ba, kodai jikin ne." Ida shiga yayi ya zauna gefen ta ya dan  bubbuga ta a hankali yana cewa."Dije na tashi mana."a hankali ta yunkura ta tashi tana turo baki gaba kamar mai baccin gaske tace."Tun dazun fa ciki na kemin ciwo."ta ida maganar kamar mai shirin yima shi kuka, numfasawa malan yayi yace."Sannu Dije na,ki daure kinji sannan kiyi ma abokiyar zaman ki addu'a tana bisa gwiwa ne."d'an tabe baki tayi sai kuma ta kakalo murmurshin karfin hali tace."Allah ya kyauta"da mamaki malan ke kallan ta yace." Ba abun ALLAH kyauta bane, addu'a take bukata."cike da kosawa tace "Haba malan yanzun ita Allah ya kyauta ba addu'a bace."murmushin manya yayi yace "wannan fagen cewa zakiyi ALLAH ya sauke ta lafiya damu baki da'ya."yana gama fa'da mata haka ya juya ya fita har ya tafi sai Kuma ya juyo yace." Yaron malan zai aiko Mudi ya kawo maki rubutu ki tabbatar da kinsha shi."toh."tace tana komawar ta ta kwanta abun ta kamar ba abun da akeyi a gidan haka Dije ke sha'anin ta,fitar malan keda wuya daga dakin Dije ya iske Dago ta haihu santalelen d'an ta namiji kukan jaririn ya karade gidan,da sauri Indo ta janye d'an tana kokarin goge masa jikin sa Hassu ta iso a rude tana ina Dagon take." Da hannu kawai malan ya nuna mata dakin tun da yaji kukan jinjiri yaji wani irin sanyi a ranshi fasama fita yayi daga gidan yana godewa Allah."Sannu Dago."Hassu tace tana amsar jaririn dake hannun Indo tace."rikemin wannan jikar  tawa duba ciki dauko mani zare a yanke masa cibin kinsan dai ba'a son ta jima a jikin jariri indai har an haifosa."toh  wlh tasha wahala sosai."Mika mata tayi ta yanke cibi tace."tashi zakiyi kisa ruwan zafi a murhu a gyara su."yanzun kuwa saidai in gyara wutar domin tun da naga haihuwa ce na tada wutan." Allah yaimaki albarka Indo kina kokari kam."Wani sabon wahalallan nishi Dago ta kuma ta ja tana kwalla ihun wahala, da sauri unguwar zomar ta iso wajen ta domin ta fahimci wata sabuwar nakudar ce Dagon keyi tace."Indo jeki ki gyara jinjirin nan,da gani ma tana kan wata nakudar ne kila Ya'ya biyu ne ma zata haifa."toh goggo, ALLAH ya biye ta bakin ki."da haka ta anshi jaririn ta nufi dakinta da shi daidai Dije ta fito tana binta da shu'umin kallo kamar taga wata bakuwa ,ita dai Indo abun da a kasata shine ta soma yi saida ta gyara jinjirin tas sannan tasa mashi kaya ta dauke shi ta nufi dakin malan dashi tana murmurshin ta mai Saka zuciyar malan cikin natsuwa tace."marhaban da bawan Allah jeka wajen mahaifin ka kasamu addu'ar sa."Shima murmurshin yai mata yace."Lale dake uwar zakina, rayuwata sannun ki da kokari farin cikina uwar Ya'yana kuma sarauniya."a tare suka sakeyin murmushin ta mika masa dan ya amsa yanajin dadi a ranta kure yaima d'an yana kare masa kallo kafin ya Maida duban sa wajen Indo yace."Allah yai maki albarka masoyiyata, kin gama mani komai a rayuwa tabbas yau rana ce mai dinbin tarihi a garemu inaji kamar kin mikomin Zakina kuma baba,Ya ALLAH ina rokon ka nuna min wannan rana"ya ida maganar yana shafawa saman fuskar sa,murmushi Ido ta sakarwa mijinta tajin tsantsar son shi aransa duk irin murnar da yake ciki na karuwar daya samu hakan bai hana shi maimaita mata burin da yake dashi ba akanta malan Fatah baida buri daya wuce yaga ya dauki jinin Ido da hannunsa,numfasawa tayi a hankali tace"insha ALLAH malan zamuga wannan ranar yanzun dai kayi masa addu'a da huduba"murmusawa kawai yayi sannan yafara yi masa addu'a saida ya gama ya da'go Kai ya kalli Ido yace"wane suna kike so a sa masa?"d'an shiru Info tayi kamar mai nazari kafin tace"Umaru"murmushi ta kumayi taci gaba da cewa"Shine sunan daya fi dacewa dashi mijina, ba dan komai ba, banda mafarkin daya wuce inga burinka ya cika malan,kuma gashi Allah ya amsa mana addu'ar mu"kamo hannayen ta yayi a hankali, ya shafi gefen kuncin ta yanajin so da kaunar ta na Kara fisgar shi yace"Umaru na nan tafe Aishatu inaji a raina zaizo kamar yanda muka tsara matsawar kin haifaman d'an fari sunan shi UMAR kuma Koda zan kare haihuwata a duniya ace Banda rabon haihuwa dake, tabbas bazan sa wannan sunan ba a kaf Ya'yan da zan haifa a duniya."tunda malan yafara magana indo ke kallan sa tarasa mi takeji akan sa, so ne ko kuwa tausayinsa takeji ita dai tasan da wahala ta haihuwa wadda ke tunkarar shekaru arba'in harda biyar bata haihu ai saidai ikon Allah kam,sihirtacciyar ajiyar zuciya ta sauke tace"duk da haka malan kaima dai kasan kowa yasan sunan da kafi kauna kenan,Kuma sunan mahaifin ka wanda na tabbata ko Ba'ba bazata taba yarda ba ace bakayi sunan mahaifin ku ba tunda dai Allah ya azurtaka da zuri'a yanzun,dan Allah ka sa Umar da ya'yan da zan haifa maka da wanda Aminatu ko Khadija zasu haifa maka duk da'ya ne malan."jinjina kai yayi alamun gamsuwa yace."tabbas duk da'ya ne, amma dai sunan Babana a da'kin ki zan sanya shi kamar yanda mukayi alkawali tun muna saurayi da budurwa."ajiyar zuciya ta shide tace"Tom malan Allah yasa da rabo a tsakanin mu Kuma Allah ya kawo mai tsoron ALLAH kuma zuriya dayyiba."Ameen Indo ta,haka nike son ji daga gareki ko kefa,yanzun mi kike so a sa mashi."malan na baka za'bi ko kuma a jira mahaifiyar shi ta dawo hayyacin ta sai ta zaba da kanta."murmushi kawai yayi mata yace."kece uwar kowa a gidan nan hatta Ni nan,dan haka wannan damarki ce Aishatu."Nagode kwarai da wannan dama amma nan gaba zan zabi wannan dai damar Aminatu ce"Bai sake ce mata komai ba ya kafa bakin sa a kunnen yaron ya gama yi masa duk abun da zai masa sannan ya mika mata shi amsa tayi yace." Allah ya raya Aliyu."mamaki fal a saman fuskar ta take kallan malan kamar ta samu Tv tace"Aliyu fa kace malan."?jinjina mata Kai kawai yayi yana mikewa tsaye itama tashi tayi tace."haba malan baka gudun abun da zaije ya dawo ne."harya isa kofar da'ki zai fita ya dakata yace."laifi ne dan nasa Aliyun."?ita dai Indo baa ce komai saima Maida kanta da tayi Kasa tanaji tsoro na shigarta ita dai tasan akwai matsala kam."mahaifin ki tamkar mahaifina nike mashi kallo bana son nakarajin komai daga bakin ki,indai har d'an mahaifa ina iko dashi sunan dana zaba mashi kenan Aliyu."ficewar shi yayi batare da ya Kuma jin daga bakin ta,ita dai Indo jikinta yai mata sanyi tasan dai Koda Aminatu tayi to tabbas Baba Hinde sai tayi tijara itama fitowa tayi daga da'kin ta iske malan tsaye da Ba'ba Hinde shigowarta kenan a gidan suna magana, a hankali ta karasa inda suke tace."barka da shigowa Ba'ba"yauwah."ta amsa ciki ciki tana cewa."toh sai ki bani d'an ko."?jikin Aishatu na rawa ta mika mata shi, ita ko Hinde sai washe baki takeyi tana."barka da arziki Dago kin raya gori da kika tashi ma sai kika haifo santalelen saurayi lale marhaban da Kai Umarul-Faruq."ita dai Indo kamar ruwa ya ci ta haka ta koma gefen bango ta lafe dama tasan za'ayi hakan."Aliyu dai Ba'ba shine sunan dana sawa yaron ai."cike da mamaki Hinde ke kallan malan Fatah baki bude tace."kagaya mani kaf dangin mu ina muka gado wannan sunan,iyehh Fatahu."?baida ce da ita komai ba cigaba da cewa tayi"Yanzun dan lalacewa ka shekara talatin kana Neman haihuwa Ido rufe yanzun kuma Allah yasa ka samu shine ka ki saka sunan tsohon ka ko? Yau naga jaraba ni Hinde! wai ma in tambayeka."?numfasawa kawai yayi yace."Ina sauraron ki Ba'ba"Dan girman Allah ina kasamu wannan sunan."?sake numfasawa yayi kamar bazai ce komai ba sai Kuma yace."nasa sunan mutumin da nikema kallan mahaifina a halin yanzun,ba kowa bane face mahaifin Aishatu,kema kinsan ta cancanci a sa mata sunan mahaifin ta koba komai duk abin da nazama a duniyar nan dai da Indo ba dinga fadi tashin neman sa har haihuwar da kike ikirarin ina nema Ido rufe da dai Indo na dinga neman haihuwar Allah bai nufa ba sai yanzun daya qaddarata akan Aminatu,saboda haka nasan ya wannan suna domin na karfafama Indo gwiwa tasan cewa duk abun da Allah ya azurtani dashi nata ne bada ta da wani shakku akan sa,kuma na tabbata ke kanki mai goyon baya nace akan wannan hukuncin dana yanke , addu'a zamuyi masa yasa ma'abocin son addinin musulunci ne,kawai Baba."idon sa ka'sa Koda wasa bai yarda ya hada ido da yayar tasa ba,yayin da ta Kasa ko motsin kirki Banda kirma ba abun da jikin Hinde keyi tsabar ki'dima da tsoron daya kamata akan kanin nata,tafi minti ukku tana kare masa kallo shidai bai yarda ya hada ido da ita ba yana dai sauraron hukuncin ta ne,itako Indo jikinta har rawa yake wannan shine dalilin dayasa bata so yasa sunan mahaifin ta ba,ita kasan yanda wasan zai kasance,uffan Hinde bata ce ma malan Fatah ba ra'ba shi kawai tayi ta shige dakin dago rike da jinjirin turus tayi ganin Hassu unguwar zoma nayima jinjira wanka inda Dago ke gefe da'ya kwance bata da Karfi ko kadan da sauri Hinde ta Isa gaban unguwar zomar tace."wai dama ya'ya biyu ne."? murmushin Jin dadi Hassu tayi tace"kwarai kuwa kin gani dai ga kuma budurwar ta, ta Kuma santalowa,gaskia Dago tasha wahala Hinde danma tasamu abokiyar zama ta gari,ita ce ta karbi haihuwar na farin fa,lokacin dana iso har ta haihu a hannun ta"uban tsaki baba Hinde taja tace."aikin banza kike fadaman fa Hassu ta ina Indo zata iya ansar haihuwa daidai dogon kashi kika ce da na yarda saboda shine ta iya gwanace a fannin nan da anci anje anjuye Masai,amma dai haihuwa ai saidai taga a nayi, kinga kawo ya'r nan kintsa Dagon dai"mika mata jaririyar tayi tana mamakin kalar tsanar da Hinde taima Indo a rayuwa,saidai uffan bata kuma cewa ba saima kama Dago da tayi suka nufi ban da'ki a tsakar gida suka iske malan da Indo yana bata hakuri duk abun da Hinde keji ba abun da basuji sannu malan Fatah ya kama jeroma Dago ita dai nata kunne ko magana Bata iyayi saidai ta da'ga kanta kawai"Fatahu."ya tsinkayi kiran Hinde,da saurin sa ya nufin da'kinsa ya shiga yace."gani Ba'ba."ka zauna ko? Kaiman tsaye 'Ki 'kam"zama yayi ka'sa yace."to Babata."

Share pls

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now