_*🏝️NAHIYATA AREWA🐄*_
*NA*
_JAMEEY_
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
*PAGE 90*
Kallon His Excellency Nurse Abida tayi tana cewa."Ranka shidade sai dai a ƙara hakuri haihuwarce tazo mata da yar matsala kaɗan tana jin ikilensiya(jijjiga) kuma jininta ya hau sosai ne amman bata mutu ba tana dai cikin yanayi addu'a take buƙata kawai in shaa Allah zata samu sauki Dr's na can suna kokari a kanta."Sauke ajiyar zuciya His Excellency yayi da yaji bata mutu ba cewa yayi."shikenan ba damuwa Allah ya tadashi kafaɗunta ya bata lafiya."Da Amin N.Abida ta ansa tana barin wajen dan komawa dakin taga cigaban da aka samu a wajen Jummala dan ita gani take kamar da wuya Jummala ta tashi, numfasawa His Excellency yayi yana cewa."Hajja dan Allah kuyi hakuri kukan ya isa haka,kunji ai tana nan da ranta ba kuka ya dace aita yi ba addu'a take buƙata Allah ya bata lafiya ya kuma raya abinda ta haifa."Sauke ajiyar zuciya Hajja tayi tana share hawayen da suka zubo mata tana cewa."Amin Yusuf Amin ya Allah." Da haka sukayi shiru ita dai Rumaisa ansar Babyn tayi daga hannun Hajja tana kallo tana jin sonshi na shiga a zuciyarta gani take kamar yayarta ce ta haihu wanda suke uwa ɗaya uba ɗaya haka take ji..lumshe idon shi Muhi yayi tana buɗewa yana jin sanyi da kuma natsuwa suna shigar mashi a lokaci guda da yaji Khadijarshi bata mutu ba, shima Hamisu godema Allah yayi da yarinyar bata mutu ba da bai san haukan da Muhi zai yi ba a asibitin nan karshenta ma a kama shi daman faderal government neman shi take ido rufe yayi mamakin da har ya shigo cikin asibitin ma ba'a kamashi ba tunda fuskar Muhsin ba bakuwa bace a wajen gwamnati ba irin videon da bayayi idan ya kama mutane,dan gyaran murya yayi yana cewa."Amman Oga Muhi da ka koma gida tunda kaji bata mutu ba zan cigaba da zama nan ina kawo maka duk information din da kake buƙata kaga asibitin nan cike take da police da DSS har da sojoji ma kar da wani ya ankare da kai a samu matsala."Murmusawa Muhi yayi yana cewa."Haba Hamisu sai kace dai ba Muhsin ba,ai duk wajen nan ba wanda ya isa ga gane nine balle har ya samu kwarin gwiwar kamani karka manta kafin na fara sai da na shirya fa Hamisu."Jinjina kai Hamisu yayi yana cewa."Haka ne Oga Allah ya ba Auntynmu lafiya."Amin kawai Muhi yace yana cigaba da kallon yaron da ke a hannun Rumaisa yana jin kaunar yaron a zuciyarsa,yana tunanin zai ma iya bari yaron yayi shekara a hannun Jummala ba tare da ya anso shi ba?tabbas a shirya kauda duk wanda zai zamai mashi barazana ga hanashi ɗaukar yaron har da ma uwar yaron idan har kuwa mutun yace zai hana tabbas zai bakunci lahira ne dan Jummala da yaronta ya yarda ya kuma yi imani sune rayuwarshi.
★★★
Kamo hannun Ramlat Momy tayi tana cewa."Haba daughter mai yasa kike haka?mai yasa kika chanza hali yanzun?sai kace bake ba anya kuwa Daughter.?" Numfasawa Ramlat tayi tana kallon First lady tana cewa."Momy nice ba chanza maki ni akayi ba Momy."Murmusawa Momy tayi tana cewa."To inda har ke ce maiyasa yanzun baki jin magana ta Daughter?maiyasa kike son ke a dole sai Son ya sake ki?kina tunanin sakin auren shine masalaha ko mai Ramlat.?" Girgiza kai Ramlat tayi tana kama hannun first lady tana cewa."Ko ɗaya Momy sai dai ni a yanzun ko kaɗan bani son Yaya Faruq da aure Allah ya cire man nima ya yaye man ya anshi addu'ata tunda har shima already bayasona kuma baya buƙata ta a rayuwarshi dole aka liƙa mashi ni ba dan yana so ba ba irin wulaƙancin da baiyi man ba da kanshi yasha yaga man ni ba'a sa'ar auren shi bace yasha gayaman baisona liƙa mashi ni akayi to ga dama ta samu nima yanzun bani bukatar zama da shi a matsayin miji dan Allah Momy ayi hakuri kawai ya sakeni ya auri wanda yake so nima a barni na auri mai sona kiyi hakuri Momy dan Allah nidai kawai ta sake ni."Numfasawa Hajia A'isha tayi tana cewa."To Ramlah idan har zaki dawo a cikin haiyacinki ki dawo kamar yanda akayi ma Faruq dole ya aureki har ya zauna dake to kema haka dolenki ki zauna da Faruq kina so ko baki so Wallahi Ramlat aurenki da faruq babu saki a cikinshi ina son kisa wannan a ranki mutuwa ce kawai zata raba inason ki zana wanann kalma a zuciyarki aurenki da Faruq babu saki kuma babu yaji a cikinshi,amman ban hanaki kiyi ma Faruq duk hukuncin da ya dace ba akan laifinka da aikata maki a baya ban hana ba dan tabbas yayi maki laifi babba dole ne yasan mutuncinki da kuma darajarki gami da martabarki a matsayinki na matarshi,amman ina mai baki umurni daga yau karda na kuskura na ƙara jin kalmar saki ta fito daga bakinki Ramlat dan kuwa baki da miji sama ga Faruq shima bai da mata sama dake idan zaki natsu ki natsu idan kuma taurin kai zakayi man ki nuna ban isa dake ba sai na gani."Hawaye Ramlat kawai ta share tana kallon Momy dan kuwa ta gaza furta komai maiyasa Momy tayi mata haka? maiyasa Momy taki yarda da bukatarta maiyasa maiyasa ai tasa daman ita tace tana son Faruq har aka hadu aka ɗaura mata shi a dole to yanzun tace bata so kuma sai ace dole zata zauna dashi, kallonta First lady tayi tana cewa."Na gama magana umurni ne na bada bawai shawara ba zama da Faruq dole ne sai ki zauna da zuciyar da ke tunzuraki akan son katse auren ku sake zama na barki lafiya."
YOU ARE READING
NAHIYA TA AREWA
General FictionThe Story of Nahiyata Arewa is the one that comprise the most important things such as Correction,Injustice,Betrayl and Revenge including Entertainment and Education, is a Falatable and testable story.