_*🏝️NAHIYATA AREWA🐄*_
*NA*
_JAMEEY_
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
*PAGE 68*
Koda su mai martaba suka koma kai tsaye asibiti ya wuce cikin ikon Allah ya samu 'dan nashi ya samu sauki harma doctor yana shirin discharge din shi wannan karon da Mommy sai Daddy ya iske a wajen shi Ramlat tabi Fulani sun koma gida."Ranka shidade sannu da zuwa."Yauwa Umaru ya mai Jikin.?"Alhamdulillahi jiki yai sauki yanzun za'a sallame shi ma."Da kyau sannu da'na."Yauwa Tsoho."ohh kasamu ko? Shine zaka fara shakiyancin ko? toh ka maida himma idan kagama nazo maka da albishir mai dadi."with surprise Faruq yace."Am so sorry na daina minene fadaman.?'' Ina gwamnati ta hana aikin banza saika biya."Murmushi Faruq din yayi yace."Naji zan biya minene na kosa naji wane albishir ne wannan."Numfawa mai martaba yayi yace."daga gobe zaka iya zuwa wajen yarinyar nan daka kusa wucewa ta silarta saika nemi so a wajenta."Wani irin dadi ya mamaye zuciyar Faruq kamar an wullo shi daga kan gado ya rungume mai martaba yana murna har jijjigashi yakeyi tsabar farin ciki yace."Am so happy dagaske an bani Jamila.?"Aa nifa ba cewa nayi an baka Jamila ba, nadai ce kaje ka nemi so a wajen yarinya da alama mahaifin ta mai bai wayence ka sosai ba kaga daga nan sai yakara sanin ka,saidai akwai kalubale a gareka."Take annurin fuskar shi ya dauke yace."kalubalen me.?"A gaskia yanzun haka akwai wanda ke sonta da ace anyi mata baiko da saidai ka hakura da ita saukin ma ba' ayi ba kaga ya zama dole ka dage kaga kasace zuciyar yarinyar har ta fiddaka matsayin Jarumin ta."Hmm wannan fa ba matsala bane tunda Babanta ya aminta dama shine barazanata ina da qualifications din da za'a soni dan shi."Jinjina kai mai martaba yayi yace."yaro yaro ne ka daina fadan haka kaje ka jaraba sa'arka."Mikewa Daddy yayi yace."Abba ka daina biye ta Faruq baisan duniya ba."kwabe fuska yayi kamar zaiyi kuka tsabar sangarta da gatancin da yai masa yawa yace."No Daddy am president son kada kamanta kuma inada cikkakkar nasaba tako ina kudi ba matsalata bane uwa uba kyau Allah ya wadatani dashi mi zaisa ta'ki ne.?"Hmm wannan shine babban shirmen da zaka tafka ba kowane side bane wa'annan abubuwan daka lissafo sukeyin rana ba, ka rike mutunci da dadtako, Ishaq and Khalid ku kara kwatanta ma shi.'Toh Daddy."hmm nifa wallahi ina mamakin yanda ake biyewa Faruq yarasa yarinyar da zaiso sai talaka, talakarma mai yawo a titi 'yar Jarida tana gantali da batala haba Abba wai minene aibun Ramlat bai...."ya isa Aishatu ranki zai baci."A fusace mai martaba ya katse zancen Mommy ta hanyar d'aga mata hannu yaci gaba da cewa."Da talaka da mai arziki daga Allah ne sannan ki sani aikin Jarida ba aikin gantalalallu bane, daga yau na haramta maki wannan maganar kwara tun wuri ki sama lamarin nan albarka, sannan ina so kisa wannan aranki da ace Ramlat tace bata son Faruq bata ra'ayin zaman aure dashi ya zama wajibi ya saketa saboda itama 'ya ce a wajena kamar shi! abinda yasa bansa Faruq ya sallami Ramlat ba saboda shi namiji ne kuma shidin mijin mace hudu ne shiyasa na bashi dama ya auri wadda yake so shima bai dace a tauye nashi hakkin ba shine ina tufka kina neman warwareman wallahi kinyi kadan zan saba maki."kayi hakuri Abba daga nan bazan kuma yin makamanciyar wannan maganar ba Allah yasa albarka ya tabbatar mana da alkhairin sa."Amin, ku tashi muje."Da haka suka dunguma zuwa gida kai tsaye dakin shi su Khalid suka wuce dashi basu jima da zama ba Ramlat ta shigo da'kin ita da Fulani Maryama suka duba shi sannan suka fita suka barshi da matar shi koda su Khalid suka fita garden suka wuce shida uncle I cikin tarin damuwa Khalid yace."Uncle akwai matsala."cikin tarin mamaki da fargaba Uncle yace."miyafaru.?'dagani mahaifin Jamila bai gane Faruq mai martaba yake nufi ba."kallon Khalid Uncle I yayi yana cewa."Miyasa kace haka.?"numfasawa Khalid yayi yace."Ni kaina da naga bawan Allahn nan shine mahaifin Jamila na girgiza sosai saboda akwai kwantacciya a tsakanin shi da Faruq bana tunanin zai karbi Faruq a matsayin surikinsa."Cikin tarin kidima da tsoro uncle I yace."kaina ya kulle kasani a duhu."Ajiyar zuciya ya sauke yace."bazaka fahimci Lamarin ba."ka fahimtar dani mana."Girgiza kanshi yayi yace."bazaka ji mutuwar Sarki a bakina ba amma I will promise zan fada maka amma sai idan Faruq yaje gidan su Jamila Baban ta ya karbe shi hannu bibbiyu ni kuma zan fada maka abinda yafaru."nauyayyar ajiyar zuciya ya fesar yace."kana so na kasa bacci kenan.?"Aa ba haka bane kaidai kayi addu'a insha Allah komai zai daidaita."shikenan saukin ma kaine zaka raka shi."Aaa bazanje ba."Kaima kasan takawa bazai bari Faruq yaje shi kadai ba."kai zaka raka shi dai."murmushi yayi yace."ka taba ganin inda kawu ke raka 'dansa zance.?"indai kaine yanda kakeji da wannan 'dan naka komi zaka iya kaga daga kanka sai afara."dariya sukayi baki dayan su uncle I yace."Naji sai muje baki da'ya."da dama dama indai hakane zanje."Allah yakaimu, mu shiga ciki duk nagaji ina bukatar hutu."is better da gajiya."tashi sukayi kowa ya wuce da'kin shi saidai maganar Khalid ta tsayawa uncle I a cikin zuciya.
YOU ARE READING
NAHIYA TA AREWA
General FictionThe Story of Nahiyata Arewa is the one that comprise the most important things such as Correction,Injustice,Betrayl and Revenge including Entertainment and Education, is a Falatable and testable story.