081

8 0 0
                                    

_*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*_

*NA*

_JAMEEY_

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*PAGE 81*

Numfasawa Sanda yayi yana sauraren yanda Ammi take cewa cikin kuka,furzar da numfashi yayi mai zafi yana cewa."Ammina dan Allah ki kwantar da hankalinki in shaa Allah Sara zata dawo cikin aminci da lafiya kibar wannan kukan karda ya jawo maki wata matsalar kuma."Daga bangaren Ammi take cewa."Sanda har yaushe zata dawo?dan Allah Sanda kayi wani abu a kai karda su cutar maka da yar'uwa."Jinjina kai yayi kamar yanda gabanta yana cewa."In shaa Allah Ammi nayi maki wannan alkawarin." Da haka Sanda ya kashe waya yana cewa."Yes come in." Shigowa dan sandan yayi yana ƙamaiwa gami da cewa."Sir anyi tracking number da taimakon airtel office saboda rashin yi ma sim din register kuma yana kashe." Numfasawa Sanda yayi yana cewa."Yanzun dai ya ake ciki suna a wani gari.?"Sir suna anan cikin garin Katsina a dutsen safe low-cost." Sauke ajiyar zuciya Sanda yayi yana cewa."Weldon Asp Khamis a haɗa mana officers a cikin personal karda ka yarda maganar fitar tamu tayi nisa ka samu amintaitu kamar guda biyar kai da ni mu kama bakwai zamuyi operation."Yes Sir." Da haka Asp Khamis ya tafi dan haɗa yan sandan da zasuyi operation..cikin mintin da baifi goma ba aka gama hada yan-sanda cikin personal ba cikin motar yan-sanda sukayi tafiyar ba a shiryarce akayi tafiyar cike da kwarewar aiki dan kuwa wanda suka dauke Sara basu kawo ma kansu za'a gano inda suke ba dan kuwa bayan sun tura ma sanda video Sara suka kashe wayar suna cigaba da hidimar gabansu dan kuwa ba kananun Kudu suka shirya ansa a wajen Sanda ba kuma ba wasu bane suka ɗauke yarinyar face wasu daga cikin shaƙiran coursemate dinta sune suka ɗauketa a hankali da kuma dubara suka zagaye gidan da Sara take cike da dubara suka kai masu hamamai shiga sukayi a parlon suna cewa."kar wanda ya motsa daga inda yake kar wanda ya motsa daga inda yake."Ɗaga hannunaye sukayi take akayi gaba dasu bayan an kunto Sara a cikin wani daki daura da igiya an dabaibaye ta direct asibiti Sanda ya nufa da Sara su kuma Asp Khamis sukayi station da yaran da suka dauke Sara wannan kenan.

★★★

A yau aka sallami Garba Jigiri daga asibiti hannu ya warke tas ba inda yake mashi ciwo a hannun,tafiya suke shi da Tosi da yake Tosi shine yayi jinyar Jigiri har tsawon watanni dan kuwa kaf dangin Jigiri kowa cewa yayi ba ruwanshi basu suka aika shi ba dan kuwa daman ance wanda baiji bari ba,dogon tsaki Tosi yayi tana kallon hannun Jigiri da yake yanke kamar bashi ba yana cewa."Allah ko Maigida Ubaidu bai cire ma banza hannu ba tabbas sai ya amshi hukunci daidai da laifin shi Allah ko Oga."Firzar da naunauyen numfashi Jigiri yayi yana shafa hannun da aka cire mashi yana jin wani irin zafi a zuciyarshi kallon Tosi yayi yana cewa."Tosi kenan tabbas ko baka faɗa ba kaima kasan ba zan taɓa yafe wannan asarar da Ubaidu yayi  dole ne shima ya dandani irin ɗacin da na ɗanɗana a wannan zuciyar tawa,kuma itama wannan munafukar tsohuwar ta gidansu ba kyaleta zanyi ba itama sai ta gane itace silar hada komai."Jinjina kai Tosi yayi tana fadin."Gaskiya ne Maigida itama har hannun sai an cire mata dan ta riga ta saka kanta a cikin faɗan da babu ruwanta kam."Jinjina kai kawai Jigiri yayi bai sake cewa komai ba dan kuwa idan ana sallah ba'a magana...zaune Ubaidu yake yana kallon Hannatu yana cewa."Yauwa kanwata zauna na kira maki gudan Yayan naki ku gaisa ko?tunda na dawo ban samu damar yin waya da shi ba saboda tashin hankalin da na tarar."Murmushi Hannatu tayi tana cewa."Allah sarki Yayana to shi ya sunanshi.?"Numfasawa Ubaidu yayi yana cewa." Shi din mutunen kirki ne kuma maison tallakawa da son kyautata masu sunan shi Umar amman da Yaya shika zaki ringa kiranshi." Washe baki Hannatu tayi tana cewa."Allah sarki Yayana to kira man shi." Dannawa Diga kira Ubaidu yayi murmushi ya saki yana cewa."Barka dai Yayana kaina a ƙasa Yayana."Girgiza kai Ubaidu yayi yana cewa.'Afuwan Yayana kaina a raina."Numfasawa Ubaidu yayi yana gaya ma Diga abinda ya faru a tsakanin shi da Jigiri da kuma abinda Ba'ba Ladidi tayi cigaba da cewa Ubaidu yayi."Wallahi Yaya ba dan Baba ya hanani cire ma sauren yaran nashi hannaye ba da tuni suma na cire masu nasu hannun,kuma abun baƙin cikin da takaici wai Ladadi ta dauko hanyarsu wai su kashe man Hannatu wai tsanar da Ba'ba take mana har ta wuce tunani na to yanda baƙin cikin Ba'ba ya zama ajalin mahaifiyata haka nima nawa baƙin cikin zai zama ajalinta."Cike da jimami da kuma son fahimtar da Ubaidu Diga ya fara cewa."Tabbas banji dadin duk abunda faru ba kuma Ladidi bata kyauta ba amman kabar cewa haka ai ko nan aka tsaya Ubaidu baƙin cikin rasa kunnenta ɗaya ma da tayi ya isa ya kashe ta balle kuma taga kana ci gaba kai da kanwarka taka ka zama wani a kasar nan kuma baka taimaka mata da komai kayi watsi da ita a haka ma sai ta hadiyi zuciya ta mutu saboda bakin ciki dan haka ba zaka ƙara kwana a Sumaila ba dan bansan wannan harka ta banga irin taku da kuke bata haifar maku da komai sai asarar rayuka da kuma wani sashe na gangar jiki to wace irin riba ce wannan?yan'siyasa na amfani daku suna baku kwayoyi kuna sha kuna fita haiyacinku kuna aikata barna dan haka wannan siyasar ba za'ayi haka da kai ba,umurnin da nike baka kai da Kure da kuma Hannatu ku hado komai naku ku dawo katsina ina da gidan da zan kai Hannatu nasan za'a kula da tarbiyarta kuma zatayi karatu mai zurfi kamar yanda kake mafarki,kaima kanka kaida Kure duk makaranta zaku koma kuyi karatu dan gina rayuwarku ku rabu da wannan kauyen naku dan kuwa ban son zuciya ta kaika kayi wani abun azo ana kuka nan gaba dan nasanka na kuma san zafin zuciyarka."Girgiza kai Ubaidu yayi kamar Diga yana gabanshi ya fara cewa."Amman Yayana sai naga da dai ka bar maganar dawowarmu Katsina dan kuwa idan...Ya isa Ubaidu." Diga ya dakatar da Ubaidu yana mai cigaba da cewa."Bani magana biyu sannan kuma ba'a yi man musu idan har nayi magana umurnin da na bada kawai ake cika dan haka zan turo maka kudin mota ku taho Katsina a yau din nan ba sai gobe ba,ba cewa zakayi idan ka dawo Katsina mutune zasu ce tsoro ne ba saboda karda Jigiri ya rama abinda kayi mashi ba.?"Cike da mamakin yanda Umar ya gane manufarshi yake ɗaga kai yana cewa."Eh Yayana shiyasa nike son na tsaya ya dawo asibiti duk randa ya dawo mu sake fafatawa ko ni ko shi."murmushin manya kawai Diga yayi yana cewa."To maza ku taho ka rabu da wannan dabar bata da amfanin komai sai kayan nadama da nasani kanena kazo nan kaga yanda ake yin siyasa cikin yanci da ilimi kaji.?" Daga kai Ubaidu yayi yana cewa."To Yayana."kashe wayar Diga yayi bayan ya gama sheda mashi zuwan nasu a yau din,kallon Hannatu yayi ta buga tagumi tana kallonsu murmushi ya sakar mata yana cewa."Kanwata maza shiga wanka ki shirya kafin na dawo zamu tafi Katsina ai zaki je ko.?"Murmushi ta saki cikin jindadi take cewa."Ehmana Yaya zan je ba naji yace har karatun boko za'a saka ni ba.?"Ɗaga mata kai yayi yana cewa."ina fatan idan har aka saka ki,ki maida hankali akan abinda aka turaki yi Hannatu."Jinjina mashi kai tayi murmushi ya sakar mata yana fita itama wankan ta tashi ta fara shirin shiga....koda Ubaidu ya fita direct gidansu Kure ya shiga da sallama a bakinshi ya gaida Umma, sannan ya shiga ɗakin Kure zaune yake yana wasa wuƙa dan shi labarin dawowar Jigiri tazo mashi ance suna hanya saukar dare zasuyi shiyasa ya fara shiri dan yasan tabbas Jigiri ba zai taɓa yafe cire mashi hannu da Ubaidu yayi kuma shi ba zai taɓa barin Jigiri ya cutar mashi da Ubaidu ba sai inda karfinshi ya ƙare,kallon wukar Ubaidu yayi yana cewa."Nawan daji zaka shiga ne.?"Murmushi Kure yayi yana kallon Ubaidu yana cewa."A'a Nawan ina gyara masu ƙaifi ne saboda mai tsotsayi ai kaima ai kasani fa."Zama Ubaidu yayi yana cewa."Ka kyauta shiyasa nike alfahari da kai nawan."Dan numfasawa Ubaidu yayi yana cigaba da cewa."Daman zuwa nayi na gaya maka Oga Diga yace komai muke yau tayi mana a cikin Katsina har da Hannatu ma."Ajiye wukar Kure yayi yana cewa."Kamar ya kenan?har yaushe kuka haɗu da Oga Diga din?kuma mai ya sako Hannatu a ciki.?"Gyara zamanshi Ubaidu yayi ga gaya ma Kure komai har tafiyar da yayi Diga ne ya bukaci ganinshi kuma yaga Diga ido da ido komai dai ya gaya mashi har saka Hannatu a makaranta dasu kansu da Diga yace numfasawa Kure yayi yana cewa."Shikenan Nawan zan bika ba dan komai ba sai dan cikar burin mu nayin karatu mai zurfi dan haka bari nayi sallama da Umma ko?Tasan da tafiyar." A tare suka fito tsakar gidan sukayi ma Umma bayanin komai sai da ta tabbatar da babu wata matsala komawar tasu Katsina suka ce mata eh addu'a tayi masu da fatan nasara shigowa Abban Kure yayi shima aka gaya mashi addu'a yayi masu daman shi jininshi a farce yake na zaman da su a cikin garin har yanzun bayan ƙurar da take kwance ya tabbata duk randa Garba ya dawo sai ya tadota shi kuma matsalar da yake gudu kenan..jikkar kayanshi kawai Kure ya ɗauka da wuƙaken shi dan ba barsu ba suna da matuƙar tarihi a wajenshi,koda suka koma gidansu Ubaidu Hannatu ta shirya ta saka Isuhu gaba da bai jima da shigowa ba tana bashi labarin komawar tasu birni da kuma karatun da za'a saka ta jinta kawai yake jiran dawowar Ubaidu kawai yake suna shigowa Ubaidu yace."Baba ka shigo kenan?daman yanzun nike niyar kiranka waya naji inda kake nazo."numfasawa Isuhu yayi yana cewa."Na shigo baka daɗe da fita ba ma ku zauna muyi magana Ubaidu ke kuma Hannatu tashi bamu waje." Zama sukayi bayan Hannatu ta tashi ta koma dakinta kallon Ubaidu yayi yana cewa."Yanzun naji Hannatu tana man wata magana mai kama da tatsinniya shiyasa na zauna jiran dawowarka dan naji daga bakinka da gaske Katsina zaku koma da zama kuma har da Hannatu.?"Gyaɗa kai Ubaidu yayi yana cewa."Eh Baba hakane zamu koma Katsina." Girgiza kai Isuhu yayi yana cewa."Ubaidu ina jin tsoro fa,kaga yarinyar nan marainiya ce ku duka baku da kowa sai ni haka nima ina tsoron karda ku jefa kanku a wani mayuwancin hali ba tare da kun sani ba balle ace Katsina kasan yanda garin yake cike da yan boko."numfasawa Ubaidu yayi yana cewa."ka yarda dani Baba babu abinda zai faru sai alkhari ai kasan dai Diga kanajin sunanshi dai a wannan Nahiyar tamu ta arewa ko ma nace kasar baki ɗaya ba wanda bai san dan bangar siyasa Diga ba duk da ba kowa ya tabbata ganinshi ido da ido ba."Ɗaga kai yayi yana cewa."Kwarai kuwa nasan sunan."To Baba mu wajenshi zamu koma nida Dahiru zamuyi irin tashi siyasar ta yanci da ilimi kuma zai sakamu boko danyin karatu mai zurfi itama Hannatu zai kai gidan su ne wajen mamarshi dan tayi karatu mai zurfi." Girgiza kai Isuhu yayi yana cewa."Ubaidu baka da hankali ashe?waye bai san Umar Diga babban dan'ta'adda bane a kasar nan ba Ubaidu shine zaku koma wajenshi daman ya muke fama daku balle kuma kun koma wajen Diga ai sai abinda hali yayi kawai."Girgiza kai Ubaidu yayi yana cewa."Baba a idon mutune Diga tabbas dan ta'adda ne amman idan har ka zauna dashi na kwana ɗaya kawai zaka san waye Diga zaka san shi mutun ne mai kyaun hali da son taimakon tallaka ba kamar matasa da bai da aiki kullum sai janyo matasa a jiki mararsa aikin yi ya basu jari ya kuma saka su suyi karatu mai zurfi dan zama wani abu anan gaba ni nan ganau ne ba jiyau ba tunda kwanakin da nayi ba Sumaila a wajenshi naje anan nasan ilar shaye-shaye ga lafiyar jikin dan'adam koda kuwa tabar sigari ce kake shi Baba,baka tunda na dawo ban sha komai ba?ai shi Digan ya gayaman silar abun shiyasa nike kokarin barin sha har abada."Shiru Isuhu yayi yana nazarin maganar Ubaidu can kuma ya numfasa yana cewa."Shikenan Allah yayi albarka a kiyaye kuma a dinga kira ana gaisawa dan jin ya kuke dan Allah Ubaidu."In shaa Allah Baba."Sosai Isuhu ya kara yi masu wa'azin na su kasance mutune masu rikon gaskiya da amana daman yasan basu sata kuma basu ba yin sata har abada dan duk jininsu babu ɓarawo itama Hannatu sosai yaja mata kunne wajen kamun kai ba ruwanta da mazan birni karatu ya kaita dan inganta rayuwarta to ta natsu tayi karatunta har ta cimma gaji,da zasu tafi ihu Ladadi ta kurma tana cewa."Ban yarda da wannan tafiyar ba Isuhu idan na isa karda ka bari su tafi da Hannatu wa zai kula dani ina fama da wannan jinyar."Tak Isuhu bai tamka mata ba dan shi daman tunaninshi yanda zai fitar da Hannatu Sumaila yake ba dare ba rana dan bai san wani abu ya samaita akan abinda Ubaidu yayi a kanta kuma ga dama ta samu ba zai biye ma kuma duk abinda ya faru da ita ai ita ta sayar ma kanshi da kudinshi shi dai Allah ya sani yayi iyakar yin shi..kamar an hura wisil haka maganar tafiyar su Ubaidu birni ta karyaƙe garin sumaila wasu na cewa tsoro ne yasa suka gudu dan sun san Jigiri zai ɗauki fansa wasu kuma na cewa ayi can an huta da faɗace-faɗacen da suke yi a cikin gari har tasha Isuhu ya raka su bai bar tasha ba sai da yaga tafiyarsu sanann ya dawo yana goge hawayenshi zuciyarshi cike da kewar yaranshi ba kamar ma Hannatu da yafi sabawa da ita sama da Ubaidu.

★★★

An duba Sara a asibiti ba abinda ya samaita dan ko kwana basuyi ba aka sallamaisu suka koma gida,a ranar Sanda bai samu damar zuwa wajen Jamila ba sai dai ya bata hakuri kawai ya zauna yana lailasar Ammi da kuma gaya mata ba wasu manyan yan'iska bane suka ɗauke Sara wasu yarane kuma suna hannu a yanzun haka ta kwantar da hankalinta ya daɗe sosai a gidansu sannan ya sake wanka yana fita dan tafiya station koda sanda ya koma station ya tadda wanda suka ɗauki Sara sun sha matsa a wajen sergeant ba ƙaramin jibga suka sha ba sai haki suke suna neman agaji bayan ya dan huta yasa aka shigo mashi da ɗaya daga cikinsu tunda aka shigo dashi sanda yake kallonshi daga sama har kasa dan matashi ne idan yayi gudu yakai shekara 27 a duniya girgiza kai Sanda yayi yana nuna mashi waje ya zauna yana cewa."Ya sunanka."Bilal." Matashin yace yana maida numfashin wahala, numfasawa Sanda yayi yana cewa."Bilal ko maiyasa kuka yi kiddneping din Sara?waye ya saka ku wanann aikin.?"Girgiza kai Bilal yayi yana cewa."Wallahi ranka ya daɗe ba wanda ya sakamu,mu muka saka kanmu."Okay idan ba wanda ya sakaku kune kuka saka kanku maiye dalilinku na yin kiddneping din nata?okay daman can already kune kiddnepers din kuke ɗauke mana mutune a wannan jahar tamu ta Katsina ko.?"kuka Bilal ya fashe dashi tana girgiza kai cikin kuka yake cewa."A'a wallahi ranka ya dade mu tunda muke bamu taɓa yin kiddneping ba sai yau kuma a kan Sara."Karya kake ba zan taɓa yarda da maganar ka ba dan haka ina kuka kai sauran mutunen da kuke yin kiddneping din.?"A'a wallahi ranka ya dade ka yarda dani bamu taɓa yin kiddneping ba asali ma mu ko sata bamu taɓa ba ko ta maiye yanzun ma wallahi qaddara ce ta gitta mana bamu da yanda zamu samu kudi shine muka yanke shawarar sace Sara saboda munga kanwarka ce zamu samu ko nawa muka buƙata a wajenka."gyara zamanshi Sanda yayi yana cewa."Qaddara daman qaddara tana saka mutun yin kiddneping kenan?toku wata qaddararce ta saka ku.?"Share hawayenshi Bilal yayi yana cewa."Wallahi ranka ya dade mahaifin Salis ne bai da lafiya tsawon shekaru tun suna biyan kudin magani har karfinsu ya kare suka zo suna saida kadarorunsu duk dan nema mashi lafiya har ya kai da babu abinda zasu ɗaga su sayar dan yi mashi magani ga karatu yana yi dan muke daukar nauyin karatun yan-squad dinmu muke haɗa kudi muna mashi registration saboda shine babba a gidan shi kuma yaji da kudin magani sai da akayi mashi wani test aka gano kodarshi ce ta samu matsala ana bukatar chanza mashi wata daman an taɓa yi mashi dashe ta Salisun aka cire itama ta samu matsala dole a sake mashi wata,dukanmu an auna kodarmu bata hau ba dole sai mun sayi koda ga kudin aiki ga kudin kwanciyar da zai yi asibiti mun nemi taimako har gidanje rediyo shiru ga mahaifin nashi yanajin jiki shine muka yanda shawarar yin kiddneping din Sara ko mun samu kudin da za'a sayi koda da kuma yi mashi aikin."ba tare da Sanda yace mashi komai ba yasa a fita dashi aka shigo da wani sunanshi ya tambaya yace mashi Musa  shima tambayoyi yayi mashi ya kuma gaya mashi the same ansar da Bilal ya bashi haka har akazo kan Salisu sosai Salisu yake kuka yana cewa."Ranka ya daɗe dan Allah karda ayi ma abokaina komai dan duk abinda ya faru sunyi ne saboda dani dan ceto ran mahaifina naji zan ɗauki duk hukuncin da za'a yanke su abarsu." Numfasawa Sanda yayi yana cewa." Ko zaka gaya man maiyasa kace komai sukayi sunyi saboda kai.?" Gyaɗa kai Salisu yayi yana gayamashi komai,kuma duk magana iri ɗaya ce da ta sauran, numfasawa Sanda yayi yana cewa."Ka yarda idan har naje gidan naku naga lafiyar mahaifinka lau na yanke maku duk hukuncin da ya dace?kun san dai hukuncin kisa ne akan duk wanda aka kama da laifin kiddnep ko?"Ɗaga kai Salisu yayi yana cewa."Eh wallahi na yarda Ranka ya daɗe." Furzar da naunauyen numfashi Sanda yayi yana tambayar Salisu address din su gayamashi yayi ya saka aka maidasu cell shi kuma ya tafi shi da Asp Khamis sosai sukayi bincike a unguwar su Salisu suka kuma tabbatar da rashin lafiyar mahaifin nashi jiki sake sanda ya dawo office zuciyarshi ba dadi da yaga halin da mahaifin Salis yake ciki kasa ƙara yin komai yayi a office sai dai kawai ya tafi gida yana bada order karda a sake taɓa su da haka ya tafi kasa isa gida yayi sake komawa gidansu Salisu yayi yasa akai Abba asibiti ya biya kudi da komai aka fara yi mashi treatment akan a bashi kwana biyu za'a kawo kudin koda da haka ya dawo gida yana gaya ma Ammi duk abinda ya faru da dalilin da yasa yaran sukayi kiddneping din Sara har da hawaye Ammi tayi saboda tausayin yaran taji har cikin zuciyarta.

Share pls

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now