065

6 0 0
                                    

_*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*_

*NA*

_JAMEEY_

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*PAGE 65*

"Sunan ta Jamila ainahin 'yar nan garince Alhaji Abubakar shine sunan mahaifin sannan yarinyar 'yar Jarida ce, wannan shine ainahin abinda na sani akan ta."Jinjina kai mai martaba yayi yace."ka tabbatar da abinda ka fa'da man?" Jinjina kanshi yayi yace."kwarai kuwa ranka shidade na tabbata."Yar Jarida fa kace? Ko itace wadda kwanaki yace yana so?"Eh Ranka shidade ya hadu da ita lokacin da suka kawo maka ziyara."cike da gamsuwa yace."anyi haka ai na dauka a lokacin shirme ne irin Faruq din ya motsa toh koma Yayane kasan gidan iyayen ta.?"kwarai kuwa ranka shidade na taba raka abokin nawa kusan sau biyu saidai sau da'ya muka taba gaisawa da yarinyar amma ban sani ko daga baya shi Faruq din ya gaisa da ita."Gyaran murya Daddy yayi yace."banda abin ka ai kaima kasan yaje gunta yanzun haka wannan accident din da'ya same shi daga gidan nasu yake Lamarin Umar sai addu'a narasa yanda ya kwallafa yarinyar nan a ranshi irin haka."hakane Daddy ya jima yana sonta tun lokacin da akayi kiddinerp din ta since before ya dade yana sonta sai dai bai gano ta ba saida yaga ana sanarwa batanta."iska mai zafin gaske Daddy ya fesar yace."Yar Jarida ikon Allah."kaga Umaru mubarwa Allah ikon shi, kaga Halidu kaje ka huta gobe in Allah yakaimu zamuje dakai da Ishaq muyima mahaifin yarinyar nan maganar yaron nan azo ayi Lamarin nan kowama ya huta."haba ranka shidade mu zaman me mukeyi bai dace ace kai da kanka zakayi wannan aikin ba tunda ga mu."ba komai indai akan farin cikin Faruqu komai ma zan iya ai banga ta zama ba wannan zuwan dai dani za'ayi shi amma wani zuwan kana iya zuwa kaida 'yan uwanka ko cikin mutanen ka, kada ka manta Faruqu fa 'dan dangine."shikenan Allah ya shige mana gaba kada idan komai ya kammala zan wuce nabar ayyuka da dama ya kamata na idasu kafin election din nan kada nabar aiki ga wanda Allah yasa shike da rabon kujerar nan."ba kana cikin masu nema ba.?"kwarai kuwa Abba ina ciki kaga mulki na Allah ne yakan ba wanda yaso kuma yana ansar shi wajen wanda yaso."gaskia Umaru haka ake son musulmin kwarai ya kasance mai yawan tawakkali da muka al'amuran sa ga Allah tabbas mutun bazai taba dana sani ba, Allah ya tabbatar mana da alkhairi."Amin Abba, tashi kaje Khalid."toh Daddy ku tashi lafiya."da haka ya nufi sashen su, sun jima suna ta'ba fira da sirikin nashi kafin shima ya tashi yai mashi sallama sannan ya nufi wajen Fulani ko tsayawa baiyi ba yayi masu sallama convey din shi suka kai shi masaukin da aka tanadar mashi domin hutawa.

★★★★

"Sannu da zuwa Baba"yauwa 'yar albarka kije Umaru na jiranki,yana falor na."Toh Baba."tashi tayi daga saman tabarmar da duke zaune ita da Umma suna fita ta shiga da'kin ta ta sakko katuwar hijab dinta har kasa ruwan kwai, ta dauki wayarta tana."miskili kafi mahaukaci ban haushi yau kuma ko da wace kalar isar yazo ya nuna mani kuma? Allah ya kyauta halin ka."zuburar baki tayi kamar wadda akaima dole ta zira takalman ta ta nufi wajen ba'kon nata,da sallama dauke a bakinta ta shiga cikin falorn sai dai bai amsata ba, idonsa akan ta ko keftawa baiyi shirun da yayi mata ya sake kular da ita cikeda masifa ta dago kanta tace."sallamar ma baza'a amsa mani ba ko saina ro'ka sann....."sauran maganar bakinta ta yanke sakamakon ido hudu da sukayi da juna fuskar shi dauke da murmushi mai tafiyar da zuciya itama sai ta samu kanta dayin murmushin a hankali takaraso ta zauna saman kujerar dake fuskantar shi tace."Yayana dama kaine? shine ko 'yar sallamar tawa ba zaka amsa min ba."murmushin sa mai tsada ya kuma sakar mata yace."zuciyata ta shagala da kallan kyakkyawar fuskar ki, tunanina ya tsaya na wucin gadi, kunnuwana sun cika da tsananin za'kin muryar ki wadda ke ratsa zuciya ta zuwa ruhina!  Jamila da ace kinsan yanda nike jin ki araina tabbas da bakiyi challenging dina ba danna kasa amsa maki sallamar ki ba dadin muryar ki da tsantsar gardinta ta shagaltar da ni kimin aikin afuwa rabin raina tuba nike."ba ka'dan takejin dadin kalamansa ba tabbas yanzun tafara jin son Umar aranta ta gama yarda shidin mutumin kirkine ya dace da rayuwarta isarsa batasa ya nuna shidin wanine ba ko wani karfin iko nashi da yake gadara dashi ya aje komai nashi da yake tunkaho dashi ya nuna mata sonta na daban ne a gareshi kuma zai iya sadaukar da farin cikin shi akan nata."gimbiya ta, kodai inyi kneel down domin kiyafe mani please bana son kiyi fushi dani."ajiyar zuciya ta fesar a hankali tace."haba Yayana ba laifin da kaiman, saidai yanzun kake kokarin yimani laifin.?" a razane yace."da bazan taba yafema kaina ba, wane kalar laifine nike kokarin yi maki fadaman domin na kiyaye."ka daina ko da'ni idan har ba so kake kanwar taka takai kanta inda Allah bai kai taba."iska mai zafi ya fesar daga cikin bakin shi yace."ina rokon wata alfarma agareki idan ba matsala."inajin ka."numfasawa yayi yace."dan Allah kidaina kirana da Yayan nan nifa masoyin ki ne Jamila ko bakyayiman kallan haka.?" A hankali ta girgiza kanta tace."kada ka manta a haka Babana ya dauke ka, kaga dole inyi maka kallan haka."to daga yau ki daina indai hakane zan sanar masa ainahin son da nikeyi naki, Jamila akanki ba abinda bazan iya ba na sadaukar da duk wani farin cikina saboda ke inayi maki kallan rayuwata banajin dadi idan har kina kallan duk wata yabawa da zanyi maki kamar ina zuba ki wallahi Jamila komai nike fada maki daga kasan zuciyata ne, na rokeki ki soni koda kwatan son da nikeyi maki ne, akan ki na daina duk wasu dabi'u marassa amfani akan ki na dage neman ilimi domin in saita rayuwata da duk wani dabi'una saboda son ki naje na koyi tausassan lafazi da kalamai nagartattun don in kwantar maki da hankali saboda kaunar da nike maki na iya saita kaina daga mutun mai saurin zafi da fushi zuwa mutun mai saukin hali duk saboda ke Jamila mi kike tunanin zai faru dani a lokacin dana rasaki kiji tausayina ki soni koda ka'dan ne Jamila."kallansa kawai takeyi ba kadan zuciyar ta ta karye ba dajin kalaman Umar ba, musamman data kara tabbatar da duk abinda ya fa'da tayi imani da Allah Umar ya dace da rayuwar ta kuma tana kyautata zaton cewa bazata taba dana sani ba matukar ya kasance masoyin ta a rayuwa numfasawa tayi tana cewa."naji abinda ka fa'da kuma na aminta da kai  tabbas nasan kana sona kuma da gaskia saidai inajin fargaba."bakinsa har rawa yakeyi ya tambayeta yace."tsoron mi.?" "Ranar da Baba ya gane kaine ka dauke nicikin sanyin muryar da shi kanshi baisan yayi amfani da itaba yace".idan kika cire ke duk duniya babu mahalukin dayasan ni na dauke ki sai Umar Sanda idan ko har haka ta kasance tabbas Sanda ne."girgiza kanta tayi tace."Aaa Sanda bazai ta'ba fadawa Baba wannan maganar ba."kare shi kikeyi kenan.?"Aaa gaskia ta na fada dai, wa'anda sukasa ka dauke ni fa.?"murmushi yayi yace."basu son ina sonki ba kuma idan ma sun sani babu wanda yasan muhallin ki kinga babu wanda zaizo ya fadama Baba, tunda kin yabi Umar Sanda."murmushin kasan makoshi tayi yanda taga kishinsa zar akan Sanda ashe shima yana jin haushin shi kamar yanda shima bai son sa tace "yaran ka fa?" shiru yayi kamar mai nazarin wani abu sai kuma yace."ina kyautata masu zato! bazanyi fatan haka tafaru ba kasancewar Baba mutumin kirki bashi ke nuna zaiyi saurin afuwa ga wanda ya ha'ince shi ba, idan naga Baba nakan ji shi tamkar mahaifina haka Umma kallan mahaifiyata nikeyi mata yayin da nike maki kallan kanwata ta jini jigon rayuwata kuma masoyiyata wadda nike fatar ta zama uwa ta gari ga ya'yana, taya zanso wani abu ya  shiga tsakanina da mutanen da suka zama komai nawa a rayuwa? Sam bana son kina tunanin abinda ya riga da ya faru kiyi mana fatan alkhairi mana."sai ta samu kanta da jin dadi ga wani irin kwarin guiwa takara samu atattare da ita tace."hakane Allah ya tabbatar mana da duk wani alkhairi."Amin  rabin raina ina sonki."murmushi tayi ta sadda kanta kasa tace."nagode sosai."rike godiyar ki bani so."waro idanunta tayi waje tace."mi kuma nayi."hararar wasa ya watsa mata yace."Ni da yake godiyar nayi maki ina sonki nace."Hmm."ta furta tana murmushi."pls kice kina sona koda saman lips dinki ne nasan da sannu zaki soni har ranki."da sauri ta dago kanta ta kalle shi yace."yes may be zuwa time din kin gama yiman jarabawar da kike kinayi man, Ya Allah kasa naci koda kaso hamsin ne cikin d'ari, nakan ji tsoro ya kamani duk lokacin dana tuna ina kan tarkon exam dinki mai girma agareni nakanyi addu'a akan Allah yabani sa'ar cin ta, kema ina so ki tayi da addu'a sannan ki tausayaman kiyiman questions masu sauki kamar yanda kike mai saukin hali da jin kai."Rasa abinda zatace mashi tayi ba kadan dadadan kalaman sa keyin tasiri a cikin zuciyar ta ba tace."indai jarabawa tace ka kwantar da hankalin ka saura ka'dan na kammalata ina sa ran kaine zakayi wining amma fa saika kara dagewa."murmushi ya kuma kawata fuskar sa yace."dagaske? Insha Allah zaki sameni nine gwarzon da zai lashe wannan jarabawar ina kaunar ki masoyiyata."nima ina kaunar ka har cikin raina."dadi na musamman ya ziyarci kasan zuciyar shi kamar ya zuba ruwa kasa yasha yace."Allah yabarmin ke rabin raina ya karemin ke."amin" Dan shirune ya biyo baya,dan gyaran murya yayi yace."albishirin ki.?"cikeda zumu'di tace."goro."fari ko Ja.?"dariya yaso ya bata cijewa kawai tayi ta maida ta yanda yake rawar jiki kamar ba Umar Diga dinta ba tace."fari kyal mai kyakkyawar siffa kamarka."a hankali ya lumshe idonsa ya bude su saman kyakkyawar fuskar ta yace.

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now