009

20 0 0
                                    

_*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*_

*NA*

_JAMEEY_

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*PAGE 9*

Maganar MD dine ya dawo da Umar haiyaci, cigaba da cewa MD yayi."Umar ka koma bakin aiki yau ka kula da tv station ke kuma Jamila ki koma gida kifara neman Joter dinnan cikin gaggawa dan ta hanyar ne kawai za'a tabbatar da zargin da ake akan CP Ahmad fatan kin gane.?" Cike da sallar damuwa Jamila ya numfasa tana cewa."Eh insha Allah." Jinjina kai MD yana cewa.""Zaku iya tafiya." A tare suka ce."Thank you Sir."Dahaka suka tafi jikinta a matukar sanyaye,bakin motarta,ta tsaya tana mamakin yanda abubuwa sukazo mata haka, to ita ina ma taje a cikin jahar Niger da har zata yarda Joter tana lissafe daga office din Cp sai gidan commissioner of information na jahar sai station kodai gadar zare Cp Ahmad yayi mata shiyasa ya yarda da taje tayi firar da ɗaya daga cikin security?idan kuwa haka ne ba ƙaramin shanmatarta Cp yayi ba kuwa ta ina zata fara ita kuwa?sauke naunauyen numfashi tayi tana jin Umar Y yana cewa."Miye mafita Jamila.?" Dan kallon shi tayi tana furzar da iskan mai zafi tana cewa cikin silence voice da damuwa ta baibaye tace."I don't know, anything come with me up side down,what can i do Umar.?"Fesar da numfashi yayi mai zafin gaske yace."Solution ɗayane kije ki duba jikkar da kika wannan tafiya insha Allah zaki ganta." Jinjina mashi kai kawai tayi ba tare da ta iya furta mashi komai ba dan duka hankalinta da tunaninta da duk nazarin ta ya karkata ga ta tuno inda Joter ta faɗa ina ma record din da tayi nasu Cp Ahmad da security ya ɓata ba Joter din ba,dan singing din da yake jikin Joter tafi duk wani abu da zata kawo dan shine kusan last hope din minister tsaro na ƙasa,ta hanga ta duba ta waiga ta haiƙaiko bata tuna komai ba,idan ɗaya take hange shine cikin jikkarta ta saka Joter,to taya akayi har Joter ta iya barin cikin jikka ba tare da an saka hannu an cireta ba? To waye zai mata haka ma?ba wanda yasa main abinda ya kaikata jahar Niger daga ita sai MD da ya aikata dan samo singing and fingerprint na Cp Ahmad kuma tayi komai yanda ake bukata to ya akayi haka?rasa abun ma totally tayi dan har kanta ya fara sara mata saboda zurfafa tunani da tayi, lura da yanayin da abokiyar aikin tashi ta shiga kuma masoyiyarshi wanda yake fata da mafarki ta zama matarsa uwar ƴaƴansa yasa Umar Y shima yasa duk wani farincikinshi dan kuwa walwala da farincikin Jamila shine nashi farincikin,damuwarta kuwa da baki cikinta yakan saka shi shiga yanayin fiye da wanda yafi nata ma..furzar da iskan baƙinshi yayi yana cewa.

"Yanzun bari insa driver yakaiki ina key din?dan ban san kiyi driving kina a cikin wanann situation din and pls kirki saka ma kanki damuwa har wani abu yazo ya samaiki in shaa Allah za'a ganta ki natsu sosai idan kin koma gida ki duba da kyau zaki ganta." Bata da karfi ko kuzarin maido mashi ansa ma at all,shiyasa ta mika mashi tayi tana sauke ajiyar zuciya,waya yakira Ali drivern shi yasa ya maidata gida,haka yaita kara encouraging dinta da haka suka tafi shi kuma ya koma office ya dauki wasu takardu sannan ya shiga tv satation ya zauna inda manajojin wajen suka fara operating na'urorin wajen bai jima da zama ba wani babban mutun yazo ya zauna saman kushin shima zama yayi kujerar dake kallan ta mutumin aka fara daukar shirin in Live ake gwada shi cikin kamewa da nutsuwa yace."Assalamu alaikum warahamatullah masu kallan mu barkan mu da sake saduwa daku a cikin wannan shirin na TAFARU TAKARE,inda yau kuke tare da bakuwar fuska nasan zakuyi mamakin ganin Umar Y Umar a cikin shirin amadadin mai gabatar da shirin Jamila Abubakar ina maku barka da wannan lokaci,sannan muna baku hakuri akancin lokaci da akayi na wannan shirin sannan uzuri ne ya riketa fatan za'ai mata uzuri.?"Waigowa yayi ya kalli bakon shirin yace."Babban bakon mu barka da zuwa wannan fili mai tarin albarka." Gyara zamanshi sosai yayi yana cewa."Barka kade Alhaji Umar." Numfasawa Umar Y yayi gami da sakar mashi murmushi yana cewa."Zamu iya jin sunan bakon namu da takaitaccen tarihinsa sannan da wace tsaraba bakon namu yazo mana.?"Gyaran murya yayi yace."Da farko dai sunana Alhaji Tahir Haruna ni haffafen dan wannan Jiha ne sannan nazo wannan shirin da tsarabobi masu yawa,a ciki kuwa harda babbar tsarabata mai taken Yabon Gwani ya zama dole."Murmushi Umar yayi yana gyada kai yace."Lallai kam babbar tsaraba ce kam domin hausawa nacewa Yabon gwani ya zama dole,amman wanene wannan gwanin.?" Murmushi Alhaji Tahir ya saki yana gyara zamanshi yana cewa."Ba wani gwani bane wannan sai haziƙi fasihi mai aiki da nazari wanda ke kishin al'ummarsa ba dare ba rana kullin burin shi yakawo cigaba a cikin Jahar nan tamu wato mai girma Gwamna Alhaji Yusuf Umar yazama dole muyaba mashi akan namijin kokarin da yakeyi wajen hidima ma al'umma musamman talakawa da matasa." Jinjina kanshi Umar Y yayi yana cewa."Hakane tabbas hausawa nacewa yabon gwani dole ne,sai dai kamar wane aikace aikace wannan gwamnati tayi? Dan kuwa wasu daga cikin al'ummar wannan jaha ta Katsina sunce sun kulle ido basu ga kyaun maƙanta ba dan kuwa basu ga abinda wannan gwamnati ta His Excellency Alhaji Yusuf Umar tayi masu ba shiru kake ji ba wani amo." Murmushi Alhaji Tahir ya saki yana cewa."To ai Alhaji Umar ko makaho idan ya shafa yasan wannan jaha tamu mai albarka ta Katsina ta chanza,chanzawa ma ba ta wasa ba an kawo tsare-tsare daban daban masu ƙayatarwa sa...katseshi Umar Y yayi yana cewa."Ai Alhaji Tahir kasan Hausawa na cewa a gani a ƙasa ko kuma gani ya kori ji,ko ba haka ba?ko zaka zaiyano mana aiyukan da yayi ma wanann jaha tamu da har ta chanza baki ɗayanta.?" Numfasawa Alhaji Tahir yayi yana cewa." Kwarai kuwa gasu nan birjik abu na ɗaya da zan fara fadi wanda shine bawa matasa aikinyi, kowa yasan His Excellency Alhaji Yusuf Umar yayi kokarin matuƙar gaske wajen ganin ya gina matasan jahar Katsina tun daga daukar nauyin karatunsu da basu ofofi gami da basu jari mai kwari dan tsaya da kafafunsu,sannan gina makarantu talafawa mata da marayu inganta harkokin noma,zuba mana shataletale da sauransu,domin idan natsaya lissafa maka abubuwan alkhairin da wannan gwamnati tayi bazai lissafuba kaga dole yabama namijin kokarin datayi dan ganin cigaban al'ummar ta."  Jinjina kai Umar Y yayi yana cewa."Alhaji Tahir kana ganin duk wannan taimakon da yayiwa matasa ya isa duk inda ya dace kuwa?kasan wasu tallafin na gwamnati idan baka da wane ba zaka taɓa garwaye dashi ba sai dai kaga anayi,ko kuma nace idan baka siyasa to baka ba samun alkhairi gwamnati dan koda wannan abun ya fito isu-isu suke rabewa ba ruwansu da tallakawa,bayan kuma dan a raba ma tallakawan aka basu har sukayi babakere dashi, baka tunanin ama cikin kwaryar birnin Katsina ba sai an je local government din ta akwai matasa da yawa wanda basu karatu kuma basu da jarin da zasu kama sana'a dan dogara da kai,rayuwa kawai suke cikin raɗaɗi da kunchin rayuwa,da wanann damar wasu yan siyasar suke amfani wajen shigar dasu bangar siyasa ana basu dubu ɗaya ko biyu dan suyi rashin kunya da fitsara daga karshe ma kaga yaro ƙarami matashi ya na shan miyagun kwayoyi mai zaka ce to akan hakan.?"

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now