030

3 0 0
                                    

_*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*_

*NA*

_JAMEEY_

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*PAGE 30*

Ana hasko hoton Jamila hakan yayi daidai da bugun zuciyar Faruq,tunda ya kafe tv da ido ya kasa ko keftawa banda zuciyar sa daya sauya atake Mumy da tagama wayar da takeyi tace."yauwa Faruq daman ina son ganinka sai gashi kazo,Faruq..."ta kuma kiran sunan shi amman kamar wanda aka sassaka bata ita yake ba still bai dauke idon daga kallan tv din ba."Faruq."ta sake kiran sunan shi tareda taba shi,a hankali ya sauke ajiyar zuciya ya dawo da duban sa kan mahaifiyar tashi."ranki shidade."Kallan mamaki takema ɗan nata."miya dauke maka hankali har haka tunanin mi kakeyi Umar.?"karan farko da mahaifiyar sa ta kirasa da ainahin Umar dinsa."Nothing."girgiza kai tayi "tell me the truth what happen Faruq.?"maida duban sa yayi sosai kanta yace."Mumy yaushe za'a kawo karshen wannan case din.?"
"Wane case.?"ta tambaye shi dan neman sani."kinsan an dauke yar jaridar nan ba wani labari har yanzun sai dai kace wadda aka batar...."ya isa Faruq insa bani na sace taba kuma kanta farau kidnap sai tayi hakuri muna kokari dan ganin an dakile wadannan mutanen shine zaka dameni da zancen wata yar jarida can."a fusace tayi maganar."sorry Mum naga itama tana kalkashin kulawar ku kuma tana yima kasarta aiki ne."ya isa Faruq tanayima kanta dai,banda agansing gwamnati mi dan jarida keyi har akwai wanda yakai dan Jarida sharri.?" Girgiza kai yayi yana cewa."Haba Mumy amatsayinki na first lady bai dace kina wannan furucin ba kuma naga kowa dan jarida burin shi ya wayarma al'umma kai sannan yaji koken su dan gwamnati tasan minene bukatun talakawan ta minene laifin dan jarida.?"Kana muhawara danine komi.?"a wannan karan cikeda tsarewa tayi tambayar."girgiza kansa kawai yayi alamun aaa."wai kai minene hadin ka da yarinyar nan?kodai itace wadda ta canza maka ra'ayi kaketa hauka akanta.?"Wannan karan murmushi kawai yayi baice komi ba."sorry Mum kibar maganar nan fatan mu Allah ya bayyana duk wanda yake cikin wannan halin."ameen."tace ta cigaba da operating phone dinta."Mumy neman me kike mani."ya canza maganar dan yaga ranta ya baci."har kadawo hayyacin ka da wuri har haka.?"Jinjina kai kawai yayi batareda yayi magana ba."okay kaje gidan su Khalid ka amso mani sako wajen Hajia."Okay."Mikewa yayi zai tafi tace."Faruq."dawowa yayi ya zauna."Na'am."maida hankalin ta tayi kanshi sosai tace."i hope kasan hidimar bikin ka na matsowa ko?"nudding kanshi yace."yes Mum."Okay gobe idan mun dawo wani campagn jibi tuesday za'a tura ordern lefe yanada kyau ya tambayi Ramlat abun da take so." da mamaki yake kallan Mumy."How ni miya hadani da lefe Mumy infact banda lokacin da zan tsaya jin ra'ayin ta." Ko kallonshi first lady batayi ba tace."Umurni nabaka ba shawarar ka nike nema ba a wajenka,kasan wacece Ramlat tana son a girmama ra'ayin ta."Okay."yace bai jira cewar taba yabar dakin,banda zafi ba abinda zuciyar shi ke mashi gani yake kwata kwata mahaifiyar sa bata damu da ra'ayin shi ba komai Ramlat side dinsa ya koma ya kwanta yana jijjuya kalaman Mumy a wani bangaren yana shakkar taya zai sanar ma Mumy kai tsaye yar jarida yake so taya Mumy zata amshi maganar shin zata goyi bayan sa?tambayoyin daya dinga jeroma kanshi kenan har baccin wahala yai gaba dashi.

_DIGA VIEW_

A sukwane ya figi motar shi kirar Benz 450 tinkan ya iso gate har gate man ya bude mashi gate a sukwane yabar gidan kamar wanda zaibar kasar baki ɗaya haka Umar ke gudu da mota ba ruwan shi da wani traffic yake wucewa ikon Allah kadai yake tafiyar da lamarim Umar Diga kamar wanda bai cikin hayyacin shi,cikin wata kafariyar unguwa ya shiga da mota sai dai yakara wata tafiyar sannan ya isa bakin wani tafaren gida zan iya cewa gidan kusan shi kadai ne a layin sannan ba kowa a cikin unguwar tayi tsit kamar wata GRA haka wajen yake,horn yake dokawa amman mai gadi yaki bude mashi gate,hakan ba karamin kular da Diga yayi ba,bai jira wata wata ba ya fito daga motar ya shigo ta kofa daidai mai gadin gidan ya rugo da gudu zai bude mashi yana isowa Umar ya dauke shi da mari har saida ya wuntsila kasa direct cikin gidan yayi sai dai tinkan Umar ya isa har labari yakai kunnen Buba cikin kankanin lokaci yasa an sauya ma Jamila wajen da suka boyeta ansa gum an rufe mata baki..Shigowar Umar keda wuya cikin falorn Buba ya fito yana tafa hannu yana sakin shu'umin murmushi a saman fuskarshi."Well come home my son."yace yana cigana da sakin murmushi a saman fuskar shi.kujera ya samu ya zauna ya harde kafa daya saman daya yace."tana ina.?"Yanda Umar yayi maganar ba alamun sauki a saman fuskar shi."wake nan na dauka kazo neman afuwane mikake faɗa Umar.?" Wani banzan kallo Umar ya watsa ma Buba yana cewa."Kayi kadan innemi afuwarka yarinyar daka sata tana ina.?"yanayin mamaki yake kallan Umar kamar bai san komai ba yace."bansan abinda kake cewa ba Umar indai bazaka iya bada hakuri wannan ba wani abu bane mun yafe maka,sannan mun dawo dakai a cikin tafiyar mu."Kafa yasa ya halla kujerar da Buba ke zaune akai har saida ta tuntsire dashi kasa sannan yasha kular sa yace."zan halakaka matukar kabari wani abu yafaru da yarinyar nan saina koya maka darasin rayuwa sannan kajini da kyau ni Umar nafi karfin nazama karen siyasa,zaman kaina nikeyi da sannu saina kawo karshen ku azzalumai."Sai lokacin ya sake shi yana fidda huci mai zafin gaske."Umar."Buba yace yana tashi zaune."kada ince akan wannan yar jarida kake wulakanta ni,daman akanta kaki bin umurnin mu.?" Dogon tsaki Diga yaja yana cewa."Nabaka nan da hour ɗaya komi kake kasa wa'anda suka dauko ma ita su maido ta sannan yar jarida tafiyemin ku saboda ita akan gaskiar ta take."yana gama fadar haka ya juya zai fita,dai dai zaibar falorn yaji kamar shehshekar kuka har ya tunkari inda yaji sautin sai kuma yasa ya fita yana bugo kofar da karfin tsiya kai tsaye mota ya shiga yabar unguwa.

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now