_*🏝️NAHIYATA AREWA🐄*_
*NA*
_JAMEEY_
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
*PAGE 96*
Jama'a kowa yayi kokari yayi register mu Samu team ya cika zuwa karshen wata mu fara kwasar romon demoradiya,Kunga dai irin salary din da muke rabawa sunata yi mana Addu'a da sam barka suna fatan Alkairi akan wannan team work kowa yayi receiving alert Yana kwance, bugu da ka'ri kana a gefe Da'ya account Dinka Yana budewa ka ringa kwasar naira 100k a hakan ma Idan baka kawo kowa bane zaka Samu 100k Amma idan kayi kokari ka kawo jama a zaka ringa samun Sama da haka duk da haka fa akwai arias na 600k bayan budewar account dinku Alhamdulillah 🙏💃💃💃 maraba da 52u,godiya ta tabbata ga Allah 52U Alkairi ne💸💸💸💸 🥰🥰🥰💃💃💃💃💃
Contact us via
07034464517
08160508316Shiga tayi wani gida ko sallama babu a bakinta sai ma cewa da tayi."Fito fito Ladingo,kina ina ne haka.?"Tsaki Ladingo tayi daga cikin daki tana cewa."wai wacece wanan ne dan Allah take neman hanani bacci da yahagaga sai kace bin bashi.?"cike da masifa Ba'ba Ladidi ke cewa."idan har kika fito ai Kinga ko wacece ai,ke matsalar ki wallahi wulaƙanci idan baki gadama ba,karya ne dai kice baki dauki muryata ba so dai kike ki gayan magana kawai Ladingo."fitowa daga cikin dakin Ladingo tayi tana cewa."kedai wallahi Ladidi ba'a iya maki,daga tambayar mai magana har nayi zunubi kuma.?"zama saman yar'tsugunnon Ladidi tayi tana zama tana cewa."Kin dai ji dashi Ladingo wallahi,ni duk ba wannan ya kawo ni ba." Taɓe baki Ladingo tayi itama tana zama tana cewa."Daman ai nasan jimina bata waigar banza,idan har kika tako kafafunki gidan nan to matsalar ki ce ta kawo ki Ladidi."Dan shiru Ladidi tayi sai kuma ta furzar da naunauyen numfashi tana cewa."Kedai wallahi baki rabuwa da tsegumi dan Allah ki barni naji da baƙin cikin da yake addabata mana, nazo na kawo maki kukana dan mu haɗu mu kawo matsalar damuwar kina man haka,bayan kin san banda wanda zai zo na kawo ma kukana sai ke tun yarinta dai muke tare."Hakane kuma Ladidi yanzun maike faruwa?maiye matsalar.?"Numfasawa Ladidi tayi tana cewa."Ai matsalar jiya da yau dai ce Ladingo na rasa ya zanyi da yaran nan Ladingo,kullum sai ƙara cigaba suke karshe ma Isuhu yarje masu yayi suka tafi yawon duniya Katsina wai da sunan neman ilimi ta ina?neman ilimi kodai yawon ta zubar?ni abinda nike so Ladingo ita Hannatu za'a yi man aiki a kanta idan har wani abu ya samu Hannatu na bala'i da masifa na tabbata hakan na iya jefar zuciyar Ubaidu har ya kaishi da mutuwa ma dan yanda yake son yarinyar ko kanshi bai so haka."Kama baki Ladingo tayi tana cewa."Ohni Ladingo shi Isuhu lalacewar da ta samaishi kenan?ke kuma kika zuba masu ido baki hana tafiyar ba?duk kina aikin mai hakan ta faru?dan yaga ke ɗaya kikayi saura a Sumaila shiyasa har yayi hakan a gaban kan shi."Hawaye Ladidi ta share tana cewa."Bari kawai Ladingo ai nida banza duk ɗaya isuhu yaranshi ne kawai a gabashin bai ƙi na mutu ba,ai wallahi Allah ya isa tsakanina da Maryama baƙin asirin da tayi ma Isuhu na sonsu ita yaranta har yanzun yana tasiri a jikin shi."
Jinjina kai Ladingo tayi tana cewa."Ikuwa idan har haka ne wallahi bata isa ba duk da ta mutu kuwa,ina amfani a haɗa jini da dangin asiri dangin tsiya Ladidi ni daman can zuri'ar Isuhu basuyi man ba saboda wannan marar tarbiyyar yaron nashi Ubaidu kina gani nabar zuwa Sumaila dan banga amfanin zuwana ba yaro ya kalli girman idona ya zageni ta uwa ta uba siyasa ma nabar waiwaiyarki baki ɗaya,dan haka baki ga ta zama ba tashi zakiyi yanzun yanzun mu tafi wajen na bakin gawo yayi maki maganin matsalar ki ta shekara da shekaru kije ki faɗa mashi duk abinda kike son ayi ma Hannatu idan ma kashe ta kike so ayi kawai a tura aljanu su shanye jinin shegiya uban kowa ya huta."share hawayenta Ladidi tayi tana cewa."Idan har aka kasheta kai tsaye ai ban cisguna ma Ubaidu baƙin cikin da ya cisgunaman a zuciyata ba ke kuwa Ladingo sai bala'in duniya da masifa sun hau mata ta wulaƙanta wanda baƙin cikin haka zai sa zuciyoyinsu ta buga daga ita har Ubaidun Ladingo ni haka nike so da su ai."Jinjina kai Ladingo tayi tana cewa."Kuma fa haka ne kin kawo shawara to mai kike son na bakin gawo yayi mata dan shi aikinshi kamar yankar wuƙa ne fa."dan shiru Ladidi tayi sai kuma tace."So nike a samu wani yayi mata cikin shege ana cikin darun cikin kuma a haukata ta hauka mafi muni kuwa wanda zata dinga yawo tsirara tana bugun mutane, tana farfaɗiya a yashe kasa karshe ai baƙin cikin hakan zai zamo ajalinsa ita kuma ko bata mutu ba masifar hauka ga wahalar ciki ma ya ishe ta."
YOU ARE READING
NAHIYA TA AREWA
General FictionThe Story of Nahiyata Arewa is the one that comprise the most important things such as Correction,Injustice,Betrayl and Revenge including Entertainment and Education, is a Falatable and testable story.