102

8 0 0
                                    

_*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*_

*NA*

_JAMEEY_

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*PAGE 102*

Jama'a kowa yayi kokari yayi register mu Samu team ya cika zuwa karshen wata mu fara kwasar romon demoradiya,Kunga dai irin salary din da muke rabawa sunata yi mana Addu'a da sam barka suna fatan Alkairi akan wannan team work kowa yayi receiving alert Yana kwance cikin aminci, bugu da ka'ri kana a gefe da'ya account dinka Yana budewa ka ringa kwasar naira 100k  a hakan ma Idan baka kawo kowa bane zaka Samu 100k Amma idan kayi kokari ka kawo jama'a zaka ringa samun Sama da haka duk da haka fa akwai arias na 600k bayan budewar account dinku da company ta baku Alhamdulillah 🙏💃💃💃 maraba da 52u,godiya ta tabbata ga Allah 52U Alkairi ne💸💸💸💸 🥰🥰🥰💃💃💃💃💃

Contact us via
07034464517
08160508316

102

Itako Ba'ba Hinde ta cika tayi fam kullin duban hanya takeyi ko taga kanin nata yazo Amma shiru kake ji maye ya ci shirwa, abu kamar wasa yau kwanan Aminatu biyar a gidan nan ta tun tana tsegumi ita da y'an uwanta har abun da ya taazzara,Maida duban ta tayi wajen Jafaru ta numfasa tace "yanzun tsakanin ka da ALLAH Jafaru miye riban abun da Fatahu keyi ma yarinyar nan ne? iyehhh yanzun ace kirikiri tunda tayi wanga bari bakinsa da nasa fa Bai hadu ba bare yai mata ya jiki haka akeyi? Da anyi magana sai ace malami ne ina malan tar take anan kana tauye hakin bayin ALLAH." Raken da yake sha a je gefen sa yace"wlh Ba'ba wannan dalilin kesawa bana shiga shirgin gidan Malan kodan wannan makirar matar tasa idan kika bibiyama ita din ce Zata hana sa ganin matarsa."Tabb ni da su ne."ita dai Amina Banda takaici ba abun da takeji ace kamar baka da wata daraja wajen mijinta duk da tasan sarai malan zaiki zuwa dubota saboda bada izinin shi tabar gidan sa ba, Kuma tasan Koda Indo tayi masa haka barin gida bada izinin shi tabbas zai iya kyaleta ita d sukema kallo shafaffa da mai din share hawayen da suka zubo mata tayi tace "Ni dai Ba'ba gaskia zan koma dakina ba zan zuba ido ba aure na ya lalace akan sakaci da rashin dalili,kinga dai malan ya fimu gaskia Kuma wlh ba zai taba biyoni ba Nidai ki barni in koma dakina."sa'kake tayi da baki tana karema Amina kallo kafin ta watsa mata Wani irin lallataccen kallo tace"Sannu tantabara uwar aure nace Ni ce nasan kanin nawa ya aureki ko? Da har kike zakemin duk ba dan ke Nike wannan hayagagar ba iyehhh? ai sai kije din nace saiki maida Kanki din? Gaki ga malan din nan,ke Amina Kibar ganin komai tsab zan kara aura masa wata zan aje danganta ka akan Fatahu komai ma zan iya yin sa dan kijini da kyau tsab zan aje danganta ka nayi maki wanki babban bargo ahtohh."mikewa tsaye Aminatu tayi tana cewa."koma dai yayane Ba'ba Nidai gidana zan tafi,aure kuma daga ALLAH ne mima ai dama wata na iske ai." Ke Amina yayar tamu kike fadawa magana son ranki."?daga mashi hannu Hinde tayi tana cewa."Rabu da ita Jafaru dani take zancen zata kwashi kashinta a hannu ne,saidai idan ba sunana ba Hindatu."ita dai Amina Bata jira cewar su ba ta fice zuwa gidan ta,wannan kenan.

Bayan kwana biyu, tunda dugu dugu Ba'ba Hinde ta aikawa Fatahu dan aike lallai tana bukatar ganin shi gidan ta,yaron malan dake tsugunne gaban malan yace."tun takwas na safe ta aiko ayi mata kiranka malan."toh ba Magaji kaci gaba da bawa yara karatu ina zuwa."toh malan."komawa yai cikin gidan sa Kai tsaye dakin Aminatu ya nufa ya shiga ya kimtsa sanann ya dubeta yace."zanje wajen Baba Hinde tana kira na,ko da najima kisa yaron malan ya hado maki cefane dan ALLAH Kada ayi ranar girkin nan, kinga akwai mabukata da yawa."toh malan insha Allah zanyi komai akan lokaci"saina dawo."fita yayi Kai tsaye gidan yayar sa ya nufa akayi sa'a ya isketa da sauran Yan uwan nasa kamar ma shi kadai suke Jira bayan sun amsa masa sallamar da yayi ya nemi wajen ya zauna ya gaishe da Baba ta amsa sa ciki ciki duk da yaga kamar akwai matsala bai yarda ya nuna hakan a fuskar shi ba,maida dubanta tayi tace."yanzun Fatahu tun yaushe na aika inakiran amma baka zo ba sai yanzun kaga damar zuwa."? Maida duban sa yayi ga Jafaru yace."fitowa ta kenan yaron malan ke sanarmi."tohh ai na dauka yar so din ce ta hanaka fitowa ba wannan ba yanzun dai ka maido hankalin ka wajena magana mai mahimmanci zan yi da Kai."Maida duban sa yayi gunta yace inajin ki Bata."munfasawa tayi tace."Aure Nike so ka kara Fatahu nan ba da jimawa ba." A razane ya dago kansa yana kallan yayar tasa cike da mamakin da ya gaza boyewa a saman fuskar tashi yace."Aure kuma."?jinjina kanta tayi alamun tabbatarwa tace "kwarai da gaske,nayi maka matar da zaka aura ma."wannan karan Shiru malan yayi baice komai ba,cigaba da cewa tayi "tana tarbiya Kuma inaji a raina zata haifa maka nagartattun Ya'ya."numfasawa yayi yace."Aishatu ko ita Aminatu a cikin su wacece ta gaza da kula dani ko daukar dawainiyata."? murmusawa tayi cike da gadara tace."Aishatu itace ta gaza ko ka manta ita din jiya ce."? Dan shiru malan yayi yana d'an ya mutsa fuskarsa kadan alamun baijin dadin maganar Sam yace."shima Jafarun auren zaki Kara yi masa kenan."? "Haba malan mi kake cewa haka Ni dai matata ta isheni aure sai Kai ai."murmushi akwai yayi yana ganin irin son zuciyar dangin sa yace"indai hakane ni matana sun wadace ni Ba'ba Kibar wannan maganar dan Allah."mikewa tayi tsaye tana mai cewa."walahi ba zaakasa inji Kunya ba na gama magana mako biyu masu zuwa Khadijatu ta zama matar ka." Shima mikewa yayi yana cewa." Da dai kinyi hakuri Ba'ba Kibar zancen nan,idan Kuma kin matsa zan sanar ma matan nawa yanda mukayi dasu zakiji."shekeke tayi tana kallansa yana zura takalmin sa alamun tafiya zaiyi tace."ba yarjewar su Nike bukata kaima din bawai shawara Nike baka ba,umurni ne idan kuma ban isa ba zaka iya tafiya." A hankali ya Isa kusa da ita ce."alqawalin da nayima Mahaifiyar mu bana fatan na saba shi a rayuwata zan maki biyayya tamkar ita,indai har kinyi magana da gidan iyayen yarinya tabbas bazan iya kunyataki ba saidai ki sani ya dace ki dinga bani dama ko da sau da'ya ne tal a rayuwata"sihirtacciyar ajiyar zuciya ta sauke ganin ta samo kan kanin nata cikin sauki tace." ALLAH yai maka albarka kaje ku gaisa da ita."Amin,saidai inda tayi maki ai ba sai naje ba Ba'ba."girgiza kanta tayi tace "Kai dai kaje ba wata bace face Khadijatu yar kanin mijina ta gidan Alhaji Almu."iskar bakinsa ya fesar yace." ALLAH ya shige mana gaba."Amin."Mai da duban sa yayi ga Jafaru yace."Kai Jafaru Ni zan wuce ko kana nan."eh ina nan."murmushi kawai yayi yace "sai anjima."toh kadafa ka manta kaje wajen yarinyar nan."toh Ba'ba Kada ki damu zanje." Da haka ya fita bai jira cewar ta ba....

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now