015

11 1 0
                                    

_*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*_

*NA*

_JAMEEY_

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*PAGE 15*

Mr President zaune a cikin katafaren office din shi,kana ganinshi zaka gane ya zurfafa a cikin nazari duk da ga files nan agaban shi yana dubawa a zahiri amman a baɗini ya zurfafa a nazarin rayuwa..Sectary yai nocking kofar sai dai shiru ba ai mashi izinin shigowa ba,almost 3mint kafin ya turo kofar da sallama abakin shi ya shigo cikin kamilallan office din,tsaye yai kamar wani soja ya kame a cikin suite yana cewa."Morning Sir."Dan shiru yayi duk da ya kalli Sectary din nashi,sai kuma ya bude wani file yanaci gana da dubawa gami da cewa."Morning."yana cigaba da aikin shi duk da ba aikin yake ba, numfasawa Sectary yayi cike da natsuwa ya fara cewa."Ranka shidade ga Schedules din yau a ciki harda request letter da aka kawo yau daga Senate."Mika mashi yayi cike da girmamawa,dubawa yayi yana ganin yanda aka tsara mashi komai na yau a ciki harda meeting da zaiyi da Sanatoci sai kuma wanda zaiyi da hukumar zabe ta kasa da karfe 3pm,firzar da iskan bakinshi yayi yana kallon sectary yana cewa."3pm meeting has been cancel becouse i have more appointment today."Dan  rissinawa Sectary yayi yace."ranka shidade za'a iya posponding dinshi zuwa wani lokacin?" Dan shiru Mrs president yayi sai kuma ya dan numfasa yana cewa."No za'a iya turo Deputy idan badamuwa." Okay Sir."Dan jim kadan yayi saida yai mashi izini sannan ya fita dan cigaba da aikin shi.

Phone dinshi tahau ruri kamar bazai daga ba sai kuma ya ɗaga gami da sakin murmushi yana cewa."Son how are you.?" Cike da zallar farinciki Faruq ya ansa da."Am fine dad." Jinjina kai Dad yayi yana cewa."Uhmm mine zaka sanar mani muryarka kadai ta tabbatar mani da hakan Faruq." Yar ƙaramar dariya Faruq yayi yana cewa."Yeah Dad yau ina cikin farin ciki."yar karamar ajiyar zuciya ya sauke sirrance,dan ba abinda yake saka mrs president a cikin farinciki in minute yaji Faruq yana cikin farin ciki da walwala,shima murmushin ya saki yana cewa."Okay you know ina office ko.?" Dan turo baki gaba Faruq yayi yana cewa."Dad give me a few minute i went gist for you."Uhmm."yai murmushin manya yasan halin ɗan nashi da shirme a zahiri yace."Okay inajinka." Sakin murmushi Faruq yayi yana cewa."Dady nasamu matar da zan aura." With suprise Mr President ke maimaita zancen Faruq a cikin zuciyar sa a zahiri kuwa yace.
"Mata are you serious"?" Ɗaga kai faruq yayi kamar yana a gaban Dad dinshi yake cewa."Yeah Dad trust me am not jocking." Cike da rashin yarda da maganar da ɗan nashi yayi mashi yake cewa."Look Faruq anjima muyi magana bansan zancen banza you know me."Thank you Dad i love you."yace yana jin dadi na ratsa shi a lokaci guda.

Jinjina kai yayi yana al'ajabin maganar Faruq kodai shirmen sa ne ya motsa anya zai iya fidda mata kamar yanda yake mafarki."Allah yasa haka."Ya faɗa a hankali yana cigaba da aikin sa yana sakin murmushi a saman fuskar shi sai ya samu damuwar sa ta rage kaso goma cikin ɗari,domin ba abinda yafi ɗaga hankalin shugaban Kasa irin yanda ake fama da rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin al'umma,musamman yan Bandit da ake fama dashi ga Kiddinerping da akeyi kusan ya zama ruwan dare,wɗannan abubuwan sukan sa Alhaji Umar shiga damuwa akowane lokaci idan yana murmushi yakan dauke a saman fuskar sa matukar zai tuna halin da kasar shi ta tsinci kanta a ciki..Duk da yana iyakar kokarin shi dan inganta harkar tsaro a kowane yanki dake fadin Kasar baki ɗaya,wannan karen PA dinsa ya shigo dauke da telephone ta office cike da kamewa da ladabi yace.

☆☆☆☆

Cikin kausassar murya mai saka zukatan maza girgiza da faduwar gaba dan kallon ɗaya zaka yi ma Umar Diga sai kaji tsoron shi ya darka maka a zuciya dan tun daga kan maganarshi har daurewarshi babu alamar wasa a ciki,ba kamar idan ma ya a a kan aiki bai san wani abu wai shi sakarci yafi son ayi komai a cikin so serious shiyasa wasa bai taɓa hadashi da yaranshi ba har Jigida da yake babban yaronshi bai wasa da kowa shiyasa ko kakinshi sukaji suke shiga cikin hankalinsu gudun samun wata matsalar kuma tunda sun san halin kayansu,kuma yana da dadin zama amman sai ka fahimci waye Dagi damai yake so da kuma wanda bai bukatar ayi mashi idan har ka kiyaye to ba ruwansa da kai,kauda kanshi daga kallonta yayi yana cewa cikin tsare fuska babu alamar wasa a taitare dashi yace."Mine sunan ki.?" ba alamu annuri ko kadan a saman kyakkyawar fuskashi  kana ganin shi kasan ya amsa sunansa akira shi cikakken namiji mai haiba da kwarjini wanda ko namiji ya tsare da idanunsa tabbas ya razana balle mace mai rauni,cike da tsoro ta maida kanta ƙasa tana cewa."Jam Jam Jamila."tace a rarrabe tana kukan zuci banda dukan tara tara kamar kirjinta yafado kasa dan kidima."
Nice name."
Yace a cikin zuciyarshi a zahiri kuwa kamar yaga abun da rai baiso ya kauda kansa gefe ya mike daga rankwafar da yayi saman gadon ta koma gefe ɗaya yana jijjuwa kansa da yai masa nauyi lokaci guda,dan ƙaramin tsaki ya ja cike da takaici yace."I can't." yana mikewa tsaye cike da kasaita yake taka kasa da cikkken damtse dake nuna shidin gwarzo ne,hannunsa ya daura saman handle din dakin ya bude kafarsa ɗaya ciki ɗaya waje ya tsaye cak sakamakon sautin ta daya tsinkaya cike da kuka take cewa."Dan Allah ranka shidade kasa su maidani karku zalince ni."Still bai waigo ba kuma bai fita ba,sai dai yanajin zancen ta na ratsa shi kodan me?ya ayyana hakan aransa.
"Saboda tana mace,kuma itadin abin a girmama ce itadin mai daraja ce kuma uwace sannan kanwa,yaya,mata. Haka zuciyarshi ta gaya mashi,fesar da iskar bakin sa yayi ya ida fitar da kafarsa waje alamun bazai saurare ta ba. Kuka ta fashe dashi tana cewa."Dan Allah Yallabai. "Call me Umar."yace ba tare da ya waigo ya kalleta ba,yai gaba abin shi cike da gadara da izzar dake bayyana tsabar mulkinsa da nasabar sa uwa uba kyawunsa dake kara sa mashi haiba da kwarjini,Kuka ta fashe dashi tana kifa kanta saman gado kamar marainiya."Why zaku kamani kamar ba musulmai ba,duk kamalar ku amman baku da imani inalillahi wa'inna ilahirraji'un." Ta cigaba da kukan ta tanayi kamar zata sike tsabar kaduwa da ɗimauta.

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now