_*🏝️NAHIYATA AREWA🐄*_
*NA*
_JAMEEY_
بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
*PAGE 67*
Kallon Isuhu Ba'ba Ladidi tayi tana cewa."Wai nikam isuhu yaushe zakazo ka tafi nifa a gaskia ina bukatar hatuwa haka nan kaga dare yayi kai kuma banda aukin fira babu abinda ka aje haba."cewar Ba'ba Ladidi tayi maganar a kausashe,murnushi 'dan nata yayi yace.haba Ba'ba duka duka yanzun tara tayi fa kuma ban gaji da gaisawa da autata ba." Tsaki Ba'ba taja tana cewa."kai dallah yiman shiru mutumin musawa da kai, kai dai Yusuf ka shiga taitayin ka dani billahi ka baro matar shine zakazo ka tare wajen wannan figigiyar yarinyar kamar mage wai auta! Ina autar take anan ka dauki son duniya ka kwallafawa yaran nan ba Hannatun ba, ba Ubaidun ba daga yau kada na kuma jin ka kiraya wannan mujiyar yarinya da auta mai bakin halin tsiya irin na uwarta."take yaji wani irin abu aranshi yanda mahaifiyar shi ke wulakanta ya'yan daya haifa kamar ba jinin taba yayin da fuskar Hannatu kadai ya kalla yakara jin ba dadi aransa yace."nakanji ba dadi a raina idan kina tozarta marainiyar yarinyar nan Ba'ba kada ki manta wacece wannan yarinyar a wajena jinina ce kidaina batun mata Allah yasani nafison yarana akan Halima dan Allah Ba'ba ki barni na kula da 'yata kada kadaicin yayi mata yawa ba Ubaidu sai kuma ace nima din bana zama nayi fira da ita."rai a bace yayi maganar.
Rike baki Ba'ba Ladidi tayi tana al'ajabin dan nata da har ya iya yin magana mai tsawo da ita irin wannan abun da bai taba yi mata ba sai yau tace."ba shakka Isuhu ina fada kana fada kai ga mai 'yaya kasan dadin su, toh ai shikenan sai kazo ka dukeni nace." Girgiza kai Isuhu yayi yana cewa."ni ba dukan ki zanyi ba gaskia na fada maki nidai nagaji da wulakancin da kikema ya'yana Ba'ba sai kace bake kika haifeni ba."tafa hannun Ladadi tayi tana firzar da iskan bakinta mai zafi tana cewa."iyeh yau ina ga rasulillahi..Isuhu ni kake gaya ma haka? Tabb ai saika nemo wata uwar ta daban idan har kana da ita! Da kake maganar yarinyar nan marainiya saika gwada mani iyayena a fadin duniyar nan nima ai marainiyar ce da anyi magana sai kuce marainiya ce kai ka fada Ubaidu shima ya fadaman haka sannan 'Dahiru ma saida ya kuma maimaitamin ohni Ladidi naga takaina ina zankai wannan jafa'i?na gaji wallahi banki an wayi gari ba yarinyar nan ta mutu kai ka huta nima in huta ita kanta marainiyar ta huta haba ina dalili.?" Ware ido Isuhu yayi cike da mamakin mahaifiyarshi yake cewa."subhanalillahi haba Ba'ba kisan kalaman da zaki dinga fadi mana,ita fa magana zanar bunu ce tana bakin mai ita ki fadi alkhairi ko kiyi shiru ki zama mai yawan tausasa zance sannan ki sama ranki imani da sallama mana yarinyar nan Allah ya nufa sai tazo duniya kuma ta silata minene laifina? dan Allah ki sarara mata hakanan idan kuma kince baki son zama da Hannatu sai in dauketa na maidata hannuna tunda ita din dole nace."mikewa tsaye Ba'ba Ladidi tayi ta kwadawa isuhu kahurin mari har saida ya rike kuncin shi nuna shi da yatsa tayi tace."dana tsine maka albarka matsawar kace zaka dauki Hannatu ka maidata wajen Halima so kake ta hana mani 'ya walwala dama taya na samu wa'annan kafuran ya'yan suka barka kayi aure yanzun bakin ciki da mugun nufin su yasa ko 'dan batan watan ma sun hanata yi sun dage tilas su kadai zasu cinye dukiyar ka."jikin Hanne ya hau rawa tsabar kidima batasan tafara kuka ba tunda take zagi bata taba ganin wani yaima Baban ta ba yau gashi har marin shi saida Ladidi tayi, Isuhu yace."shikenan Ba'ba naji abinda kikace saidai ki sani tabbas kin nuna mani karfin ikon haihuwa babu yanda zanyi dake amma kisani kiji tsoron Allah duk abinda zakiyi ki zama mai kyautatawa ina tsoron ranar da Allah zai kamaki ta silar marainiyar yarinyar nan." Tsaki Ladadi taja tana cewa."kaji shashasha da tsoron ka nikeyi Isuhu.?"Numfasawa Isuhu kawai yayi yana cewa."shikenan ke kuma Hannatu ki kara hakuri da ikon Allah zaki zama wata a rayuwa kuma Allah natare dake kinji tashi keji 'daki ki kwanta ki tabbatar kin saka kuba karki kwanta baki saya daki ba kinga ba kyau kwana a bude."Toh Babana kayi hakuri sai da safe."Allah yakaimu."harta juya zata shiga 'daki tace."ke zo nan."juyowa Hannatu tayi saidai bata dawo wajen Ladidin ba domin tasan labarin gizo bata wuce na ko'ki tarasa dalilin dayasa kullin sai Ladidi tayi mata kashedin kada ya rufe kofa, haka kuwa akayi tace."kika rufe da'kin nan saina yanka ki ko gawarki baza'a kuma gani ba kinajina.?"Murmushi Hannatu tayi tace."Dama kin daina wahalar da kanki wajen nanata mani wannan zancen domin kuwa na kiyaye su indai koface ba zan rufe ta ba ki kwantar da ranki."maida duban ta tayi ga mahaifin tace."Asuba ya gari Baba."Allah ya tashemu lafiya."da haka Hannatu ta shige da'kin ta Isuhu yace."Haba Ba'ba narasa daliln dayasa 'yan kwanakin nan kika bijiro da wannan al'adar kinsan fa dare sirrine dashi komai sirrinta shi akeyi."Yayi ubana Jatau sai naji duka sannan zan fada idan ta isa ta rufe kofar taga yanda wasan zai canza salo."Allah yabaki hakuri sai Allah yakaimu."Da ka kyautawa kanka."shidai ba kuma cewa komai ya fita yana mamakin dabi'un mahaifiyar tashi itama tashi tayi ta fa'da dakinta ta kwanta duk da ba wani dare ne yayi sosai ba bai wuce goma saura ba dare.
YOU ARE READING
NAHIYA TA AREWA
General FictionThe Story of Nahiyata Arewa is the one that comprise the most important things such as Correction,Injustice,Betrayl and Revenge including Entertainment and Education, is a Falatable and testable story.