025

10 1 0
                                    

_*🏝️NAHIYATA  AREWA🐄*_

*NA*

_JAMEEY_

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

*PAGE 25*

"Wanda ya jikan maraya Allah zai jikan shi,yaku mutane kuji tausayin maraya a koda yaushe kada ka zama marar imani da tausayi sau nawa kataba tunanin maraya nawa ya kwana baici ba?sau nawa katabawa jin tausayin maraya? Kada ka manta kaima wata rana zaka mutu kuma zakabar marayu a wannan rana waye zaiji tausayin naka zuriyar? Manzon Allah SAW yace kuji tausayin maraya kada kucinye masu dukiyar su,duk wanda ya shafi kan maraya da niyar jinkai bazai sauke hannunsa daga bisa kan wannan marayan ba har sai Allah ya gafarta mashi yajikan shi Hadisi ne ingantacce inaga wanda yasaka maraya dariya? Yakai uba ka tsaya ka nutsu da kyau a cikin lokacin da Allah ya wadataka dashi ka duba kayi karatunta natsu kaga marayu nawa ke unguwar ku kataba taimaka masu daidai da kwayar zarra to idan baka taba ba kafara domin Allah SWT ya girmama maraya kuma baisan yaga maraya yana kuka yana da kyau mujibinci lamarin maraya sai Allah yaji tausayin mu,amman yanzun da yawan mutane basu da tausayi sun manta da rayuwar maraya wanima dukiyar da maraya ya gada zai cinye sannan ya kore su kuma abin mamaki dayawan su dangin mahaifin su ne amman basu iya taimakon su da komai saima abinda Allah ya mallaka masu shi zasu cinye bayan Allah SWT ya tanaji azaba mai tsanani ga wanda yaci dukiyar maraya wuta yaci ma kansa ayoyi da dama a cikin alqur'ani mai girma sunyi hani akan haka...Hadisi ne ingantacce manzon rahama SAW yayi hani da cutar maraya yana da kyau mu shiga taitayin mu,mu kiyaye saukar hawayen maraya a saman doron kasa alhalin Allah SWT ya hore mana yanda zamuyi har mu taimake su.

Ya kai dan uwa idan Allah yai maka arziki kayi hakuri ka dibe wani bangare daga cikin zuciyar ka,ka ciyar da maraya ka tufatar da maraya,idan kana da arziki ka dauki nauyin marayu ta hanyar basu ilimi da lafiya wlh da ace Allah SWT zai nuna mana dinbin ladar dake cikin daukar dawainiyar maraya da kowa sai ya gwammaci ya bayar da dukiyar sa baki daya dan ganin ya taimaki maraya,akwai kisso shi da dama da suka kwadaitar damu akan ladar dake cikin taimakon maraya,sannan kuma akwai kissoshi da ayoyi da suka tsoratar damu akan cutar da maraya da tanadin azabar da Allah ya tanadar akan wanda ya handame hakkin maraya yanada kyau mu taimaki marayu dan samun rabauta ranar gobe kiyama wannan koba komai muma Allah ba zai tagayyarar da namu zuriyar ba Allah yasa mudace agurguje duba da lokaci zamuyi tsokaci akan zumunci,da yawan mutane sunyi watsi da hankar zumunci kowa nashi yasani abu yakai ya kawo ɗan kanin ka ko wanka bai zama dolen ka ba naka kadai kasani daga kauri dai guiwa wlh muji tsoron Allah,zumunci ba karamin abu bane kalma ce dake cikin sunan Allah yace shine zumunci kuma  akwai kabaki daya tanadar ma masu sada shi kada mubiyema shaidan mu manta da zumunta halin da muka tsinci kanmu yasa mun lalata zumunta yau dan uwan ka bai iya zuwa wajen ka dan zumunta sai kaji ta takura maka shima bai iya zuwa kai tsaye saiya samu abunda ya kawo maka wai dan ka dauke shi da kima gaskia muji tsoron Allah..Ada iyayen mu sukanje zumunci batareda komai ba daga su sai su zasuje zumun ta su da dangin su kowa nason dan uwan sa zasu koma suna kewar juna yanzun fa? Kowa bai son kowa mun yada zumunci bamu iya rike ya'yan yan uwan mu,bamu ziyarta su da ran iyayen su hakama bayan basu wlh mu guji haduwar mu da uban gijin mu,Allah yai mana muwafaka a cikin al'amuran mu,duba da lokaci nan zamu tsaya sai Allah yakaimu karatu na gaba zamuyi magana akan zakka da hakkokin ta sai kuma falala da azumi ya kunsa insha Allah,sububana rabbuka rabbil izzati ammayasfun wassalamun alal mursalin walhamdulillah rabbil alameen."Kowa yasha karatun da Sheik Abubakar ya gabatar kenan bayan gama sallar magarib sannan suka tada sallar isha'i,wannan kenan.

☆☆☆☆

Tafiya take kamar wahainiya tsabar iya taku da zallar yanga,ga natural makeup da tayi sai ya ƙara ma fuskarta kyau da ƙaya dan ba cika fuskar tayi da kayan tarkacen kwalliya ba daga powder sai kwali da pinklip da ta shafa a fuskar ba ƙaramin kyau tayi ba so cute masha Allah cike da yangarta da ta zamai mata jiki ta dan kalleshi tana cewa."Na shirya."Wani irin kallo ya watsa mata yab maida kanshi bisa plasma dake aiki a hankali gami da satar kallonta ta gefen ido dan kwana biyu tunda ya dawo daga Katsina ko wace irin Ramlat zatayi tana mashi kyau kamshinta yana shiyarshi har cikin zuciyarshi tsaye Ramlat tayi tana kallan Faruq da ya daura kafa ɗaya saman ɗaya yana aikin kallan shi hankali kwance dan kwabe fuska tayi tana cewa."Na shirya fa Ya Faruq."cike da shagwaba tayi maganar ɗagowa yayi yana ƙare mata kallo from head to toe maida numfashi yayi a hankali yana cewa."Nayi kama da driver dinki.?"girgiza kanta tayi dandanan idanun ta sun kawo kwalla tana maida su."Dan Allah."Ta kuma cewa tana marairaicewa sifar roko,maida hankalinshi wajen kallon yayi yana cewa."Bazan jeba."Mumy dake saukowa daga bene ta tsaya tana karema yaran nata kallo daya bayan daya,yanayin Ramlat kawai ta gani taji ranta ba dadi."Lafiya.?"Ta tambaya tana karasowa cikin falorn,zama tayi tana maida kallan ta wajen Faruq."mikayi mata.?"Mamaki cike da fuskar shi ya kalli mahaifiyar tashi."Afternoon Mumcy." Daure fuska Mumy tayi tana cewa."Am asking for you why are you silence.?"Nothing."A takaice yai maganar yana kara kama kan shi."Ramlat seat dowm mi yayi maki.?"Zama tayi tana aza kanga saman kafadar Mumy tace."Wai bazai rakani shopping ba."a shagwabe tayi maganar tana kwabe fuska kamar karamar yarinya kankanuwa maida kallonta wajen Faruq Mumy tayi tana cewa."Faruq why.?" Turo baki Faruq yayi yana cewa."Ni dan aikin ta ne,ko ni tsaran tane.?" Jinjina mashi kai Mumy tayi tana cewa."Yeah you are her mate becouse she's your wife." Cike da kosawa da maganar ya gyara zamanshi da kyau yana cewa."Mumy kidaina fadan haka baiko ba aure bane why zakina cewa haka.?"Faruq."A zafafe takira sunan shi cikeda da tsarewa take cewa."ya zama dole ka saki jiki da Ramlat becouse your wife is ur friend you know that dole kasan damuwar ta kana son friends din ta suyi mata dariya baka damu da damuwar ta ba tana yar uwar ka kuma matar da zaka aura." Firzar da naunauyen ajiyar zuciya yayi yana cewa."Ohh Mumy bansan ya zan nuna maki manufata ba karki ce..."ya isa maza kaje ka kaita tayi shopping."ta katse shi ta hanyar daga mashi hannu."Duk drivers din dake gidan nan amman ni zan kaita shopping imagine the hole Faruq haba Mumy."Tashi Mumy tayi tana cewa."Okay tunda baka kai ta bari ni na kai ta banji komai tunda nasan kimar ta." Girgiza kai yayi yana cewa."No naji zan kaita."Komawa tayi ta zauna saman kushin tana aika mashi mugun kallo itako Ramlat dadi ya ta lullube ta batasan sanda ta saki murmushin dadi ba."Thank you dear."Tace tana mai farin ciki."ki nutsu ki dauki abinda kike bukata,ka taya ta choosen abinda ya kamata."

Baice komai ba saima mikewa da yayi yai gaba kamar zai tashi sama duk soldier din da ya sarama Faruq bai kallan shi bare ya amsa har ya isa bakin mota itama Ramlat da sauri ta maye mashi baya tasan tsab zai iya barin ta baijin komai aikuwa haka akai yana isa yahau mota G wagon ya tada mota yana danna horn,da sassarfa Ramlat ta isa tana daga mashi hannu,yana ganin ta yai gaban gate daidai an bude ma Khalid gate ya danno hancin motar shi,shi kuma Faruq zai fita sukayi clashing a hankali ya zuge glass din motar shi yana kallan Khalid da shima tashi ke zage ido cikin ido suke kallan juna raban da yasaka Khalid a idon shi tun da yabaro Katsina bai kara bari sun hadu ba dauke idon shi Khalid yayi daga kallan Faruq maganar  Ramlat da yaji yasa shi maida kallan sa akan ta."Ya Faruq miye haka kajira mana."daidai wajen ta Khalid ya tsaya yana sakin fuskar shi yana cewa."Ramlat ya dai.?"Juyowa tayi da idanun ta da suka fara sauya kala tace."Ya Khalid sannu da zuwa."Yawwa"Lafiya mike faruwa.?" Maida hawayenta tayi tana cewa."Shopping zai kaini shine ya tafi yabar ni"Faruq problem bai taba sauya halin sa  azuci yai maganar a zahiri daukar wayar shi yayi ya kira Faruq duk da yana cikin gidan sai dai bai dawo ba kuma bai fita ba da kallo yabi wayar kamar ba zai daga ba sai kuma ya dauka ya sashi a speaker."Ba girman ka bane Faruq."Yace yana datse wayar ya aje a gefen sa yace."Kiyi hakuri da halin Faruq."Horn taji kamar cikin kunnen ta ya sake shi a kidime ta waiga ganin shi gefen ta fuskar shi murtuke still kallan Khalid yakeyi kallo mai ma'ana shima kallan ba nasa yakeyi,sai lokacin Ramlat ta zagaya ta shiga gaba ya danna motar yabar gidan shima shigewa yayi wajen Mumy dake neman shi sosai yake sheka gudu da ita cikin bacin rai ta Gimbiya Street yabiyo da ita,dai dai City Center ya tsaya duk da bai bukaci sanin inda tayi niyar zuwa ba."Fushin fari ba naka bane,girma anayin shi a wajen daya dace."Faruq ya turama Khalid text message."Bazaki fita ba.?"Yace a tsawace."ba nan zanje ba."Fita sai ki nemi mai kaiki inda zaki je."Da mamaki take kallan Faruq ko keftawa batayi ta rasa kalar halin baudewar Faruq."Get out kika tsareni da ido."Minayi maka ne ka tsane ni"hawaye suka ziraro mata."did you ask me?"Wani bakin ciki ya tokare Ramlat batasan ta fita daga motar ba har sauri takeyi ta faɗa cikin city center.

Girgiza kai kawai yayi ya maida seat ya kwantar da kan shi yana mamakin son zuciya irin tasu da kyal Ramlat ta saita kanta sannan tafara duba abinda take so,saidai bacin rai ya hanata daukar komai fitowa tayi tana tunanin yanda zata koma gida shawara ta fado mata ta kira Khalid yazo ya maida ta tasan Faruq ba zai jira taba tun fitowar ta yake kallan ta,ganin bata gan shi ba ya dauko wayar shi."Shanyar da kika shanya ta bushe."tana cikin kokarin kiran Khalid taji karar shigowar sako."my life." ta gani jikin ta na kyarma ta duba tana maida kallan ta inda tabar motar shi,jiki mace take tafiya a hankali kamar wadda kwai ya fashe mawa a ciki ta isa inda tabar shi,bude mota tayi ta shiga ko kallan shi batayi ba ya tada mota har suka isa gida uffan ba wanda yace ma kowa a cikin su.

☆☆☆☆

Uban daba da Jama'ar sa suka tare yaran Jigiri guda ukku a wata unguwa dake hayin yama dasu Ubaidu."Ku daga mani su yau saidai gyatumar su ta haifi wani."Uban daba yace yana daga katuwar addar shi sharbebiya dal da ita tana ta daukar ido."Kayi mana rai Ubaidu mun tuba."suka ce jiki na bari tsabar firgita ciki da rashin mutunci Ubaidu yake cewa."Ubaidu bai yafiya bai manta ranar daukar fansa dole yau ku bakunci kiyama."Kaddamar masu Oga."kure yace a buge alamu sun nuna sun sha sunyi babil rike mashi su akayi Uban daba yasa takobi ya datse ma babban yaron gijiri kunne kwalla razananan kara yayi yafadi kasa yana wulle wulle banda jini ba abinda ke zuba..Sauran na ganin haka sunsan halin Ubaidu bai iya gaba ba Allah ya basu sa'a suka runtuma ana kare harda wanda ya fadi yana burgima."Ku bisu kada kubari su tsere."Da gudu yaran Ubaidu suka bisu banda gudu ba abinda suke zagbawa a cikin unguwa lungu da sako kowa na neman ya cece ransa shima Ubaidun da gudu ya maye masu baya rike da sharbebiyar adda a hannun shi haka sauran kowa da makamai duk wanda ya hadu dasu sai ya watse musamman da aka gansu da makamai kowa yasan Kauraye ne,kuma ansa idan suka fara fadan gaba basu dainawa gudun da yaran Gijiri sukayi yana da nisa kwarai sannan suka afka cikin wani gida a sukwane mai gidan tana wanke wanke taji an bigeta an afka cikin dakin ta wani daga cikin su ba buga tsalla yahau katan ga cikin zama Ubaidu ya daba mashi wuka a kafa kwara ya saki ya dire waje."Suna ina.?"Ubaidu yace yana tambayar matar,sunajin shi suka boye kalkashin gadon dakin matar,yaran sa suka duba toilet saidai ba wanda ya duba dakin ta da haka suka tafi suna shan alwashi a ran su."Baki dayansu sai na karsu daga su har uban gidan nasu."Ubaidu yace yana fita daga gidan saida suka tabbatar da sun bar unguwar sannan suka fito daga boyen da sukayi.

A jigace ya iso wajen uban gidan nasu kafar shi na zubar jini,baki dayan su suka mike cikeda da tsoro."Zarto  lafiya.?"Gijiri ya tambaye shi yana shan taba."Uban daba ne yana can zai kashe su Mudi." Tashi Jigiri yayi yana busar taba yana cewa."Babban bala'i ina raye akwai wanda ya isa ya matsama yarana kam uban can kowa ya dauko takubba yau ni Garba Gijiri sai na fasama Ubaidu kai idona idon shi."Yace yana fesar da iska mai zafi a bakin shi dashi da yaran sa suka bazama neman Uban daba (Ubaidu) da yaran sa.

Share pls

NAHIYA TA AREWA Where stories live. Discover now